Faransa Da Burtaniya Sun Ba Da Shawarar Tsagaita Wuta Na Wata Guda A Ukraine
Published: 3rd, March 2025 GMT
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce Paris da London na aiki kan shirin tsagaita wuta na wata guda a Ukraine.
A wata hira da jaridar Le Figaro ta Faransa, Emmanuel Macron ya ce London da Paris suna ba da shawarar tsagaita wuta na wata guda da kuma samar da makamashi.”
Daga baya a cikin jawabin nasa, Macron ya ba da shawarar cewa kasashen Turai su kara yawan kudaden da suke kashewa a fannin tsaro da kashi 3 zuwa 3.
“Tsawon shekaru uku, Rashawa suna kashe kashi 10% na GDPn su a fannin tsaro; Don haka dole ne mu shirya don abin da ke gaba. »
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Pezeshkiya: Iran A Shirye Take Don Mu’amala Amma Bazata Bar Hakkinta Ba
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa Iran a shirye take ta fadada hulda da kasashen turai, amma kuma wannan ba zai sa ta saryar da hakkinta na sarrafa makamashin nukliya karshen dokokin kasa da kasa wadanda suka amince mata ta yi haka ba.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a yau Litinin a lokacinda yake ganaw da sabon jakadan kasar Faransa a Tehran pierre Cochard wanda ya mika masa tarkardun fara aikinbsa.
Shugaban ya kara da cewa an takurawa kasar Iran dangane da shirinta na makamashin nukliya a bayan. Amma daga yanzun kuma ba zata amince da irin takurawa ta bay aba.
Ya kuma bayyana cewa tattaunawa tsakanin Iran da kasashe uku na turai wato Faransa da Jamus da kuma Burtaniya, saboda samun fahintar juna da kuma daukewa kasar takunkuman tattalin arzikinn da turawan suka dora mata.