Aleksandar Vucic: Serbia Na Goyon Bayan Shawarar Kula Da Harkokin Duniya Da Kasar Sin Ta Gabatar
Published: 13th, September 2025 GMT
Shugaban kasar Serbia, Aleksandar Vucic, ya ce kasarsa na goyon bayan Shawarar Kula Da Harkokin Duniya da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar.
Shugaba Vucic ya bayyana haka ne yayin da yake hira da wakilin CMG a birnin Beijing na kasar Sin a kwanan baya, inda ya ce tsarawa da gabatar da wannan shawara mai ma’ana, ya zama wani abun da ya wajaba, saboda da farko, a zamanin da ake ciki, ana bukatar samar da karin ikon wakilci ga kasahe masu tasowa a fannin kula da al’amuran kasa da kasa.
A cewar shugaban na kasar Serbia, burin da shugaban kasar Sin Xi Jinping yake neman cimmawa, ta hanyar gabatar da wannan shawarar, shi ne tabbatar da daidaito tsakanin kasashe da al’ummu daban daban, gami da ba jama’a damar cin gajiyar duk wani mataki da ake dauka. Saboda haka, Mista Vucic ya ce ya kamata kowane mutum, da shugaban duk wata kasa, su goyi bayan shawarar ta kula da harkokin duniya, saboda tana da kyakkyawar manufa, kuma kasar ba ta da niyyar lalata tsarin kasa da kasa da ake kai yanzu. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
A Kan Wa Trump Ke Son Kaddamar Da Hari a Najeriya?
Duk da cewa suna da karfi a fannin aikin soja, amma harinsu zai zama tamkar amfani da igwa ne wajen kashe sauro. Duk wani fifikon da suke da shi ba zai dore ba. Saboda haka, a zahiri wannan tambayar da wani mai amfani da yanar gizo ya yi, ta nuna rashin hankali cikin kalaman shugaban Amurka.
Sai dai kalaman sun dace da halayya, da salon musamman na shugaba Donald Trump. Wani lokaci, da gangan ya kan yi amfani da kalmomi, da aikace-aikace marasa ma’ana wajen samar da yanayi na rashin tabbas, ta yadda zai samu damar matsawa wani lamba, don tilasta masa ya yi wani aiki. Wannan dabara ce da wasu masanan kasar Amurka ke kira da “ka’idar mahaukaci”, watakila ta dace da halayyar shugaba Trump, abun da ya sa yake ta amfani da ita wajen kula da harkokin waje.
Kana wannan batu na yin barazanar kai hari ya dace da halayyar kasar Amurka. Kasa ce wadda ba ta mai da hankali a kan neman gano gaskiya ba, balle ma la’akari da bayanan da Nijeriya ta gabatar dangane da zargin da aka yi mata. Kai tsaye an yi fatali da ikon mulkin kai na Najeriya, da dokokin kasa da kasa, da ra’ayoyin kasashen yankin da ake ciki. A ganin kasar Amurka, tana iya tsoma baki a duk wani aiki, da aikata yadda ta ga dama, kuma idan za ta iya yin amfani da karfin tuwo wajen tilasta wani, to ba za ta taba tattaunawa da shi ba. Kawai kasar tana kokarin aiwatar da mulkin danniya ne a duniya.
Amma, a cewar wasu masana, “ka’idar mahaukaci” ba ko yaushe take yin tasiri ba. Saboda idan wani ya dade yana kwaikwayon mahaukaci, to, ba za a ci gaba da tsoronsa ba. Kana mulkin danniya na kasar Amurka shi ma ba zai dore ba, idan aka yi la’akari da yadda kasashe masu tasowa ke tasowa cikin sauri a zamanin da muke ciki.
Ko ta yaya ya kamata Amurka ta daidaita kalamanta da ayyukanta? Kuma ta wace hanya ya kamata kasashe daban daban su yi mu’ammala da juna?
Na farko, ya kamata mu tabbatar da daidaito tsakanin mabambanta kasashe, da kuma bin dokokin kasa da kasa. Na biyu, ya kamata mu daukaka ra’ayin kasancewar bangarori masu fada-a-ji da yawa a duniya, da neman daidaita harkoki ta hanyar yin shawarwari, maimakon tayar da rikici. Na uku, ya kamata mu dora muhimmanci kan jin dadin jama’a, ta yadda ba za a tsaya ga kula da mutanen gida kadai ba, wato a hada da al’ummun sauran kasashe. Ya kamata a lura da hakkinsu da bukatunsu. Wadannan abubuwa suna cikin shawarar da kasar Sin ta gabatar, dangane da inganta jagorancin duniya.
Watakila kasar Amurka ba ta yarda da wadannan ka’idoji ba tukuna, amma tabbas wata rana za ta amince da su. (Bello Wang)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA