2025-11-03@06:25:11 GMT
إجمالي نتائج البحث: 400
«Salah al Bardawil»:
Sakataren Ma’aikatar Yaki na Amurka, Pete Hegseth, ya ce ma’aikatarsa na shirin daukar matakin soja idan gwamnatin Najeriya ta gaza kawo karshen “kashe-kashen Kiristoci marasa laifi” a kasar. Hegseth, yana mayar da martani ga wani sako da Shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa a Truth Social, inda ya zargi gwamnatin Najeriya da yin shiru kan hare-haren da ake kai wa Kiristoci. Gwamnatin Najeriya ta mayar da martani kan jawabin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi inda yake zargin kashe kiristoci a Najeriyar. A martanin da ta mayar, ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, ta ce lamarin ba haka ba ne. Sanarwar da kakakin ma’aikatar Kimiebi Imomotimi Ebienfa ya sanya wa hannu, ta ce, “duk da cewa Najeriya na godiya da kulawar...
Jamus ta shiga sahun ƙasashen duniya da ke kiran a gaggauta tsagaita wuta a yaƙin da ke ci gaba da salwantar rayuka a ƙasar Sudan. Sama da shekaru biyu ke nan Sudan na fama da yaƙin da ya ɗaiɗaita fararen hula baya ga asarar rayuka. Rikicin PDP: Tsagin Wike ya dakatar da Damagum Kisan Kiristoci: Za mu kai hari Najeriya — Trump Ministan Harkokin Wajen Jamus, Johann Wadephul, ya bayyana halin da Sudan ke ciki a matsayin “mummunan bala’i,” yana mai cewa babbar matsalar jinkai ta duniya a yanzu ta tattara ne a Sudan ɗin. A taron da aka gudanar a Bahrain, ƙasashen Birtaniya da Jordan su ma sun yi magana kan rikicin, suna kiran da a kawo ƙarshen...
Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya
Ya ce Sin tana maraba da kamfanonin dake fuskantar kalubale su tuntubi ma’aikatar ko hukumomi masu ruwa da tsaki, yana cewa, ma’aikatar za ta nazarci ainihin abubuwan dake faruwa da kuma bayar da damar fitar da kayayyaki ga wadanda suka cancanta. (Mai fassara: FMM) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya November 1, 2025 Daga Birnin Sin Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar November 1, 2025 Daga Birnin Sin Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung November 1, 2025
A cewarsa, ta hanyar wadannan shirye-shirye, kasar Sin ta nuna goyon baya mai dorewa ga kasashe masu tasowa kuma tana ba da gudummawa mai ma’ana ga ci gaban duniya a karkashin tsarin hadin gwiwar kasashe masu tasowa. (Abdulrazaq Yahuza Jere) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace October 31, 2025 Daga Birnin Sin Xi Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Kolin Shugabannin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC October 31, 2025 Daga Birnin Sin Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare October 31, 2025
Shugabannin Rundunar tsaro da Tinubu ya sallama sun hada da shugaban rundunar tsaro ta kasa Janar Christopher Musa da shugaban sojojin ruwa, Emmanuel Ikechukwu Ogalla da shugaban sojojin sama Hassan Abubakar. Wadanda suka maye gurbin su da idanu ya koma kan hobbasar kwazon da za su nuna su ne shugaban rundunar tsaro Olufemi Oluyede, shugaban sojojin kasa Waidi Shaibu, shugaban sojojin ruwa Idi Abbas da shugaban sojojin sama S.K Aneke sai kuma shugaban rundunar leken asiri, EAP Undiendeye wanda ya ci-gaba da rike kujerar sa. Yan Nijeriya sun jima suna kukan duk da kwarewa da gogewar jami’an sojojin Nijeriya da irin makuddan kudaden da gwamnati ke kashewa a sha’anin tsaro a kowace shekara amma matsalar kullum gaba- gaba take kara...
Shugabannin Rundunar tsaro da Tinubu ya sallama sun hada da shugaban rundunar tsaro ta kasa Janar Christopher Musa da shugaban sojojin ruwa, Emmanuel Ikechukwu Ogalla da shugaban sojojin sama Hassan Abubakar. Wadanda suka maye gurbin su da idanu ya koma kan hobbasar kwazon da za su nuna su ne shugaban rundunar tsaro Olufemi Oluyede, shugaban sojojin kasa Waidi Shaibu, shugaban sojojin ruwa Idi Abbas da shugaban sojojin sama S.K Aneke sai kuma shugaban rundunar leken asiri, EAP Undiendeye wanda ya ci-gaba da rike kujerar sa. Yan Nijeriya sun jima suna kukan duk da kwarewa da gogewar jami’an sojojin Nijeriya da irin makuddan kudaden da gwamnati ke kashewa a sha’anin tsaro a kowace shekara amma matsalar kullum gaba- gaba take kara...
Kasar Rasha ta sanar da samun nasarar gwajin jirgi maras matuki na nukiliya wanda yake ninkaya a cikin ruwa. Gwajin dai ya biyo bayan wasu gwaje-gwajen da Rashan ta yi ne na makamai masu linzami samfura mabanbanta masu iya daukar makaman Nukiliya. Jirgin maras matuki mai daukar makamin Nukiliya yana a karkashin rundunar sojan ruwan kasar,da aka bai wa sunan; Bosidon. Bugu da kari shi kanshi jirgin yana aiki ne da nukiliya a matsayin makamanshin da yake tafiyar da shi. Shugaban kasar Rasha Vladmir ya ce; babu wata na’ura wacce za ta iya dakatar da wannan jirgin mai ninkaya a cikin ruwa na Nukiliya. Shugaban kasar ta Rasha ya kara da cewa; Wannan sabon makamin babu kwatankwacinsa a duniya saboda...
Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada cewa: Dole ne a dage takunkumin da Amurka ta kakaba wa Cuba nan take Jakadan Iran kuma Wakilin Dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, Amir Sa’ed Irawani, ya jaddada cewa: Dole ne a dage takunkumin da aka sanya wa Cuba nan take ba tare da wani sharaɗi ba. Ya bayyana cewa: Kawo ƙarshen waɗannan matakan ba wai kawai zai samar da sauƙi ga al’ummar Cuba ba ne, har ma zai aika da saƙo mai haske da yanke hukunci ga duniya cewa zamanin tilastawa, mulkin mallaka, da rashin adalci na tattalin arziki ya ƙare. Irawani ya jaddada a ranar Talata, a lokacin taron Majalisar Dinkin Duniya da aka keɓe don tattauna ɗage takunkumin Amurka...
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar Gombe, DSP Buhari Abdullahi, ya shaida wa LEADERSHIP cewa, wasu manoma uku da makiyayi daya sun samu kananan raunuka. Ya kara da cewa an tura ‘yansanda da ‘yan banga na yankin don dawo da zaman lafiya. Kakakin rundunar ‘yansandan ya kuma ce, sun kama mutane 17 da ake zargi da hannu a rikicin, amma zaman lafiya da kwanciyar hankali ya dawo a yankin. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kano Ta Bai Wa Mata 5,200 Tallafin Naira Miliyan 260 October 28, 2025 Labarai Gwamnatin Neja Ta Bayar Da Hutun Kwanaki 2 Don Zaɓen Ƙananan Hukumomi October 28, 2025 Manyan Labarai Majalisar Dattawa Ta Maido Da Ranar Tantance Sabbin Shugabannin Sojoji Zuwa Laraba October...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun bayan sauya hafsoshin tsaro da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi ne dai mutane da dama keta tofa albarkacin bakinsu, yayin da wasu ke ganin hakan zai taimaka wajen yaki da rashin tsaro, wasu kuwa na ganin duk jama’ar ja ce. Shin ko sauya hafsoshin tsaro zai kawo karshen fargaban da al’umma ke yi? NAJERIYA A YAU: Me Dawowar Hare-hare Kan Sojoji Ke Nufi A Arewa Maso Gabas? DAGA LARABA: Shin Ko Jam’iyyar PDP Ta Fara Gushewa Ne? Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari akai. Domin sauke shirin, latsa nan
A ranar 25 ga watan Oktoban shekarar 1945, wato bayan da kasar Sin ta samu nasara a yakin kin harin mayakan Japan, kasar ta Sin ta karbi yankin Taiwan daga hannun Japanawa da suka yi rabin karni suna mamayar yankin, inda suke aiwatar da mulkin mallaka. Sa’an nan zuwa ranar 25 ga watan Oktoban bana, babban yankin kasar Sin ya gudanar da biki na musamman don tunawa da dawowar yankin Taiwan cikin harabar kasar. Dangane da batun, dimbin kafofin watsa labaru na kasashe daban daban suna ganin cewa, bikin da aka shirya ya nuna nasarar da Sinawa suka samu a yakin duniya na biyu, kana ya shaida cewa, Taiwan wani yanki ne na kasar Sin, wanda ba za a iya...
A yau Asabar 25 ga wannan wata, ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin da ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na majalisar gudanarwar kasar sun gudanar da liyafar murnar kebe ranar tunawa da kawo karshen mulkin mallakar Japan a yankin Taiwan, a dakin taro na Diaoyutai dake birnin Beijing. Wakilan bangarori daban daban na yankin Taiwan da na babban yankin kasar Sin masu halartar bikin murnar cika shekaru 80 da kawo karshen mulkin mallakar Japan a yankin Taiwan da safiyar wannan rana sun halarci liyafar. Direktan ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta Sin da ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na majalisar gudanarwar kasar...
Wannan shi ne daya daga cikin martanin NASENI da abokan huldarta don samar da CNG, wannan kuma na daga shirin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na daƙile tasirin cire tallafin man fetur ta hanyar samar da iskar gas mai rahusa. Manufar ita ce a rage dogaro da na’urorin lantarki da ake shigowa da su daga waje, da inganta dogaro da kai a ɓangaren fasaha, da samar da ayyukan yi. NASENI tana ba da ababen more rayuwa da tallafin manufofin, yayin da ɓangaren da ke kula da masana’antu, yana mai da hankali kan haɗin gwiwa, ƙirƙira da kasuwanci don kafa Nijeriya a matsayin cibiyar fasahar Afirka. Wannan dabarar da NASENI ta yi ya tabbatar da cewa ba a bar kasar a baya...
An Gudanar Da Taron Cika Shekaru 80 Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan Da Dawo Da Shi Kasar Sin A Beijing
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Wakilin Sin: Shawarar GGI Ta Nuna Yadda Za A Jagoranci Bunkasa Makomar MDD October 25, 2025 Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Tsara Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-biyar Na 15 October 25, 2025 Daga Birnin Sin An Kaddamar Da Nuna Muhimman Shirye-shiryen CMG A Membobin APEC October 25, 2025
Mahalifinsa, Chief Thomas Osen Ekpemupolo, da mahaifiyarsa, Mrs. Ewe Ekpemupolo, sun rayu cikin al’umma mai arziƙin mai a lokacin da ake tsaka da nema a yi wa yankinsu adalci. Daga cikin wannan rikicewar ya taso mutum wanda daga baya zai zama ɗan gwagwarmayar Niger Delta don neman daraja, adalci, da samun ikon gashin kai. Sojoji Sun Kama Mutane 69 Masu Fasa Bututun Mai A Yankin Neja-Delta Sojoji Sun Lalata Matatun Mai 20 A Yankin Niger Delta A tsakiyar shekarun 1990, arzikin mai na Nijeriya yana samu wadata a wasu wurare amma ya zama ana barin al’ummomi masu arziƙin mai cikin talauci, gurɓawa, da kuma rashin muryar magana. Ga matashin Tompolo, yin shiru wannan bai zama zaɓi ba. Gwagwarmaya Da...
An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Ta Saka Burikan Da Za Ta Cika A Shekaru 5 Masu Zuwa October 24, 2025 Daga Birnin Sin An Shirya Harba Kumbon Shenzhou-21 A Kwanan Nan October 24, 2025 Daga Birnin Sin Shugaba Xi Ya Jagoranci Zaman Jin Ra’ayoyin Wadanda Ba ‘Yan JKS Ba Game Da Tsara Shirin Raya Kasa Karo Na 15 October 24, 2025
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A cikin ‘yan watannin da suka gabata, an sake ganin karuwar hare-haren Boko Haram da ISWAP musamman a yankin Arewa maso Gabas. Kazalika, ko a kwanan nan ma anga irin wadannan hare hare. Wadannan hare-haren sun fi karkata kan sansanonin sojoji, inda ake samun asarar rayuka da dama, da kuma lalata kayan aikin gwamnati. Rahotanni daga Borno da Yobe da ma wasu sassan kasar nan sun nuna yadda ‘yan ta’adda suka sake samun karfi wajen kai hare-hare cikin dare, tare da amfani da dabaru irin na soji da kuma kayan yaki na zamani. Wannan lamari ya jawo tambaya daga al’umma: shin wannan karin hare-hare alama ce ta dawowar kungiyar Boko Haram da...
Jami’ar mai aikin tsarawa MDD rahoto akan Falasdinu Farencesca Albanese ta bayyana cewa; tsagaita wutar yaki da aka yi a Gaza, bai wadatar ba, wajibi ne a kawo karshen tsarin mamaya a Falasdinu. Albanese ta kuma ce Amurka ce take bai wa ‘yan mamaya cikakken goyon baya a kisan kiyashin da take yi wa al’ummar Falasdinu,don haka ya zama wajibi a kawo karshen yadda ‘yan mamayar suke sarrafa albarkatun al’ummar Falasdinu,sannan kuma a tarwatsa tsarin mulkin mallaka na mamaya. A halin da ake ciki a yanzu dai Albanese tana kasar Afirka Ta Kudu, inda take halartar taron shekara-shekara akan “Nelson Mandela” za kuma ta gabatar da jawabai a wurin. Tun a cikin watan Mayu ne dai Amurka ta kakawa ma’aikaciyar...
A cikin jawabin da ya gabatar a wannan Talata da aka nuna kai tsaye a taron jana’izar babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Yemen Laftanar Janar Mohammed al-Ghamari, Sayyed Abdulmalik al-Houthi ya jaddada cewa, kasar Yemen za ta ci gaba da kasancewa cikin shirin komowa ga ayyukan soji idan Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta koma kisan kare dangi, da kuma ci gaba da killace yankin zirin Gaza. Sayyed al-Houthi ya yi ishara da irin babban gangami na dubban daruruwan mutane da suka taru a wurin jana’izar shahid al-Ghamari a matsayin abin da ke nuni da tsayin daka na al’ummar Yemen a kan manufofinsu. Sayyed al-Houthi ya kuma yi nuni da cewa al’ummar Yemen sun gamsu da matsayi mai Daraja da suke a...
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jaddada cewa yaki da matsalar rashin tsaro a jihar nauyi ne na gwamnatinsa da sauran masu ruwa da tsaki, da ma al’umma baki. Wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a ranar Litinin, ta ce gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake jagorantar taron majalisar zartarwa ta jihar karo na 18 da aka gudanar a fadar gwamnati da ke Gusau. Sanarwar ta ce, majalisar ta tattauna kan muhimman batutuwa da suka shafi jihar, ciki har da tsaro, ilimi, kiwon lafiya, da cigaban ayyukan raya kasa. Dr. Lawal ya tunatar da mambobin majalisar muhimmancin hadin kan su wajen yaki da rashin tsaro a karkashin wannan gwamnati. “Muna samun...
Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a unguwar Danbare a Jihar Kano, ta gurfanar da wani mutum mai suna Malam Shaddadu bisa zargin sayar da gidan ɗansa ba tare da izini ba. Ɗan mutumin wanda ya gabatar da ƙara, Muhammad Shaddadu, ya shaida wa kotu cewa, lamarin ya samo asalin ne tun bayan da mahaifinsa ya saya wa wasu ‘yan uwansa biyu da suke uba ɗaya babura masu kafa uku da aka fi sani da Adaidata Sahu. APC ta rage wa Mata kuɗin tsayawa takara a Borno Dembele ya dawo PSG bayan jinyar makonni Sai dai daga baya, tsautsayi ya rutsa da ɗaya daga cikinsu wanda ɓata-gari suka kai masa hari har suka kashe shi, kuma suka yi awon...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya bayyana cewa, mafi yawancin kasashen duniya sun yi Imani da ka’idoji na cin gashin kai da ‘yanci. Abbas Arakci wanda ya gabatar da jawabi a wurin zaman majalisar zartarwa a yau Lahadi ya ce ya bayyana cewa a fagen diplomasiyya Iran ta dauki makamin dakile kokarin kasashen turai na sake dawu da takunkumi a kanta, ta hanyar aiki tare da kasashen Rasha da kuma China. Haka nan kuma ya yi jinjina ga matakin bayan nan da kungiyar ‘yan-ba-ruwanmu ta dauka na nuna cikakken goyon bayanta ga Iran, yana mai cewa; Ana samun kafuwar sabon kawance a duniya, yayin da kasashen turai da wasu tsiraru suke a gefe daya, ita kuwa Iran da mafi...
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana talauci a matsayin babban abokin gabar ɗan Adam. Ya ce ƙaruwar talauci a Najeriya na ci gaba da jawo rashin lafiya, jahilci, rashin tsaro, da rashin fata a tsakanin jama’a. ’Yan sanda sun tsare ɗan jarida kan zargin ɓata sunan hadimin gwamnan Kano Mahukunta sun kai samame wani gidan shan Shisha a Kano A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook domin bikin Ranar Yaƙi da Talauci ta Duniya, Atiku, ya ce wannan rana tana tunatar da gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki muhimmancin ƙara ƙoƙari wajen yaƙar talauci “Talauci ne babban abokin gabar ɗan Adam. Yana haifar da matsaloli kamar rashin lafiya, jahilci, rashin tsaro da sauransu,” in...
Wasikar Iran, Rasha da China ga Majalisar Dinkin Duniya dangane da kawo karshen kuduri mai lamba 2231 Mataimakin ministan harkokin wajen kasar mai kula da harkokin shari’a da kasa da kasa ya sanar da cewa, kasashen Iran, Rasha, da China sun aike da wata wasika ta hadin gwiwa zuwa ga babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da shugaban kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya dangane da kawo karshen kudurin kwamitin sulhu mai lamba 2231. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar kan harkokin shari’a da kasa da kasa, Kazem Gharibabadi, ya bayyana irin gagarumin yunkurin diplomasiyya da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke yi na kawo karshen kudurin kwamitin sulhu mai lamba 2231 a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin...
Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar ADC, za su koma APC a mako mai zuwa. A makonnin da suka gabata, ’yan siyasa da dama daga jam’iyyun adawa suna sauya sheƙa zuwa APC, yayin da ake shirin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027. HOTUNA: Al’ummar Jihar Neja sun yi addu’o’in neman zaman lafiya Ta’addanci: An fi kashe Musulmi a kan Kiristoci a Najeriya — Jakadan Amurka Idan ba a manta ba, Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, ya koma APC, sannan Gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri, shi ma ana sa ran zai sanar da sauya sheƙarsa a hukumance nan ba da jimawa ba. Yilwatda, yayin ganawarsa da mambobin APC a Jos, Jihar Filato, ya ce: “A...
Ya kara da cewa, Allah ya albarkaci Jihar Taraba da dimbin dabbobi, wanda kuma gwamnatin jihar za ta yi dukkan mai yiwuwa, wajen samar da kayan aiki tare da kara bunkasa fannin kiwo na jihar. Kazalika, ya sanar da cewa; gwamnatin za kuma ta tabbatar da ta kara bunkasa kasuwancin fannin, musamman domin wadanda suke a fannin su kara samun kudaden shiga tare da kuma kara samar wa da gwamnatin kudaden shiga. Nicholas, ya sanar da hakan ne, ta bakin wakilinsa Daraktan Kula da Harkokin Dabbobi da ke Aikin Noma da Samar da Wadataccen Abinci na jihar, Daudu A. Mbaamo Kwamishinan ya ci gaba da cewa, har yanzu fannin aikin noma, da shi jihar ta dogara a...
Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar ADC, za su koma APC a mako mai zuwa. A makonnin da suka gabata, ’yan siyasa da dama daga jam’iyyun adawa suna sauya sheƙa zuwa APC, yayin da ake shirin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027. HOTUNA: Al’ummar Jihar Neja sun yi addu’o’in neman zaman lafiya Ta’addanci: An fi kashe Musulmi a kan Kiristoci a Najeriya — Jakadan Amurka Idan ba a manta ba, Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, ya koma APC, sannan Gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri, shi ma ana sa ran zai sanar da sauya sheƙarsa a hukumance nan ba da jimawa ba. Yilwatda, yayin ganawarsa da mambobin APC a Jos, Jihar Filato, ya ce: “A...
A wani bayani da kungiyar Hamas din ta fitar tayi tir da Israila kan yanayin da gawarwarakin da ta bata na palasdinawa dake hannunta, inda aka ga alamomi na Azabtarwar ajikinsu da kuma cire wasu sassan jikinsu don haka ta yi kara da a kafa kwamitin bincike na kasa da kasa kan halin rashin dan adamta da isra’ilan ta nuna kan gawarwakin. Ta ce yin amfani da hanyoyi daban daban wajen Azabtarwa yana haifar da damuwa sosai kuma ya taka dokokin kasa da kasa da kuma yarjejeniyar Janeva, kuma wadannan ayyukan daidai suke da kisan kiyashi kan alummar falasdinu, Wasu kungiyoyin sun mika batun ga kwamitin kula da hakokin dan adam na majalisar dinkin duniya domin yin matsin lamba kan...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fidda bayani kan cewa daga yau Asabar 18 ga watan Octoban shekara ta 2025, kudurin kwamitin tsaro na MDD wanda aka samar don goyon bayan aiwatar da yarjeniyar Nukliyar kasar Iran wacce aka fi sani da JCPOA ya kawo karshe. Don haka daga yau shirin Nukliyar kasar Iran ta koma karkashen yarjeniyar NPT, kuma za’a yi mu’amala da shirin kamar sauran kasashen karkashin kula na hukumar IAEA. Tsahar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ma’aikatar na bada wannan sanarwan a safiyar Asabar ta kara da cewa dama kudurin na tsawon shekaru goma ne daga yau ta gama aiki. Daga yau shirin Nukliyar JMI zai ci gab aba tare da wani karin ka’idojin...
Rahotanni sun bayyana cewa Gwamnonin Jam’iyyar APC sun gudanar da wani taron sirri a gidan gwamnati da Jihar da ke Birnin Kebbi. An bayyana cewa aƙalla gwamnoni 20 daga cikin gwamnoni 24 na jam’iyyar ne suka gudananar da taron ƙarƙashin shugaban ƙungiyar gwamnonin APC, Hope Uzodinma, wanda shi ne gwamnan Jihar Imo. Gwamnan Gombe ya ƙaddamar da shirin tallafa wa karatun yara mata Wani mutum ya ƙona tsohuwar budurwarsa a Oyo An bayyana maƙasudin taron gwamnonin kan cewa za su tattauna muhimman batutuwan da suka shafi ƙasa da wasu batutuwa na jam’iyya mai mulkin ƙasar. Majiyar tashar Channel TV ta ruwaito cewa, shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda yana Jihar Kebbi amma bai halarci taron gwamnonin ba. A wata...
Abokan Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya Sun Ce: Sake Dawo Da Takunkumin Da Aka Kakaba Kan Iran Baya Kan Doka
Abokan Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya sun bayyana cewa: Sake dawo da takunkumi bayan karewarsa baya da wani tushe na doka ko tsari Kungiyar aminan Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da wata sanarwa game da cikar kudiri mai lamba 2231 kan yarjejeniyar makamashin nukiliyar Iran a ranar 18 ga watan Oktoba, inda ta bayyana cewa matakin da Amurka da Turai suka dauka na sake daukar matakin kakaba takunkumin da ya kare kan wata kasa tsari ne da baya ya kan wani tushe na doka ko yarjejeniyar kasa da kasa. Kungiyar aminan Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da wata sanarwa a ranar Alhamis da ke nuna cikar kuduri mai lamba 2231 na kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya...
An fara gina magudanan ruwa domin dakile afkuwar ambaliyar ruwa a kananan hukumomin Malam Madori da Kaugama dake jihar Jigawa. Tawagar Injiniyoyin jihar karkashin jagorancin Daraktan kula da ambaliyar ruwa da zaizayar kasa, Injiniya Mukhtar Muhammad Usman sun ziyarci kananan hukumomin domin duba yadda aikin ke gudana. Haka zalika Daraktan da mataimakin sa Injiniya Mahdi Isyaku da sauran ma’aikata ssn ziyarci wurin da ambaliyar ruwa tayi ta’adi a garin malam Madori. A lokacin da tawagar ta fara auna fili da tona magudanun ruwan, daraktan ya ce an fara aikin tona magudanar ruwa mai tsawon kilomita 2 a matsayin wani ɓangare na aikin karkatar da ruwan da ya lalata wurare zuwa sabon wurin da aka tsara. Yana mai cewar,...
A Kenya dubban al’ummar kasar ne suka hallara a babban filin jirgin saman kasar domin tarben gawar tsohon Firaministan kasar Raila Odinga. Shugaban kasar, William Ruto da tsohon shugaban kasa Uhuru Kenyatta da manyan jami’an gwamnati na daga cikin wadanda suka tarbi gawar tare da iyalan Odinga. Raila Odinga ya mutu ne a ranar Laraba a Indiya yana da shekara 80 bayan ya fadi a lokacin da yake tafiya. An dai ayyana ranar Juma’a a matsayin ranar hutu domin shirye-shiryen jana’izar sa, wanda za a yi ranar Lahadi a mahaifarsa ta Bondo, da ke yammacin kasar. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email*...
Shugaban kasar Amurka ya yi barazana ga shugaban kasar Rasha na aike wa Ukraine makamai masu linzami kirar Tomahawk Shugaban Amurka Donald Trump ya ce: Zai gargadi takwaransa na Rasha Vladimir Putin cewa: Akwai yiwuwar Ukraine za ta iya samun makamai masu linzami kirar “Tomahawk” idan Rasha ba ta kawo karshen yakin Ukraine ba. Da aka tambaye shi a cikin jirgin Air Force One da ke kan hanyarsa ta zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila da Masar da yammacin ranar Lahadi ko shi da kansa zai tattauna da Putin kan batun, Trump ya ce, “Yana iya magana da shi. Yana cewa: Idan ba a warware wannan yakin ba, zai aika wa Ukraine da makamai masu linzami na Tomahawk.” Trump ya kara da...
Ta ce, “Dole ne akwai kalubale da dama, wanda daga cikinmu muke fuskanta a yayin shigowa wannan masana’anta, amma dai ni babu wani abu da zan iya tunawa, illa wani wanda na iske a masana’antar ya karbi zunzurutun kudi har Naira 50,000 a mabanbantan lokuta da sunan zai yi min rijista a masana’antar, kuma bai yi ba, daga karshe ma na gano cewa; kudin rijistar duka-duka Naira 5,000 ne. A wata hira da Khadija ta yi da gidan Rediyon Hikima, ta bayyana cewa, matukar ta samu abin da ya kawo ta masana’antar (Kudi), to nan da shekara daya ma; za ta iya shiga daga ciki, ma’ana za ta samu miji ta yi aurenta na Sunna. Khadija, wadda ta...
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana cewa: Iran tana goyon bayan duk wani Shirin zaman lafiya da ya hada da dakatar da kisan kiyashi a Gaza Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta tabbatar da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana goyon bayan duk wani mataki ko wani yunkuri da ya hada da kawo karshen yakin kisan kiyashi a Gaza, janyewar sojojin mamayar Isra’ila, shigar da kayan agajin jin kai, sakin fursunonin Falastinawa, da kuma tabbatar da dukkanin hakkokin Falasdinawa. Haka kuma ta kara da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran a matsayinta na mai goyon bayan halastacciyar gwagwarmayar al’ummar Falastinu samun tabbatar da ‘yancin kai, ta yi amfani da dukkanin karfinta na diflomasiyya a cikin shekaru biyun da suka gabata, musamman...
Ma’aikatar Wajen Sin Ta Yi Tsokaci Kan Amincewar Da Isra’ila Ta Yi Da Yarjejeniyar Kawo Karshen Rikicin Gaza
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sojojin Ruwan Sin Za Su Gudanar Da Aikin Sintiri A Zirin Tekun Aden Da Yankin Tekun Somaliya October 10, 2025 Daga Birnin Sin CMG Ya Kaddamar Da Shirin “Dabarun Tallata Kayayyakin Sin” A Tafarkin Gina Kasa Bisa Hadin Gwiwa October 10, 2025 Daga Birnin Sin Sin Za Ta Fara Cajin Kudi Na Musamman Ga Jiragen Ruwan Amurka October 10, 2025
Bugu da kari, an rufe shafukan hakar ma’adanai haramtacce 98 a fadin kasar. “An kiyasta cewa Nijeriya na asarar kusan Dala biliyan 9 a kowace shekara sakamakon haramtacciyar hakar ma’adanai. Wannan sata ta albarkatunmu da ya kamata ta bunkasa kasarmu ta wuce kima, kuma lokaci ya yi da za a kawo karshensa,” in ji Abdulraheem. A cewar sa, kwamitin na da alhakin hana asarar kudaden shiga, tabbatar da gaskiya da adalci a harkokin hakar ma’adanai, da tabbatar da cewa dukiyoyin ma’adanin kasar suna ba da cikakken gudunmawa ga ci gaban tattalin arziki. “Yayin da muke ci gaba, daya daga cikin manyan manufofin wannan kwamitin shi ne hana asarar kudaden shiga da haramtacciyar hakar ma’adanai da ayyukanta ke...
Cikin darussan da wannan rikici ya tabbatar mana, akwai rashin tasirin amfani da karfin tuwo wajen warware duk wani rikici. Tabbas karfin soji kadai ba zai iya magance takaddama ko tashin hankali ba, ballantana ya wanzar da tsaro da walwalar bil’adama. Muna iya ganin hakan a zahiri, idan mun lura da yadda Isra’ila ta nuna a fili cewa hare-haren da ta kwashe shekaru biyu tana kaiwa sassan Gaza za su iya kawo karshen barazanar da ta ce kungiyar Hamas ke haifar mata, amma sai ga shi daga karshe sakamako ya nuna akasin haka. Har yanzu dai sannu a hankali ana komawa ga shawarar da kasashe masu son zaman lafiya suka jima suna bayarwa, wato a rungumi tattaunawa, da...
Kwamishinan Zamfara Ya Yabawa Yunkurin da Gwamna Lawal Ya Yi Na Jawo Masu Zuba Hannun Jarin Kasashen Waje.
Kwamishinan kasuwanci da masana’antu na jihar Zamfara, Abdulrahman Muhammad Tumbido, ya yabawa gwamna Dauda Lawal bisa jajircewar sa wajen tallata jihar Zamfara a matsayin cibiyar zuba jari. Kwamishinan, wanda ya bi sahun gwamna Lawal a wata tawaga ta hukuma zuwa bikin baje kolin kasuwanci da zuba jari na Canada–Africa da aka gudanar a Toronto, Canada, ya ce halartar gwamnan ya bude wa jihar sabbin damammaki na kasuwanci da bunkasar tattalin arziki. A wata sanarwa da jami’in yada labarai na ma’aikatar, Jamilu Bello, Tumbido ya fitar, ya tabbatar da cewa ma’aikatar kasuwanci da masana’antu za ta ci gaba da bin diddigin ayyukan hadin gwiwa da yarjejeniyoyin da aka kulla a wannan tafiya. A cewarsa, Gwamna Lawal ya baje...
Adaidai lokacin da ake taron cika shekaru 2 da fara yakin Gaza Babban sakatare janar din Majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya sake yin kira da a gaggauta cimma yarjejeniyar dakatar da bude wuta ta din din din a yankin Gaza .inda ya bayyana yakin a matsayin babban bala’I da ba’a taba ganin irinsa ba Yakin ya jawo mummunar asarar rayukan mutane fararen hula da kuma lalata abubuwan amfani na jama’a , kuma ya jawo matsaloli masu yawa a ayyukan jin kai da yake bukatar kulawa ta gaggawa da kuma warware matsala ta hanyar siyasa Guterres ya halarci wannan taron ne inda yayi alkawarin ganin an kawo karshen yakin Gaza kuma ya amince da dukkan shawarwarin da Amurka ta bayar...
Uche Nnaji, Ministan Ƙirƙira, Kimiyya da Fasaha, ya yi murabus daga mukaminsa. Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar da yammacin ranar Talata. Joash Amupitan na iya zama sabon shugaban INEC Jerin ministocin da zargin takardun bogi ya tabaibaye su Nnaji na fuskantar zarge-zarge kan sahihancin takardun karatunsa, inda binciken da jaridar Premium Times ta gudanar ya gano cewa Jami’ar Najeriya da ke Nsukka (UNN) ta ce ba ta ba shi takardar kammala digiri ba. A cewar jami’ar, tsohon Ministan bai kammala karatunsa a cikinta ba, kuma ba ta taɓa ba shi takardar shaidar kammala ta ba. A cewar jaridar, Simon U. Ortuanya, Shugaban Jami’ar UNN, ya...
Wani saksmkon kuri’ar jin ra’ayin jama’a da cibiyar dimokuradiyya ta Isra’ila ta gudanar ya nuna cewa kashi 66 cikin 100 na Isra’ilawa sun yi imanin cewa lokaci ya yi da za a kawo karshen yakin Gaza, tare da bayyana hadarin da fursunoni ke fuskanta. Wannan adadi na kashi 66% ya karu da kashi 13% a kan sakamakon da aka fitar a shekara guda da ta gabata lokacin da aka yi musu tambaya iri ɗaya. Sakamakon ya kuma nuna cewa kashi 45% na Isra’ilawa sun yi imanin cewa ya kamata Firayim Minista Benjamin Netanyahu ya yi murabus nan da nan kafin karshen yakin, tare da dora masa alhakin abubuwan da suka faru a ranar 7 ga Oktoba, 2023. Sakamakon ya nuna...
Da yake jawabi yayin kaddamarwar, ministan ilimi na kasar Rwanda Joseph Nsengimana ya ce shirin na hadin gwiwa ya nuna kudurin kasar na samar da ilimin fasaha ba tare da barin kowa a baya ba. Shi ma babban sakataren ma’aikatar kula da fasahar sadarwa da kirkire-kirkire ta kasar, Eraste Rurangwa, cewa ya yi, DigiTruck wani muhimmin bangare ne na shirin Rwanda na One Million Coders, wanda wani jigo ne dake ingiza cikar burin kasar na zama mai bunkasa tattalin arziki bisa dogaro da ilimi. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake...
A Malawi an rantsar da Peter Mutharika a matsayin shugaban kasar a karo na biyu. Mutharika, wanda ya taba zama shugaban kasar daga shekarar 2014 zuwa 2020, ya sake komawa kan kujerar shugabancin kasar bayan nasarar da ya samu a zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 16 ga Satumba da ya gabata. Mutharika wanda farfesan shari’a ne ya sami kuri’u miliyan 3 kwatankwacin kashi (56.8%) a kan abokin hamayarsa Lazarus Chakwera na kusan miliyan 1.8 (33%). Peter Mutharika ya yi rantsuwar ne a matsayin shugaban kasar Malawi na bakwai a wani biki da aka shirya a filin wasa na Kamuzu. A cikin jawabinsa na farko, Mutharika ya bayyana cewa “lokacin farin ciki ‘’ wawashe dukiyar gwamnati ya kare”....
Ita dai wannan yarjeniyar wadda wanda mamallakin karamin Jirgin Sama, zai bayar da hayar Jirginsa na Sama, ba tare da ma’aikata da kula da Jirgin da kuma yin inshore ba. Akasarin wannan yarjeniyar ana yinta da takardar shedar mamallakan Jiragen Samn wato AOC. “Hakan ya nuna cewa, mun fara shiga cikin matakin fafada harkar kasuwanci mai zaman kansa ne kuma za mu yi hakan a bangaren Kamafnin Jirgin Sama na Air Peace ba ne, sai dai kawai, a bangaren sauran Jiragen Sama,” A cewar Manajin Darakantan. A shekarar 2024 ne dai, aka cire Nijeriya daga cikin jeren kasasshen da suka yi kaurin suna wajen saba yarjeniyar, ta bayar da hayar Jirgin Sama. Kazalika, hakan ya biyo bayan kiyaye daukacin ka’idojin...
Gwamnatin jihar Nasarawa ta ce ta ware naira biliyan biyu domin biyan kudaden tallafin karatu da alawus alawus na guraben karatu a jihar. Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana hakan ne a lokacin bikin kaddamar da biyan alawus-alawus na shekarar 2023/2024 da aka gudanar a Kwalejin Ilimi ta karamar hukumar Akwanga ta jihar. Gwamnan a lokacin da yake kaddamar da shirin raba kudaden ya jaddada cewa baya ga biyan kudaden NECO, gwamnatin jihar tana biyan dalibai sama da 155 tallafin karatu na kasashen waje da sama da dalibai 30,000 a fadin kasar nan. Shima da yake nasa jawabin, kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa, Dokta Danladi Jatau wanda shugaban kwamitin majalisar kan harkokin ilimi Mista Abel Yakubu Bala...
Masar ta jaddada goyon bayanta ga zaman lafiyar Sudan tare da yin watsi da matakan bangare guda kan kogin Nilu Kasar Masar ta jaddada cikakken goyon bayanta ga zaman lafiyar kasar Sudan da kuma yankinta a jiya Laraba, tare da tabbatar da hadin kan matsayar kasashen biyu da kuma kin amincewa da matakan bangare daya kan kogin Nilu. Wannan dai ya zo ne a wata ganawa da ministan harkokin wajen Masar Badr Abdel Aty da shugaban majalisar gudanar da mulkin Sudan Abdel Fattah al-Burhan suka yi a birnin Port Sudan, a cewar wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Masar ta fitar. Abdel Aty ya ce ziyararsa ta uku zuwa Port Sudan cikin shekara guda sako ne na nuna goyon baya...
Jakadan kasar Rasha a Majalisar Dinkin Duniya, Vasily Nebenzya, ya ce maido da tsarin takunkuman karya tattalin arziki a kan Iran da wasu kasashen yammacin duniya suka yi ya saba wa kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya. Nebenzya ya bayyana hakan ne a wata doguwar wasika da ya aike wa babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da kuma shugaban rikon kwarya na kwamitin sulhun bayan da kasashe 15 suka kada kuri’ar sake kakaba takunkumi kan Tehran, wanda aka soke a karkashin yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma a shekara ta 2015 tsakanin Iran da manyan kasashen duniya, ciki har da Birtaniya, Faransa, da Jamus. Wakilin na Rasha ya jaddada cewa, an bullo da abin da ake kira tsarin dawo da takunkumai a...
An kuma amince da cewa ma’aikatan da aka kora za a mayar da su kan ayyukan su cikin wasu kamfanoni na rukunin Dangote ba tare da sun yi asarar albashi ba, kuma babu wani ma’aikaci da za a ci zarafinsa saboda rawar da ya taka a wannan taƙaddamar. An cimma matsayar ne a gaban manyan jami’an gwamnati da suka hada da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, ministan kudi kuma mai kula da tattalin arziki, ministan kasafin kudi da tsare-tsare, karamin ministan albarkatun man fetur (Gas) da shugabannin NMDPRA da NUPRC, da wakilan kamfanin man fetur na kasa (NNPCL). Haka kuma shugabannin kungiyar ‘yan kasuwa (TUC) sun halarci tattaunawar tare da shugabannin kungiyar ta...
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa; Iran zata iya taka muhimmiyar rawa wajen gina duniya da ba ta da tashin hankali Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Iran a yau, kamar irin abubuwan da ta faru a baya, za ta iya taka muhimmiyar rawa wajen gina duniya da ba ta da tashin hankali, da kuma cike da zaman lafiya, da abota, da zaman tare, da tattaunawa, kuma za ta iya sanya tausayi ya mamaye harshen bai daya ta hanyar yin amfani da arzikin al’adu. A cikin sakon da ya gabatar a wurin taron karrama mawakan Iran Shams Tabrizi da Mawlana Jalaluddin Mohammad Balkhi, shugaba Pezeshkian ya ce a ranar Talata: An ambaci ranakun 29 da 30 ga watan...
Janar Safawi; Iran Ta Kashe Matukan Jirgin Saman Isra’ila 16 A Yakin Kwanaki 12 Da Aka Yi A Tsakaninsu
Mai ba da shawara ga Jagoran juyin juya halin Musulunci Janar Safawi ya bayyana cewa: An kashe matukan jirgin saman yakin Isra’ila 16 a harin da aka kaddamar kan Iran Mai ba da shawara ga Jagoran juyin juya halin Musulunci Manjo Janar Yahya Rahim Safawi ya sanar da cewa: Iran ta harba makamai masu linzami sama da 500 kan haramtacciyar kasar Isra’ila a lokacin yakin kwanaki 12 da aka kwashe ana gwabzawa. Ya tabbatar da cewa: An yi nasarar kashe matukan jiragen saman yakin gwamnatin mamayar Isra’ila akalla 16 a daya daga cikin hare-haren makamai masu linzami da aka kai kan cibiyar horar da matukan jirgi. Wannan ya zo ne a cikin jawabin da Manjo Janar Yahya Rahim Safavi ya...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A ’yan watanni da suka gabata, matasa da yawa a Najeriya sun dukufa don ganin hakar su ta cimma ruwa wajen samun kudaden kirifto. Amma alamu na cewa a baya-bayan nan wasu daga cikinsu sun sare sun kuma saduda sun dawo daga rakiyar harkar. NAJERIYA A YAU: Abin Da Ɗangote, PENGASSAN Ba Su Yi Ba Don Magance Rikicinsu DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Cin Kifi Yadda Ya Kamata Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya yi nazari ne a kan dalilan wasu matasan na yin watsi da harkar kirifto. Domin sauke cikakken shirin, latsa nan
Shigowar Ganduje Da Sauya Mallaka A Asirce Sakamakon barazanar soke yarjejeniyar ya sa dole wanda ya kafa kamfanin, Ahmad Rabiu, ya nemi sabon abokin tarayya. A cikin wannan lokacin ne, a ranar 5 ga Maris, 2020, aka gudanar da wani taro na musamman na kamfanin Dala Inland Dry Port. A cikin wannan taron, an cire duk tsoffin daraktocin kamfanin, an kuma naɗa ƴaƴan Ganduje uku da wani ɗan nasa na kut da kut mai suna Abubakar Bawuro, a matsayin sabbin daraktoci. An ba kowane ɗaya daga cikin ƴaƴan Ganduje hannun jari na kashi 20% kowanne, haka kuma aka ba Bawuro da Rabiu kashi 20% kowanne. Wannan shi ne lokacin da aka cire Jihar Kano gaba ɗaya daga cikin masu mallakar...
Gwamnatin Tarayya wajabta wa ɗaliban da suka kammala karatu mika kundin bincikensu na ƙarshe a matsayin sharaɗi kafin a tura su aikin yi wa kasa hidima (NYSC). Dokar za ta fara aiki ne daga ranar 6 ga Oktoba, 2025, kamar yadda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume ya sanar. Ya bayyana cewa dokar ta shafi duk ɗaliban ajin ƙarshe da suka cancanci zuwa NYSC ko da kuwa a ƙasashen waje suka kammala karatu. Wannan yana daga cikin sauye-sauyen da Gwamnatin Tarayya ta yi wanda ya alaƙanta aikin Yi wa Ƙasa Hidima (NYSC) da Tsarin Tattara Bayan Ilimi ma Kasa (NERD). Ranar Laraba jirgin ƙasan Abuja-Kaduna zai dawo aiki Shekara 1 bayan rushewa, har yanzu ba gyara titin Kano–Maiduguri ba Bisa...
Hukumar lura da jiragen ƙasa ta Nijeriya (NRC) ta tabbatar da cewa daga ranar Laraba, 1 ga Oktoba, 2025, za a dawo da zirga-zirgar jirgin ƙasa na fasinjoji a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna. Wannan na zuwa ne bayan dakatar da tafiye-tafiye a watan Agusta sakamakon hatsarin da ya rutsa da ɗaya daga cikin jiragen. A cikin sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Callistus Unyimadu, ya fitar, NRC ta ce matakin ya nuna jajircewarta wajen tabbatar da tsaro da kuma inganycin sufuri ga ’yan ƙasa. Hukumar ta bayyana cewa ranar Laraba za ta kasance rana ta Musamman domin yin gyara a kan layin jirgin don gujewa matsaloli a nan gaba. NRC Ta Dakatar Da Sufurin Jirgin Ƙasan Abuja-Kaduna...
Gwamnatin Tarayya ta tabbatar wa da ƴan Nijeriya cewa za a ci gaba da samun isasshen man fetur duk da barazanar shiga yajin aiki da ƙungiyar PENGASSAN ta yi kan taƙaddama da matatar man Dangote. Wannan na zuwa ne bayan raɗe-raɗin cewa matatar ta dakatar da tsarin siyar da ɗanyen mai da ake biya sa da Naira. A wata sanarwa daga ma’aikatar kuɗi ta tarayya, daraktan hulɗa da jama’a Mohammed Manga ya bayyana cewa an gudanar da taron kwamitin kula da tsarin “buyqn Naira-don sayen ɗanyen mai” ƙarƙashin jagorancin Ministan Kuɗi, Wale Edun. Taron ya samu halartar Ministan tsare-tsare, da shugaban FIRS, da wakilai daga NNPC, CBN, NMDPRA da Afreximbank. Matatar Dangote Ta Dawo Sayar Da Man Fetur A Kuɗin...
A ranar Laraba, 1 ga watan Oktoba, 2025, jirgin ƙasan da ke jigilar fasinja tsakanin Abuja zuwa Kaduna zai dawo aiki. Hukumar Sufurin Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC) ta ce jirgin farko a ranar zai baro tashar Idu da ke Abuja da ƙarfe 8.45 na safe, ya iso Kubwa 9.05 sannan ya sauka a tashar Rigasa da ke Kaduna da misalin 12.42 na rana. Daga Kaduna kuma jirgi zai baro Rigasa da misalin ƙarfe 2.30 na rana ya isa Kubwa da ƙarfe 8.40 na yamma. Sanarwar ta ƙara da cewa daga bisani za a ware kowace ranar Laraba domin aikin kula da lafiyar jiragen da ke aiki a layin na Abuja zuwa Kaduna. Shekara 1 bayan rushewa, har yanzu ba...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce kasarsa za ta gwammace ta fuskanci mayar da takunkumin da aka kakaba mata, maimakon ta mutunta bukatar Amurka da ke neman Iran din ta mika dukkanin tataccen Uranium da take da shi. Da yake zantawa da manema labarai kafin ya bar birnin New York zuwa birnin Tehran, Pezeshkian ya yi karin bayani kan kokarin diflomasiyya a lokacin babban taron Majalisar Dinkin Duniya, wanda ya hada da ganawa da shugabannin kasashen Faransa, da Finland, da Switzerland, da Norway, da Iraki, da Bolivia, da kuma majalisar kungiyar Tarayyar Turai. Yayin da yake nuni da cewa an cimma yarjejeniya da bangarorin Turai, ya nuna rashin jituwar da cewa duka daga bangaren Amurka ne. “Mun cimma yarjejeniya...
Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC) ta bayyana cewa jiragenta da ke jigilar fasinjoji daga Abuja zuwa Kaduna, za su koma aiki a mako mai zuwa. Mai magana da yawun NRC, Callistus Unyimadu, ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da hukumar ta fitar a jiya Asabar, duk da yake bai sanar da haƙiƙanin ranar da za a koma aikin ba. Tun daga shekarar 1899 Faransa take haddasa mana rikici — Nijar Ɗalibi ya kashe malaminsa har lahira a Kuros Riba Callistus, ya ƙara da cewa matakin ya biyo bayan nasarar kammala gyare-gyare da bincike a ɓangaren da aka samu matsala a baya-bayan nan. A cewarsa, hukumar na yin aiki ba tare da gajiyawa ba don...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Yawan ribar da manyan kamfanoni na kasar Sin suke samu ta karu da kashi 0.9 cikin 100 a mizanin shekara-shekara a cikin watanni takwas na farkon shekarar 2025, lamarin da ya farfado da raguwar da aka samu da kashi 1.7 cikin 100 a tsakanin watannin Janairu zuwa Yuli, kamar yadda alkaluman hukuma suka nuna a yau Asabar. Jimillar ribar da kamfanonin da ke samun makudan kudin shiga na kasuwanci a shekara na akalla yuan miliyan 20 (kimanin dalar Amurka miliyan 2.81) ta kai kusan yuan tiriliyan 4.7 a cikin watannin takwas, a cewar hukumar kididdiga ta kasar Sin. A cikin watan Agusta, ribar da manyan kamfanonin suka samu ta farfado sosai, inda ta karu da kashi 20.4 cikin 100 a...
Yunkurin kasashen rasha da china na jirkinta dawowa da iran takunkumi har na tsawon wata 6 bai yi nasara ba a kwamitin tsaro na MDD saboda kasashe 4 ne suka nuna goyon bayansu da suka hada da kasashen China Rasha Pakistan da kuma Aljeriya, yayin da kasashe 9 kuma suka nuna rashin amincewa da shirin ciki harda mambobin kwamitin tsaro na mdd wato kasashen Birtaniya, Faransa da kuma Amurka. Kasar Rasha taki amincewa da wannan lamarin na dawo da takunkumin madd kan kasar iran , kamar yadda ita ma kasar china ta nuna rashin amincewarta afili da wannan mataki. Ana sa bangaren shugaban kasar iran Masud pezeshkiyaan ya bayyana cewa da sannuu Tehran za ta yi galaba akan wannan batun...
Yayin da aka ce jam’iyyun siyasa a jamhuriya ta farko, sun fi karkata kan yanki, an yi yunkurin kafa jam’iyyun kasa a jamhuriya ta biyu da gangan. A wancan jamhuriyar (1979–1983), manyan jam’iyyun siyasar Nijeriya su ne GNPP, NPN, NAP,NPP, PRP, da kuma UPN. Duk da cewa, jam’iyyun sun banbanta a akida; amma ana ganin jam’iyyun UPN da PRP, a matsayin na masu fafutuka da kuma jajircewa, domin kuwa jam’iyyar UPN ta tsaya tsayin-daka wajen aiwatar da manufofinta. An gina tsarin jam’iyyar bisa manyan manufofi hudu kamar haka: ilimi kyauta tun daga makarantar reno har zuwa manyan makarantu, harkar kiwon lafiya kyauta, hadin gwiwar karkara da ci gabanta da kuma samar da cikakkun ayyukan yi masu dorewa. Wadannan alkawura, an...
Sakataren Majalisar Koli ta Tsaron kasar Iran ya bayyana cewa, Tehran za ta katse yarjejeniyarta da take yi da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, tare da daina bada hadin kai ga binciken makamai na kasa da kasa, idan har aka aiwatar da tsarin “sake dawo mata da takunkuman Majalisar Dinkin Duniya. Sakataren Majalisar ta Iran Ali Larijani ya sake nanata kudurin Iran na cewa ba da ta niyyar yin amfani da makamin nukiliya – ko dai a yanzu ko a nan gaba. Ya kuma ce ayyukan wuce gona da iri da Amurka da Isra’ila suka yi kan cibiyoyin nukiliyar Iran guda uku a watan Yuni ya sanya tattaunawar ta zama “bazara”. Yau Juma’a ne kwamitin sulhu na...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya yi kakkausar suka ga kasashen Turai uku da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar nukiliyar ta shekarar 2015, inda ya zarge su da yin “ba bisa ka’ida ba da kuma rashin da’a” ta hanyar neman mayar da takunkumin da kwamitin sulhu na MDD ya kakabawa Iran ta hanyar da ta dace. A wata tattaunawa da ta yi da sakatariyar harkokin wajen Birtaniya Yvette Cooper a ranar Alhamis, Araghchi ya bayyana cewa, kasashen Turai ba su da hujja kan kokarin da suke yi na maido da kudurorin da aka soke a baya. Araghchi “ya yi kakkausar suka kan matsayin kasashen Turai uku da cewa bai dace ba, ba bisa ka’ida ba kuma maras nauyi,” in...
Kwararan bayanai na nuni da cewa tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya fara tattaunawa da Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, kan shirin komawa jam’iyyar. Majiyoyi daga cikin APC a Kano sun bayyana cewa Kwankwaso ya rubuta wasiƙa zuwa sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa a Abuja, yana sanar da aniyarsa ta komawa jam’iyyar. An rufe wurin haƙar zinare a Kebbi Sauya Sheƙa: Kwankwaso ya gindaya sharuɗa kafin sake komawa APC Sai dai Aminiya ba ta iya tabbatar da hakan ba ya zuwa lokacin hada wannan rahoton. Wata majiya daga sakatariyar APC ta ƙasa kuma ta tabbatar da cewa ana ci gaba da tattaunawa tsakanin Kwankwaso da Farfesa Nentawe kan sauya shekar, kuma maganar ta yi nisa...
Har kullum Sin tana nacewa shawarwari, da tuntubar juna a matsayin muhimman matakan kyautata hadin gwiwa dake share fagen inganta cudanya. Tare da hakan, Sin na fatan Amurka za ta kaucewa kokarin dakile ci gabanta. Kuma duk wasu matakai na matsin lamba daga bangare guda kan kasar Sin, ba za su taba yin nasara ba, kamar dai yadda muka gani a baya. Don haka, a wannan gaba da ake ta samun karin sakamakon kyautata muamala da gudanar da shawarwari, kamata ya yi bangaren Amurka ya kauracewa kakaba shingen cinikayya, wanda ka iya gurgunta nasarorin da aka riga aka cimma. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na...
Sabon kwantiragin ya nuna Arsenal na son kare shi daga ƙungiyoyi manya na ƙasashen Turai irin su Real Madrid da Manchester United. Arteta na fatan hakan zai taimaka wajen cika burinsa na lashe gasar Firimiya. Haka kuma, abokin Saliba a tsaron baya, Gabriel Magalhães, ya tsawaita kwantiraginsa har zuwa shekarar 2029. Arsenal za ta kara da Newcastle a filin St James’ Park a ranar Lahadi, inda ake sa ran haɗin Saliba da Gabriel zai ƙara ƙarfafa bayan ƙungiyar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban gwamnatin riƙon ƙwaryar Syria Ahmed al-Sharaa ya shaida wa babban taron Majalisar Dinkin Duniya cewa ƙasarsa ta sake ƙwato matsayinta a idon duniya. Wannan ne karon farko cikin kusan shekaru 60 da wani shugaban Syria ya yi jawabi a taron MDD. Siyasa ba ta yiwuwa da rowa — Gwamna Buni Za a gudanar da taron kiwon lafiya na farko a Gombe Al-Sharaa ya zama shugaban Siriya na farko da ya yi jawabi a Majalisar Dinkin Duniya tun bayan da Noureddine Attasi ya yi jawabi a shekara ta 1967, jim kaɗan bayan yaƙin Larabawa da Isra’ila, a lokacin da Damashka ta rasa iko da tuddan Golan wanda Isra’ila ta ƙwace a shekarar 1981. Al Sharaa ya ce yaƙin basasa ya...
Majalisar Dokoki ta Kasa ta ɗage ranar dawowarta daga hutu zuwa 7 ga watan Oktoba, 2025. Karin bayani na tafe..
Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya ayyana gobe Talata, a matsayin ranar ɗaya ga watan Rabi’ul Thani, 1447 bayan hijira, wanda ya kawo ƙarshen watan Rabi’ul Awwal, 1447, daidai da ranar 23 ga Satumba, 2025. Sanarwar ta fito ne a wata takarda da Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaid, wanda shi ne shugaban kwamitin da ke bai wa Majalisar Sarkin Musulmi shawara kan al’amuran addini, ya sanya wa hannu ya kuma raba wa manema labarai. A sanarwar, Sarkin Musulmi bai fayyace wuraren da aka ga sabon watan ba, sai dai ya bayyana cewa ya gamsu da sahihan rahotannin da aka gabatar, lamarin da ya sa ya ayyana ganin watan a hukumance. Ya yi addu’ar Allah Ya kawo zaman lafiya da...
Pezeshkian: Kasashen Da Ba Su Cika Alkawura Da Suka Dauka Ba Suke Zargin Iran Kan Rashin Mutanta Yarjejeniyar Nukiliya
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Kasashen da ba su cika alkawuran da suka dauka ba suke zargin Iran da rashin mutunta yarjejeniyar makamashin nukiliya Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Kasashen da ba su cika alkawuran da suka dauka ba, a yanzu suke zargin Iran da kin mutunta yarjejeniyar makamashin nukiliyar. A cikin wata hira da gidan talabijin na CCTV na kasar China, Pezeshkian ya ce, “Suna sa ran za a aiwatar da yarjejeniyar manyan tsare-tsare na shekaru 25 da aka tsara a baya tsakanin Iran da China.” Pezeshkian ya yi ishara da gazawar Amurka da kasashen Turai wajen cika alkawuran da suka dauka karkashin yarjejeniyar makamashin nukiliya, yana mai cewa, a yau kasashen da ba su...
Ya gargadi cewa, tarihi ba zai gafarta wa shugabannin Arewa ba idan suka kasa daukar matakin gaggawa wajen dakile kashe-kashe, garkuwa da mutane da rikice-rikicen da ke addabar yankin. Ya ce shiru da fifita wasu akan wasu daga cikin shugabanni suna kara ta’azzara matsalar tsaro a jihohin Zamfara, Kaduna, Katsina, Filato da Benuwe. Ya bayyana cewa akwai damuwa matuka yayin da ‘yan bindiga ke ci gaba da addabar al’umma, wasu daga cikin manyan mutane na fifita shirya shagulgula masu tsada maimakon kiraye-kirayen tarurrukan neman mafita na gaske don kawo karshen wannan rikici. “Lokacin yin shiru ya wuce, yanzu ne lokacin daukar mataki. Tarihi ba zai gafarta wa halin ko-in-kula ba a lokacin da ake bukatar mataki fiye da...
Wanda zan iya tunawa za su kai goma haka. Ko akwai wani fim wanda bayan fitar sa ka samu ƙalubale daga dangi ko wajen masu kallo? Gaskiya a fim dai har yanzu ban samu wani ƙalubale ba, saboda duk abin da nake fitowa a rol na malunta ne. Kawai dai akwai wata waƙa da na yi bidiyonta a kanta ne gaskiya na fuskanci ƙalubale sosai, dan akwai wanda ya taɓa kira na yana hawaye ya ce min me ya ja min wannan harka haka har na fito ina rawa da jaruma?. To, sai na ji ban ji daɗi ba a lokacin, dan akwai gidajen TƁ da suka karɓa suke haskawa, nayi sauri na hana a haska ɗin. Sai kuma wani...
Shugaban kasar Iran Masud pezishkiyan ya bayyana cewa Iran ba za ta mika wuya ga bukatun da suka wuce kima ba, kuma za ta iya shawo kan duk wani takunkumi da aka kakaba mata, Shugaban ya fadi haka ne a wajen bukin karrama yan kasar da suka samu lambobin yabo a gasar Olympic ta kimiyya ta duniya , bayan da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya kada kuriar amincewa da kudurin dawo da takunkumi dake da alaka da shirinta na nukiliya. Haka zalika shugaban kasar yace makiya suna iya kai hari kan sakamakon binciken fasaha da aka yi, amma kwararru da masana ilimin kimiya wadanda suka samar da wadannan naurorin su ne hakikanin gaskiyar dukiya ga kasarmu, don haka...
Shugaba kuma Babban Jami’in Gudanarwa na Matatar Man Fetur na Kamfanin Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana cewa tun bayan fara samar da man fetur a shekara guda da ta gabata, matsalar dogon layin man fetur da ta shafe shekara 50 ana fama da ita ta zama tarihi. A lokacin wani taron bita da aka gudanar don murnar cika shekara ɗaya tun bayan ƙaddamar da samar da man fetur daga masana’antar dake samar da ganga 650,000 a kowace rana, Dangote ya jaddada cewa Ƴan Nijeriya sun sha fama da dogon layin mai tun daga 1975, amma wannan matsala ta fara zuwa karshe tun lokacin da masana’antar ta fara aiki a ranar 3 ga Satumba, 2024. Dangote ya yi nuni da kalubale...
A baya, ƙasashe biyu kawai na Afirka ba sa shigo da man fetur, amma abin takaici, yanzu sun koma shigo da kaya. Wannan yana da illa ga Afirka,” in ji shi. Dangote ya bayyana cewa aikin masana’antar ya kasance mai haɗari sosai. Ya ce ya samu gargaɗi sau da dama daga masana harkokin mai, masu zuba jari, da jami’an gwamnati na cikin gida da waje, waɗanda suka yi jayayya cewa irin wannan aikin masana’antar mai girma manyan ƙasashe ne kaɗai ke iya yi, ya amince cewa da aikin ya gaza, zai rasa dukiyoyinsa ga masu ba da rance. “Yanke shawarar gina masana’antar ba abu ne mai sauƙi ba. Idan ya gaza, masu ba da rance za su daka wawa a...
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Zamanin kebe kai ya ƙare, Haɗin gwiwar Iran da Rasha ya cimma abin koyi mai nasara A yayin ganawarsa da ministan makamashin kasar Rasha Sergei Tyswell da tawagarsa, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Nasarar da aka samu na hadin gwiwa tsakanin kasashe masu cin gashin kai kamar Iran da Rasha, ya tabbatar da cewa zamanin kebe kai a duniya ya kare. Ya kuma jaddada cewa, wadannan kasashe suna iya samun ci gaba da bunkasa ba tare da bukatar ko dogaro da karfi mai amfani da bangare guda. Shugaban na Iran ya bayyana jin dadinsa da ci gaban hadin gwiwar kasashen biyu, musamman a fannin sufuri, makamashi, da ayyukan samar da wutar...
Kafofin yada labaran Isra’ila sun rawaito cewa, an gudanar da wani dogon zaman tattaunawa a birnin London a yammacin jiya tsakanin ministan harkokin wajen Syria Asaad al-Sheibani da ministan kula da tsare-tsare na Isra’ila Ron Dermer, tare da halartar jakadan Amurka na musamman Tom Barak. Kafofin yada labaran Isra’ila sun bayyana cewa ganawar ta dauki tsawon sa’o’i biyar, inda bangaren Syria ya gabatar da martaninsa kan shawarar da Isra’ila ta gabatar na cimma yarjejeniyar tsaro, inda ta ce an samu ci gaba a tattaunawar. A baya dai bangarorin biyu sun gana a zagaye na biyu da aka sanar, ban da kuma tarukan sirri da suka gudanar a lokuta daban-daban wand aba a sanar ba, da nufin kulla alaka ta siyasa...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A yau ne Gwamna Siminalaye Fubara ke dawowa kujerarsa a matsayin gwamnan Jihar Ribas bayan dakatarwa da ayyana dokar ta baci na watanni shidda da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi a jihar. Manazarta dai na hasashen wannan dawowar zata bude wani sabon babi a siyasar jihar Ribas. NAJERIYA A YAU: Matsayin Doka Kan Hawa Mumbari Ba Tare Da Izinin Gwamnati Ba DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya Yayin da wasu ke ganin gwamna Fubara zai koma bakin aiki ne ya cigaba da gudanar da mulkin jihar kamar yadda ya barta, wasu kuwa gani sukeyi akwai babban kalubale dake gaban gwamnan. Domin sauke shirin, latsa nan
Wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Folasade Boriowo, ya fitar, ta ce a karon farko cikin shekaru da dama, daliban Nijeriya za su ci gaba da karatun tarihin Nijeriya tun daga Firamare 1 zuwa karamar Sakandare 3 yayin da daliban SSS 1 – 3 za su koyi sabon darasin da aka samar na ‘Civic and Heritage Studies’, wanda ya hada tarihin Nijeriya da Ilimin zamantakewar Jama’a. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Yakin Haraji Da Cinikayya Ba Zai Gurgunta Fifikon Da Sin Ke Da Shi A Fannin Raya Masana’antun Sarrafa Hajoji Da Kasar Ta Gina A Tsawon Lokaci Ba
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce alkaluman baya bayan nan da aka fitar cikin Mujallar Economist, sun shaida yadda hada-hadar cinikayyar fitar da hajoji ta kasar Sin ke kara bunkasa cikin sauri a shekarar nan ta bana, inda fannin ke samun karuwar abokan hulda, da daidaiton matsayi cikin tsarin samar da hajojin masana’antu na kasa da kasa. Kakakin ya kara da cewa, kasashen duniya suna maraba da hajojin kasar Sin, kuma yakin ciniki da haraji ba su yi wani babban tasiri kan kasar Sin ba. A fannin hada-hadar cinikayya, sanya shinge ba alama ce ta karfin gwiwa ba, kuma katangar da Amurka ke ginawa kanta, daga karshe za ta illata karfinta ne. Lin Jian, wanda ya...
Ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomin Jihar Yobe (ALGON) ta karrama Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, da lambar yabo ta karramawa bisa himmar ayyukan raya ƙasa da gwamnatinsa ke gudanarwa a faɗin jihar. Karramawar, wacce aka bayyana a matsayin irinta ta farko a tarihin Jihar Yobe, shugabannin ƙananan hukumomi 17 na jihar suka ba da ita ga gwamna. Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabala Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno Da yake jawabi, shugaban ƙungiyar ALGON a Jihar Yobe, kuma shugaban ƙaramar hukumar Damaturu, Alhaji Bukar Adamu, ya yaba da yadda Gwamna Buni yake gudanar da harkokin mulki na bai ɗaya. Ya ce nasarorin da aka samu sun haɗa da fannoni na...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rikicin kwamitin gudanarwa da malaman Kwalejin Fasaha ta Tarayya da ke Bida (Bida Poly), ya ƙara ƙamari bayan da makarantar ta dakatar da ayyukan Kungiyar Malamai (ASUP) sannan ta kawo sojoji domin kula da jarrabawa da dalibai ke gudanarwa. Ƙungiyar ASUP reshen kwalejin ta shiga yajin aiki mara wa’adi, domin neman a biya su alawus ɗin ƙarin aiki na watanni 18 da suka wuce. Ƙungiyar ta umarci mambobinsu da kada su gudanar da jarrabawar zangon da ta fara ranar Litinin, 15 ga Satumba, 2025. Wani ma’aikacin makarantar ya shaida wa wakilinmu cewa sojojin an gayyace su ne domin kare ɗalibai da wasu malamai daga shirin da ASUP ke yi na hana gudanar da jarrabawa. ’Yan bindiga sun kai wa sojoji...
Majalisar dattawa ta dakatar da Sanata Akpoti-Uduaghan a ranar 6 ga Maris, 2025, na tsawon watanni shida. Duk da cewa an kalubalanci lamarin a kotu, amma babbar kotun tarayya ba ta bayar da wani umarni na soke dakatarwar ba ko kuma tilasta sake dawo da ita bakin aiki. A ranar 4 ga Satumba, 2025, Sanatar ta sanar da ofishin magatakarda akan aniyar ta na ci gaba da ayyukan majalisa, nan take, ofishin ya mika wasikar ga shugabannin majalisar dattawan. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) ya roƙi Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na KEDCO ya gaggauta dawo masa da wuta bayan rasuwar wasu marasa lafiya da ke samun kulawa ta ceton rayuwada na’ura. Wata sanarwa da kakakin asibitin, Hauwa Inuwa Dutse ta fitar ta nuna takaici bisa rasuwar marasa lafiyan, tana mai cewa mace-macen waɗanda za a iya kauce wa ne idan akwai tsayayyiyar wutar lantarki. Ta bayyana cewa Asibitin yana AKTH yakan biya kuɗin wuta akai-akai daga kuɗaɗen shigansa, kuma yana kashe kuɗaɗe wajen sanya mai a janareto domin amfani idan aka ɗauke wuta daga KEDCO. Don haka, “Hukumar gudanarwar Asibitin AKTH na roƙon Kamfanin KEDCO da ya taimaka wa ayyukan asibitin ta hanyar dawo da wutar a yayin...
Kamar yadda Oche, wadda ‘ya’yan ‘yar’uwarta suke zuwa makarantar Reno ta Oluwami da Firmare , da take Abuja inda shekarun baya suke biyan wajen Naira 600,000 ko wane zangon karatu, saboda wasu haraje- harajen da aka haɗa da su ciki. “Maganar gaskiya kowace shekara idan za’a shiga sabon zangon karatu, makarantu su kan ƙara kuɗin makaranta, su ƙara wasu sabbin abubuwa, kamar su kuɗin ICT, wasanni tsaro. Sai dai ƙarin da akwai matuƙar matsala.” A makarantar( Prime School ) da ke, Karu,inda aka ƙiyasta ana biyan kusan Naira 300, 000, kowane zangon karatu,wani Malamin da baya son a ambaci sunansa ya ce, akwai ƙarin kuɗin makaranta waɗanda suna da alaƙa ne da lamarin daya shafi kayn zuwa makaranta, bunƙasar makaranta,...
Babban sakatare tsaron kasa na Iran Ali Larijani ya fadi cewa ya zama wajibi kasashen musulmi su hada kai waje guda don tunkarar rashin hankalin Isra’ila da take yi kan alummar falasdinu. A cikin wani bayani da ya aike da shi a shafinsa na X ya ce wannan mataki zai tilastawa shugaban Amurka yin gaggawa wajen mika umarninsa ga gwamnatin Isra’ila bisa hujjar kawo zaman lafiya a duniya da kuma bada kyautar zaman lafiya ta Nobel. Kasar Qatar ta sanar da kiran zaman gagganawa na kasashen larabawa da na musulmi a ranar litinin mai zuwa domin tattaunawa game da harin da Isra’ila ta kai domin kashe jagororin kungiyar Hamas a kasarta. Manyan jami’an hamas da suke tattaunawa kan batun bukatar...
A cikin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 14, kasar Sin ta samu ci gaba a bangaren sufurin jiragen kasa na cikin birane, da motocin bas na zirga-zirgar yau da kullum, da zirga-zirga cikin aminci. A halin yanzu, akwai layukan dogo 331 a cikin birane 54 dake fadin kasar, inda jimilar tsawonsu ta kai kusan kilomita 11,000, wanda ke matsayi na farko a duniya. Babban rukunin gidajen rediyo da talabin na Sin wato CMG, ya samu wannan kididdiga ne daga ma’aikatar kula da sufuri da jigilar kayayyaki ta kasar a kwanan nan. A yanzu haka, sama da mutane miliyan 200 a kasar Sin sun zabi hanyoyin sufuri masu kiyaye muhalli a kowace rana, wadanda suka hada da miliyan 100 da suke hawa jiragen kasa masu inganci...
Sanata Ibrahim Lamiɗo, mai wakiltar Sakkwato ta Gabas, ya nuna damuwarsa kan yadda matsalar tsaro ke ƙara tsananta a yankinsa, inda ya ce hare-hare da satar mutane sun zama ruwan dare. A hirarsa da manema labarai, Sanatan ya ce: “Gaskiya abin tsoro ne rayuwa a Gabashin Sakkwato. Kusan kowace rana sai an kai hari, an kashe mutane ko kuma an sace su. Muna cikin tashin hankali sosai.” ’Yan bindiga sun harbi fasinjoji 2, sun sace makiyaya a Neja Gwamna ya aike wa majalisa dokar haramta auren jinsi ɗaya a Kano Ya bayyana cewa duk da ƙoƙarin da yake yi wajen ganin an kawo gyara, wasu ’yan siyasa suna kawo cikas. Sai dai ya ce ba zai fasa jajircewa wajen ganin...
Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Sanin Makamar Aiki ta Najeriya (NARD), ta bai wa Gwamnatin Tarayya sa’o’i 24 don ɗaukar mataki game da buƙatunsu, ko kuma su tsunduma yajin aiki. Wannan matakin ya biyo bayan cikar wa’adin gargaɗin kwanaki 10 da suka bayar a baya. Gwamnatin Tarayya za ta gurfanar da shugabannin Ansaru 2 a kotu Tinubu ya bayar da umarnin a sake karya farashin kayan abinci Tuni wasu likitoci a Abuja da Jihar Oyo suka tsunduma yajin aiki. Likitocin, waɗanda yawancinsu ke aiki a Asibitocin Koyarwa da na Ƙwararru, suna yawan tafiya yajin aiki saboda rashin biyan wasu haƙƙoƙinsu. A halin yanzu, suna neman a biya su kuɗin horon 2025 da bashin albashin da suka bi, sannan sun buƙaci a...
A yau Laraba kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum, inda ya bayyana cewa, kasar Sin ta soki lamirin harin da aka kaddamar a birnin Doha, fadar mulkin kasar Qatar a jiya Talata, tana kuma adawa da matakin Isra’ila na cin zarafin ikon mulkin kasa da tsaron kasa na Qatar. Lin Jian ya ce kasar Sin na kira ga dukkan bangarorin da abin ya shafa, musamman Isra’ila, da su kara kokari wajen dakile rikicin, da sake fara tattaunawa maimakon akasin hakan. Dangane da sanarwar da Isra’ila ta gabatar wa Amurka kafin ta kaddamar da harin ta sama, Lin Jian ya bayyana cewa, matakin da Isra’ila ta dauka na da...
A halin yanzu, sauye-sauyen da ba a taba ganin irinsu ba a cikin karni guda suna ci gaba da habaka cikin sauri, yayin da mulkin kama-karya, son kai, da kuma kariyar tattalin arziki suka kara yawaita. A wannan yanayi, a wajen taron yanar gizo na shugabannin kasashen BRICS da aka gudanar a ran 8 ga watan nan da muka ciki, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da shawarwari uku don karfafa “hadin kan kasashen BRICS” da kuma kafa kyakkyawar makomar bil’adama ta bai daya. Wato na farko nacewa ga kasancewar mabambantan bangarori a duniya. Bugu da kari, a kare adalcin duniya domin ci gaba da bude kasuwanci don samun nasara ga kowa, da kuma kiyaye tsarin tattalin arzikin duniya....
Majalisar Dattawa ta sanar da cewa ba ta amince da buƙatar Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar Kogi ta Tsakiya kan komawa bakin aiki, saboda har yanzu ba a kammala shari’ar dakatar da ita ba. Tun dai a ranar 8 ga watan Agustan bana ne Sanata Natasha ta rubuta wa majalisar wasiƙa, inda ta sanar da ita shirinta na komawa bakin aiki a ranar 4 ga watan Satumba, tana mai kafa hujja da cikar wa’adin watanni shida da aka dakatar da ita. NAJERIYA A YAU: Tasirin Takaddamar NUPENG Da Dangote A Kan Tattalin Arzikin Najeriya Ana zargin jami’in sibil difens da harbe abokin aikinsa a Abuja Sanatar ta bayyana cewa kotun tarayya ta yanke hukunci a watan Yulin da ya gabata...
Gwamnatin Tarayya, NUPENG Da Ɗangote Sun Fara Tattaunawa Don Kawo Ƙarshen Yajin Aikin Ma’aikatan Mai
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da jami’an Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA), wakilan kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC, shuwagabannin kamfanin ‘MRS Holdings Limited’ da kuma kungiyar ‘yan kasuwa ta kasa (TUC). Da yake bayyana bude taron, Minista Dingyadi ya jaddada aniyar gwamnati na sulhu a tsakanin kungiyar da masu gudanar da masana’antu. Ya bayyana bangaren mai da iskar gas a matsayin jigon tattalin arzikin Nijeriya, yana mai gargadin cewa tsawaita yajin aikin zai haifar da mummunan sakamako ga kasar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya...
Kungiyar Hamas ta jaddada cewa: Tana maraba da duk wani yunkuri da zai taimaka a fagen dakatar da ta’addanci kan al’ummar Falasdinu Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta jaddada hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a yammacin jiya Lahadin da ta gabata cewa, tana maraba da duk wani yunkuri da zai taimaka a fagen yunkurin da ake yi na dakatar da kai hare-hare kan al’ummar Falasdinu, tana mai bayanin cewa ta samu wasu ra’ayoyi daga bangaren Amurka ta hanyar masu shiga tsakani don cimma matsaya. A cikin wata sanarwa da kungiyar ta Hamas ta fitar ta ce: “Ta samu wasu ra’ayoyi daga bangaren Amurka ta hanyar masu shiga tsakani don cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta. A wannan...
Yayin da makarantu a fadin Najeriya ke dawowa sabuwar zangon karatu ta shekarar 2025/2026 a yau Litinin, iyaye sun koka kan mummunar ƙalubalen tattalin arziki da ke hana su samun sauƙin biyan kuɗin makaranta da sauran kayayyakin karatu. Rahotanni daga jihohi daban-daban sun nuna yadda tsadar rayuwa da hauhawar farashin kaya suka zame wa iyaye da ɗalibai babban cikas, inda wasu ke neman rance domin ganin ’ya’yansu ba su zauna a gida ba. Kukan Iyaye A hirarraki da aka yi da iyaye da dama, sun bayyana cewa duk zangon karatu yanzu yana zama tamkar shiga jana’iza, inda suke binne albarkatunku da nutsuwarsu da farin cikin gida. Misis Victoria Edem, uwa ce mai yara uku daga garin Kalaba a Jihar Kuros...
’Yan ta’adda sun kashe aƙalla mutum 63 a wani mummunan hari da suka kai a garin Darul Jamal, kusa da kan iyakar Najeriya da Kamaru, a yankin Bama na Jihar Borno. Gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum, ya tabbatar da cewa daga cikin waɗanda suka rasa rayuka akwai sojoji 5 tare da fararen hula 58. Tsagin NNPP na ƙasa ya yi watsi da korar Abdulmumin Jibrin Kofa ’Yan bindiga sun kashe jami’an Sibil Difens 8 a Edo Wannan harin ya faru ne da daddare a ranar Juma’a, inda maharan haye a kan ɗaruruwan babura, suka fara harbe-harbe da ƙone gidaje. Wani mazaunin garin, Malam Bukar, ya shaida wa manema labarai cewa: “Sun shigo suna ta kabarbari da harbi kan mai uwa...