2025-05-01@09:18:51 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1540

«Allah Ya ba shi»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Yadda za ku hada: Idan kuka samu filawa kamar kofi daya, sai suga kamar babban cokali biyu, sai gishiri kadan haka, sai baikin fauda rabin babban cokali , baikin soda rabin babban cokali, kwai daya, sai mai babban cokali biyu, madara rabin kofi. Sai ki tankade filawar sannan ki zuba suga ki zuba gishiri baikin fauda ki zuba duk kayan da na ambata sai ki cakuda su gaba daya, ki dame su sosai, sannan ki dora firayin fan dinki idan ya danyi zafi sai ki fara zubawa daidai fadin da kike so, sannan za ki iya yi mishi dan kunne haka a sama zai dauki hankalin yara, amma za ki rage wuta ne sosai saboda shi baya son wuta, idan...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Masu iya magana kan ce, banza ba ta kai zomo kasuwa. Mai yiwuwa hakan ne ya sa matasan da ake zargi da aikata manyan laifuffuka shiga ofishin ’yan sanda, su kuma fita ba tare da wani ya harare su ba, balle ya kama su. ’Yan sandan dai sun ce wannan wata dabara ce ta yakar aikata manyan laifuka irin su sata da fashi da makami da ƙwacen waya da fyaɗe kai har ma da satar mutane domin karɓar kuɗin fansa a tsakanin matasa. NAJERIYA A YAU: Ainihin Abin Da Ke Hana Matan Arewa Koyon Ilimin Kimiyya DAGA LARABA: Dalilan Ɓaraka A Tsakanin Iyayen Riƙo Da Ƴaƴan Riƙo Ko yaya wannan dabara take aiki?...
    Gwoza dai tana daga cikin wuraren da Boko Haram suka mamaye a baya kafin sojoji su ƙwato ta. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jami’an rundunar ’yan sandan jihar Edo sun ceto ɗalibai 10 da wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Edo. An kashe ɗaya daga cikin ’yan bindigan, a yayin musayar wuta da ’yan sanda a lokacin aikin ceto, yayin da sauran suka tsere da raunukan harbi. Daily Trust ta ruwaito cewa an yi garkuwa da ɗaliban ne a ranar 16 ga Afrilu, 2025, a kan hanyarsu ta zuwa Jami’ar Babcock don taron shekara-shekara na GYC Africa. Kakakin rundunar, SP Kontongs Bello, wanda ya tabbatar da ceton, ya ce da samu rahoton sace daliban, kwamishinan ’yan sandan jihar, Funsho Adegboye, ya tura ’yan sanda na musamman tare da ’yan banga da maharba cikin daji domin ceto su da kuma...
     Sojojin Sudan sun sanar da kashe mayakan dakarun kai daukin gaggawa 70, ciki har da kwamandojin mayakan a birnin a El Fasher fadar mulkin jihar Darfur ta Arewa A ranar Alhamis ne rundunar sojin Sudan ta sanar da kashe mayakan da jami’an dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces fiye da 70 da suka hada da kwamandojin ‘yan tawaye a shiyar kudu maso gabas da arewa maso gabashin El Fasher. Kamfanin dillancin labaran Sudan (SUNA) ya watsa rahoton cewa: A ranar Alhamis ne sojojin kasar Sudan tare da hadin da tallafin dakarun hadin gwiwa na kungiyoyin fafutuka, da hukumar leken asiri ta kasar da ‘yan sanda, suka dakile wani mummunan hari da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support...
    Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta yi nasarar kubutar da wasu mutane shida da aka yi garkuwa da su, a wani samame da ta gudanar cikin gaggawa tare da tabbatar da ganin an dawo da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar.   A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, DSP Yazid Abubakar ya fitar, ya ce a ranar 16 ga Afrilu, 2025, da misalin karfe 1:45 na rana, tawagar hadin guiwa da ta kunshi jami’an ‘yan sanda da kuma jami’an kare hakkin jama’a (CPG) suna sintiri a kan babbar hanyar Anka-Gummi, inda suka gano wata mota samfurin Peugeot 206 da suka yi garkuwa da su a gefen hanya.   A cewar sanarwar, ba tare...
    Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bukaci Kiristoci da su yi tunani a kan darussa, muhimmaci, da kuma kyawawan dabi’u na makon Easter.   Gwamna AbdulRazaq a wani sako da ya aike a Ilorin, ya taya mabiya addinin kirista a jihar da ma fadin Najeriya murnar bikin Easter.   Gwamnan ya ce nasarar da Yesu Kiristi ya samu a fuskantar wahala, wanda bikin Ista ke alamta, ya kamata ya fitar da imani ga Allah da kuma yuwuwar da ba su da iyaka da ke zuwa tare da samun bangaskiya mara girgiza cikin ikonsa.   Ya yi addu’ar Allah ya sa lokacin Easter ya kawo farin ciki da jin daɗi mara iyaka ga kowane gida a jihar da kuma bayansa  ...
    Kakakin majalisar dokokin jihar Neja, Barr. Abdulmalik Sarkin-Daji, ya mika sakon taya murna ga al’ummar kiristoci a jihar da ma sauran sassan jihar bisa nasarar kammala azumin Easter na kwanaki 40.   A madadin shugabanni da membobin majalisar ta 10, shugaban majalisar ya yaba wa mabiya addinin kirista saboda sadaukarwar da suka yi da kuma ci gaban ruhaniya a wannan lokaci mai tsarki.   Duk da haka ya yaba musu bisa sadaukarwar da suka yi a wannan lokacin kuma fatan sabunta ruhi da aka samu a lokacin Azumi ya kawo zaman lafiya, farin ciki, da wadata ga kowa.   Barr AbdulMalik Sarkin Daji, ya amince da muhimmiyar rawar da shugabannin addinin Kirista ke takawa wajen jagorantar al’ummar Nijar cewa majalisar...
    Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sanar da cewa za ta gudanar da atisayen harbe-harbe ga sabbin ‘yan sanda a karamar hukumar Birnin Kudu ta jihar Jigawa.   Kwamishinan ‘yan sandan jihar Jigawa, Ahmad Tijjani Abdullahi ya bayyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Dutse babban birnin jihar.   Ya ce, atisayen zai fara ne daga ranar 19 ga Afrilu zuwa 11 ga Mayu 2025 a kauyen Tsohon Kafi da ke Birnin Kudu.   A cewarsa, makasudin bayar da horon shi ne don inganta shirye-shiryen gudanar da aiki, da dabarun sarrafa makamai, da kuma kwarjinin sabbin jami’an ‘yan sandan da aka dauka, a daidai lokacin da rundunar ‘yan sandan Najeriya ta himmatu wajen tabbatar da kwarewa da...
    Jami’an rundunar ’yan sandan jihar Edo sun ceto ɗalibai 10 da wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Edo. An kashe ɗaya daga cikin ’yan bindigan, a yayin musayar wuta da ’yan sanda a lokacin aikin ceto, yayin da sauran suka tsere da raunukan harbi. Daily Trust ta ruwaito cewa an yi garkuwa da ɗaliban ne a ranar 16 ga Afrilu, 2025, a kan hanyarsu ta zuwa Jami’ar Babcock don taron shekara-shekara na GYC Africa. Kakakin rundunar, SP Kontongs Bello, wanda ya tabbatar da ceton, ya ce da samu rahoton sace daliban, kwamishinan ’yan sandan jihar, Funsho Adegboye, ya tura ’yan sanda na musamman tare da ’yan banga da maharba cikin daji domin ceto su da kuma...
    Shugaban ya kuma bai wa masu ruwa da tsaki a fannin cewa, ako da yaushe, kofar Hukumar ta NPA, bode take domin hadaka wacce ta zarce ta gudanar da baje koli. Dakta Dantsoho ya kara da cewa, an samar da tsarin na EPT domin a tabbatar da cewa, ana fitar da kaya zuwa waje, ta hanyar yin amfani da na’urar zamani. “Wannan na zai taimaka matuka wajen kaucewa samun jinkiri da kuma mai-maita aiki da Hukumar ta saba fuskanta a baya,” A cewar Dantsoho. Kazalika, Dantsoho ya bayyana cewa, domin a samu sauki wajen kai kaya a tsakanin masu kananan da matsakaitan sana’oi, musamman duba da cewa, tsarin na EPT, zai taimaka matuka ga guraren da ake adana kaya a...
    Wannan nasarar ta nona irin namijin kokarinda Bankin ya yi na kara habaka samar wa da kansa kudaden shiga duk da matsin tattalin arzikin da kasar nan ke fuskanta. Bugu da kari, kadarorin Bankin sun karu zuwa jimmlar kaso 47 daga Naira tiriliyan 20 a shekarar 2023 zuwa Naira tiriliyan 30, a shekarar 2024. Kazalika, abokan huddar Bankin sun karu zuwa kashi 45, wanda kudaden da suka ajiyarsu ya karu zuwa Naira tiriliyan 22 a shekarar 2024, sabanin yadda ya ke kan Naira tiriliyan 15, a shekarar baya. Duk da samun hauhawan farashin kaya a kasar, Bankin ya samu karin kudaden shigar Bankin, sun karu zuwa kashi 38.9, sabanin kashi 36.1. Bankin na da yakinin samun ribar shiyar da ta...
      Makera, Jihar Kaduna – Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Rt. Hon. Yusuf Dahiru Liman, ya halarci bukukuwan Easter tare da al’ummomin Kiristoci na Gundumar Makera, inda ya bukaci su yi amfani da lokacin wajen tabbatar sa saƙon bangaskiya, yabo, da sadaukarwa da ke tattare da bikin. A jawabin da ya gabatar, Hon. Liman ya jaddada muhimmancin bikin Easter a matsayin lokaci na sabunta dogaro da Allah. Ya kuma bukaci mabiya addinin Kirista da su rungumi koyarwar hakuri, kauna, da kuma fifita bukatun wasu akan nasu. Kakakin ya kuma yi kira ga daukacin jama’ar Jihar Kaduna da su ci gaba da bunkasa zaman lafiya da juna ba tare da la’akari da bambancin addini, kabila ko ra’ayin siyasa ba, yana mai...
    Bugu da kari, saboda karancin masu sayen Kwan, musamman sakamakon matsin tattalin arziki da ake fama da shi, ana kara samun masu sayen Kwan don amfani da shi, wanda hakan ya sanya ake ci gaba da samun Kwan da ba a sayar ba. Misali, a makwanni biyu da suka gabata a garin Jos, an samu matukar raguwar farashin Kwan, inda ake sayar da shi kasa da Naira 3,900 zuwa Naira 4,000. Sai dai, a wannan makon an dan samu karin farashin, wanda ya kai daga Naira 4,200 zuwa 4,300. Daya daga cikin irin wadannan masu kiwon Kajin na gidan gona, Muhammad Bello Ibrahim, ya bayyana bacin ransa kan yadda wannan matsala ke ci gaba da faruwa. “Masu sana’ar kiwon Kajin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kazalika, Injiniya Xie ya kara da cewa, a cikin rubu’in farko na bana, sashen masana’antu na kasar Sin ya taka rawar gani wajen samun ci gaba ba tare da tangarda ba sakamakon ingantuwar tsari da zurfafa ayyuka wajen samar da sabbin ginshikan bunkasa ci gaba mai inganci. (Abdulrazaq Yahuza Jere). Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wata majiya ta ce PDP na cikin mawuyacin hali da kuma rashin tabbas a harkokinta wanda ya tilasta jinkirta taron shiyya da aka shirya gudanarwa a karshen makon da ya gabata. Wata majiya ta ce hukuncin da kotun koli ta zartar akwai rikitarwa saboda an gwama siyasa a ciki. Amma sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na kasa, Debo Ologunagba ya fada a wata hira kan cewa hukuncin kotun koli a bayyane yake kuma yana da fa’ida ga gudanar da jam’iyyar a kasar, ya kara da cewa an ba da ikon magance matsalolin da ke tattare da rikice-rikicen da za su iya shafi masu rike da mukaman jam’iyyar. Ya ce abin da kotun ta yanke hukunci shi ne cewa dole...
    Duk da cewa Atiku ya dage yayin tattaunawar da ya yi da manema labarai bayan ziyarar cewa ganawar ba ta batun siyasa ba ne, amma jawabin El-Rufai ya nuna karara akwai siyasa a cikin ganawar. Bayan ziyarar ‘yan adawa kwanaki kadan da na gwamnonin APC, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya isa gidan Buhari sa’o’i kadan bayan tawagar Atiku, wanda ya kara tsananta siyasa. Ya kuma ba da tabbaci ga ra’ayin cewa shugabannin jam’iyyar APC sun damu da siyasar tsohon shugaban kasar. Masu lura da al’amura siyasa sun bayyana cewa kalaman da Ganduje ya yi bayan ganawar, ya tabbatar da cewa APC na yin duk mai yiwuwa wajen tabbatar da cewa Buhari ya kasance tare da jam’iyya...
    Waɗanda suka take wa Ministan sawu a tafiyar su ne jagororin hukumomin yaɗa labarai da wayar da kai da ke ƙarƙashin ma’aikatar sa. Ya yi zama daban-daban tare da ƙwararru inda suka tattauna kan yadda za a inganta ƙwarewa da kuma kayan aiki na zamani na kafafen yaɗa labarai na gwamnatin Nijeriya.   Ya ce: “Ina sanar da ku waɗannan abubuwan ne domin jaddada ƙudirin gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na ganin an samu cigaba mai ɗorewa a fannin watsa labarai a ƙasar nan.   “Wannan ne ma ya sanya muke gudanar da irin wannan taron bita na ministoci, da kuma shirin ƙaddamar da Taron Tattaunawa da Jama’a a sassan ƙasar nan nan gaba kaɗan.” Idris ya kuma...
    Sojojin kasar Yemen sun bada sanarwan cilla makamai masu linzami kan birnin Telaviv da kuma kan jirgin yakin Amurka saboda tallafawa falasdinawa a Gaza, da kuma maida martani kan hare-haren Amurka kan kasar a jiya Alhamis. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin sojojin kasar na Yemen Burgediya Janar Yahayah Saree yana fadar haka a yau Jumma’a ya kuma kara da cewa sojojin kasar ta yemen sun cilla makami mai linzami samfurin Zulfikar kan wani sansanin sojojin HKI a kusa da tashar jiragen sama na Bengerion dake birnin Yafa (telaviv. Saree ya kara da cewa sojojin, har’ila yau sun kai wasu hare-hare kan jiragen yaki masu daukar jiragen saman yaki na Amurka Harry Truman da kuma USS...
    Hare-haren da jiragen yakin Amurka suka kaiwa lardin Hudaida ya karu zuwa 74. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar gwamnmatin kasar ta Yemen na fadar haka a yau Jumma’a ta kuma kara da cewa dukkan mutanen da suka mutu a hare-haren jiragen yakin Amurka a cibiyar man fetur na Ras Isa a birnin Hudaida fararen hula ne. babu wani mayakin kungiyar Ansarulla ko guda a cikinsu. Labarin ya kara da cewa jiragen yakin Amurka wadanda suka taso daga jiragen ruwa masu daukar jiragen sama na Amurka masu suna USS Harru Truman da kuma USS Carl a tekun red sea, sau kai hare kan ras Isa ne har sau biyu, hare na biyun ya fada ne kan...
    Wani mutum mai suna Muhammad Ma’aba daga ƙauyen Fujeregi da ke Ƙaramar hukumar Gbako a Jihar Neja, ya mutu a hannun tsohon mijin matar da yake shirin aura. Rahotanni sun bayyana cewa, wata Ƙungiya ƙarƙashin jagorancin tsohon mijin matar mai suna Alhaji Yikangi, daga ƙauyen Yikangi Chikan ne suka kai wa Ma’aba hari a tsakanin garin Saganuwa da Fujeregi. PDP ba ta shirya yin zaɓen 2027 ba – Wike Benuwe: Har yanzu ba a gano wasu mutanen ƙauyuka ba – Gwamna Alia Mazauna garin sun shaida wa Daily Trust cewa, tsohon mijin ya saki matar mai suna Fatima Suleiman sau uku, amma ya dage cewa ba za ta ƙara aure ba — ko da ta samu sabon mai neman aurenta....
    A cikin dan kankanin lokacin da wannan hukuma ta fara aiki, ta horar da matasa sama da 100,000 horo kan shirye-shiryen koyon sana’o’i daban-daban a fannonin noma, ICT, kananan sana’o’i da dai sauran su, gwamnatin jihar ta bayar da tallafi da jarin sama da Naira biliyan 1.7 ga wadannan matasa domin fara sana’o’i. Har ila yau, ya saukaka wa wadannan matasa rayuwa sa suka cancanta a cikin jihohi da tarayya. Jihar jigawa jiha ce mai girma ta kuma yi fice a fannin noma a kokarin gwamnati na inganta rayuwar al’umma ta hanyar sabbin manufofin noma da ya zama abin a yaba. Domin tabbatar da samar da wadataccen kayan aikin noma akai-akai, gwamnatin jihar ta zuba Naira biliyan 5 ga kamfanin...
    Wasu ’yan ta’adda da ake kyautata zaton ’yan Boko Haram ne sun kai hari a sabuwar unguwar Yamtake da ke Ƙaramar hukumar Gwoza a Jihar Borno, inda suka kashe sojoji biyu tare da wasu fararen hula da ba a bayyana adadinsu ba. Majiyoyin tsaro da na cikin gida sun tabbatar da harin, inda suka ce maharan sun mamaye unguwannin ne da misalin ƙarfe 11:15 na daren Alhamis. Gwamnatin Yobe ta sayo hatsi don tunkarar kakar bana Matan da suka tsira daga Boko Haram na buƙatar tallafin musamman Ɗaya daga cikin majiyar sojojin ta ce, kafin a aike da wata tawagar sojoji daga Gwoza, maharan sun riga sun afkawa jama’a  da sansanin sojan Yamtake. “Muna jiran tawagar masu ƙarfafa musu su...
    Ita Jihar Yobe,rashin biyan sabon mafi krancin albashi da tsohon na Naira 30,000 ga Malaman makarantun ta na Firamare da Sakandare, hakan ta kasance ne saboda rashin amincewa tsakanin Kungiyar NUT da kuma Kungiyar ma’aikatan Kananan Hukumomi ta kasa (NULGE). A ma’aikatar ilimin bai daya ta Jihar Abia, bangaren Kungiyar Malaman makaranta NUT, da reshen Kungiyar kwadago ta kasa (NLC), LEADERSHIP ta Lahadi ta gano cewa har yanzu Gwamntin Jihar bata fara biyan mafi karancin albashin ba. An samu tsaikon yin hakan ne saboda niyyar ita gwamnatin ta dauki su Malaman makaranta matsyin kwararru ta cire daga tsarin albashi na ma’aikatan gwamnati,inda za ta fara biyansu da tsarin albashi na Malaman makaranta(TSS). Kamar yadda Shugaban kungiyar kwadago na Jihar NLC,Okoro...
    Jawabin shugaban majalisar, ya biyo bayan dambarwar hankalin al’ummar kasar ne, bayan shelar ranar 18 ga watan Maris da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi na ayyana dokar ta-baci na tsawon wata shida a Jihar Ribas. Matakin ya zo ne daidai lokacin da rikicin siyasa ke kara kamari, inda aka dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara tare da rusa majalisar dokokin jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas, ya fitar da wata sanarwa mai ƙarfi game da yiwuwar dawowar wasu shugabannin siyasa cikin jam’iyyar. A lokacin ganawar da manema labarai a Kano, Abbas ya bayyana cewa APC ba za ta karɓi mutane da hukumomin yaƙi da cin hanci kamar EFCC da ICPC ke bincike ba. Wannan sanarwa ta zo ne a yayin da jita-jita da ake cewa wasu daga cikin mambobin jam’iyyar NNPP, musamman waɗanda ke cikin rukuni na Kwankwasiyya, suna duba yiwuwar komawa APC. El-rufa’i Ba Zai Halarci Taron Jam’iyyar APC Na Kasa Ba, Kuma Ganduje Na Nan A Shugabanci  NNPP Ta Mutu, Kwankwaso Zai Sake Dawowa APC – Ganduje Abbas ya bayyana cewa duk wanda ke...
    “Maimakon ya bai wa babban jami’in nasu kudin ya raba wa mutanensa, sai ya zabi rarraba musu shi da kansa”, kamar yadda wata majiya ta shaida wa wannan jarida. Sai dai, wata majiyar ta shaida wa wakilinmu a ranar Larabar da ta gabata cewa, an gayyaci ‘yansandan ne zuwa babban birnin tarayya Abuja, domin ladabtar da su. An gayyaci jami’in da sauran yaransa zuwa hedikwatar ‘yansanda da ke Abuja, domin daukar matakan ladabtarwa, in ji majiyar. Kamar yadda siginal mai dauke da kwanan wata na ranar Talata 15 ga Afrilun 2025, wadda LEADERSHIP ta samu, ya nuna cewa; ‘yansandan da shugaban tawagarsu, DSP Aliyu Adejembi, za su bayyana a hedikwatar ‘yansan da ke Abuja, domin amsa tambayoyi kan rashin da’a...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Makiya suna adawa da fadada dangantakar Iran da Saudiyya Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da ministan tsaron Saudiyya Khalid bin Salman a jiya Alhamis. A yayin ganawar, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa, alakar da ke tsakanin Iran da Saudiyya za ta kasance mai amfani ga kasashen biyu, kuma kasashen biyu za su iya taimakawa juna. Imam Khamenei ya yi nuni da cewa, akwai makiya da suke adawa da fadada alaka a tsakanin kasashenmu biyu, kuma wajibi ne a shawo kan wadannan munanan manufofin, kuma a shirye Iran take ta yi hakan. Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da ci...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Iran da Saudiyya za su iya magance yawancin matsalolin yankin Gabas ta tsakiya Shugaban kasar Iran Mas’ud Pezeshkian ya jaddada cewa: Iran da Saudiyya za su iya magance yawancin matsalolin yankin Gabas ta Tsakiya ta hanyar dogaro da karfinsu a hade ba tare da bukatar shiga tsakani daga kasashen waje ba. Shugaban kasar Iran Mas’ud Pezeshkian ya tarbi ministan tsaron kasar Saudiyya Khalid bin Salman a yammacin jiya Alhamis, wanda ke ziyarar aiki a birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran dauke da wata babbar tawagarsa. Shugaban na Iran ya jaddada cewa Iran ta kuduri aniyar karfafa alakar ‘yan uwantaka a tsakanin kasashen musulmi. Pezeshkian ta kara da cewa: Saboda wata wasiyya ta...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Za a gudanar da zagaye na biyu na tattaunawar ba na kai tsaye ba da Amurka a birnin Roma a ranar Asabar Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya sanar da cewa zai tafi birnin Roma a ranar Asabar domin halartar zagaye na biyu na shawarwari ba na kai tsaye ba da Amurka, yana mai jaddada cewa sakon da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya aikewa shugaban kasar Rasha ya kunshi muhimman batutuwa. A cewar kamfanin dillancin labaran IRNA, Araghchi ya ce: Roma ba ita ce mai masaukin baki ba, a’a, a maimakon haka, wajen da za a yi shawarwarin, gwamnatin Oman ce ta kasance mai daukar nauyin shawarwarin ba na...
    Sojojin mamayar Isra’ila sun sake aiwatar da wani sabon kisan kiyashi kan Falasdinawa 5 a sansanin Jabaliya da ke arewacin Gaza Fararen hula 5 da suka hada da yara biyu da mace daya ne suka yi shahada, wasu kuma suka bace sakamakon harin da rundunar sojin mamayar Isra’ila suka kai kan wani gida a sansanin ‘yan gudun hijira na Tal al-Za’atar da ke gabashin Jabaliya da ke arewacin Zirin Gaza. A cewar majiyoyin yankin, gidan da aka kai harin na dangin Nasiyo ne, kuma yana dauke da ‘yan gudun hijira daga iyalai sama da biyar a cikinsa, inda harin ya turbude su a karkashin baraguzan gine-gine.
    Masu wannan fahimta sun yi imanin cewa duk lokacin da mutum ya ji baya son wani abu to a wurinshi wannan abin ba mai kyau ba ne. Haka nan kuma duk lokacin da mutum ya ji cewa ga wani abu amma shi ne ya kwanta mashi, toh wannan abin shi ne mai kyau. Babban misalin da wadannan masu ra’ayi suke jaddadawa da nanatawa a kullum shi ne cewa a lokacin da mutum ya yi tsammanin cewa wani abu na da kyau a ra’ayinshi, to idan ya je cikin wata al’ummar zai tarar da cewa wannan abin barna ko wani abin ki. Misali da shan giya, caca da sauransu. Da irin wannan nazari ne aka samar da mafi shaharan nazariyyar nan...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Gombe, Bello Yahaya ya bayar da umarnin tura isassun jami’ai a fadin jihar domin samar da isasshen tsaro kafin bukin Easter, da kuma bayan bikin Easter.   Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi ya fitar a Gombe.   A cewarsa, an tura jami’an dabarun dakile hare-hare zuwa muhimman wuraren da suka hada da wuraren ibada, wuraren shakatawa, kasuwanni, da sauran wuraren taruwar jama’a.   Ya kuma ce, kungiyoyin sintiri da jami’an tsaron cikin za su kasance a kasa domin sanya ido kan ayyukan da kuma gaggauta daukar matakin magance duk wata matsala idan ta taso.   Kwamishinan ya lura cewa rundunar...
    Rundunar sojin sama na Operation Hadin Kai ta yi nasarar aiwatar da wasu hare-hare ta sama guda biyu, inda ta auka wa maboyar ‘yan ta’adda a yankin Sambisa na jihar Borno da kuma Kudancin Tumbun.   A wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na NAF, Air Commodore Ehimen Ejodame ya fitar, ya ce harin farko ya afku ne da misalin karfe 5:30 na safe a Kollaram- sanannar tungar ‘yan tada kayar baya, a ranar 15 ga watan Afrilu, inda aka kawar da mayaka da dama tare da lalata muhimman ababen more rayuwarsu.   Farmaki na biyu kuwa ya biyo bayan da misalin karfe 3:55 na rana a garin Arra na Sambisa, bayan binciken sirri da bincike...
    Akwai kuma Sanata Adeniyi Adegbonire dan jam’iyyar APC daga mazabar Ondo ta tsakiya, Sanata Seriake Dickson dan jami’yyar PDP, daga mazabar Bayelsa ta Gabas, Sanata Shehu Lawan Kaka, dan jam’iyyar APC, daga mazabar Borno ta tsakiya. Sauran sun hada da; Sanata Banigo Ipaligo dan jam’iyyar PDP, daga mazabar Ribas ta Yamma, Sanata Jarigbe Jarigbe dan jami’yyar PDP, daga Koros Riba ta Arewa, Sanata Ekong Sampson dan jami’yyar PDP, daga mazabar Akwa Ibom ta Kudu, Sanata Sani Bello dan jami’yyarAPC, daga mazabar Neja ta Arewa sai kuma Sanata Aniekan Bassey, dan jam’iyyar PDP, daga mazabar Akwa Ibom. Majalisar ta kafa wannan kwamtin ne, biyo bayan kudurin da Sanata Aniekan Bassey na mazabar Arewa da Gabas daga Akwa Ibom, ya gabatar mata...
    He Yongqian ta kara da cewa, bangaren Sin na fatan kokari tare da bangaren Turai, don kiyaye tsarin cinikayya bisa ra’ayin bangarori daban daban tare da kungiyar WTO a matsayin tushensa da bin ka’idojin cinikayya.   Game da bikin baje kolin kayayyakin shige da fice na kasar Sin karo na 137, wanda aka fi sani da Canton Fair dake gudana, He Yongqian ta ce, ya zuwa yanzu, masu sayayya fiye da dubu 110 daga kasashe da yankuna 216 sun halarci bikin, adadin ya karu da kashi 10 cikin dari bisa na karo na 135. (Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga...
    Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, Fu Cong, ya bayyana a gun taron kwamitin sulhu na MDD game da yankin manyan tabkuna na Afirka a ranar 16 ga wata cewa, sakamakon ci gaba da kai hare-hare na kungiyar M23 a baya-bayan nan, ya ta’azzara yakin gabashin Kongo DRC, kuma daukacin yankin manyan tabkuna sun fada cikin rudani. Dole ne kasashen duniya su yi aiki tare kuma su hada kai don kawar da wannan mummunar yanayin cikin gaggawa.   Fu Cong ya jaddada cewa, dole ne a gaggauta tsagaita bude wuta domin hana shi ci gaba da ruruwa. Babu wata hanyar soji da za ta magance rikicin gabashin Kongo DRC, kuma tattaunawa ta siyasa ita ce kawai mafita. Dole ne...
    Ministan Wutar Lantarki, Adedayo Adelabu ya bayyana cewa kimanin ’yan Najeriya miliyan 150 ne yanzu ke samun isasshiyar wutar lantarki, yayin da miliyan 80 ke da ƙarancin wutar lantarki. Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a yayin taron sabunta sassan ministoci na 2025 da aka gudanar a Abuja, inda ya yi magana tare da ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Malagi, da sauran masu ruwa da tsaki. ISWAP sun ruguza gadar Mandafuma a Borno ’Yan bindiga sun sace makiyaya 5, da shanu 1,200 a Kaduna Adelabu ya bayyana cewa ci gaban ya samo asali ne daga shigar Najeriya cikin shirin “Mission 300” – wani gagarumin ƙoƙarin haɗin gwiwa na Bankin Duniya da Bankin Raya Afirka (AfDB)...
    “Na gode Allah, babu wanda ya jikkata, kuma an kai rahoton lamarin ofishin ‘yansanda.” Ofishin yaɗa labaranta ya buƙaci jama’a da su kwantar da hankalinsu, inda ya ce “ƙoƙarinta na kare gaskiya da wakiltar al’ummarta bai kamata a mayar da shi barazana ko tashin hankali ba.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Sakon jagora ga shugaban kasar Rasha yana da alaka da ci gaban kasa da kasa da na yanki Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana hakan ne a yau Alhamis a birnin Moscow na kasar Rasha cewa: Abu ne da ya dace a rubuta sakon da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya aikewa shugaban kasar Rasha dangane da ci gaban kasa da kasa da na yanki da kuma batutuwan da suka shafi kasashen biyu. Araqchi ya bayyana hakan ne a lokacin da ya isa filin tashi da saukar jiragen sama na Vnukovo da ke birnin Moscow a yau, yayin da yake amsa tambayar da wakilin IRNA ya yi masa kan...
    Mutane fiye 300 ne suka mutu a cikin kwanaki a wani kazamin fada a yankin Darfur da ke yammacin kasar Sudan Hukumar kula da ayyukan jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya ta watsa rahoton cewa: Sama da fararen hula 300 ne aka kashe a wani kazamin fada na kwanaki biyu a yankin Darfur na kasar Sudan mai fama da rikici. Dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces sun kaddamar da hare-hare a ranakun Juma’a da Asabar a kan sansanonin ‘yan gudun hijira biyu da ke fama da matsalar yunwa a arewacin Darfur da kuma babban birnin da ke kusa, inda rahotannin farko suka nuna cewa sama da mutane 100 ne suka mutu, ciki har da yara 20 da ma’aikatan...
    Mazauna gundumar Kufana a Ƙaramar Hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna sun shiga cikin fargaba sakamakon jerin hare-haren ’yan bindiga da ya yi sanadiyyar sace mutane biyar da kuma kwashe shanu 1,200 cikin kwanaki hudu. Babban Jami’in Gundumar, Mista Stephen Maikori, ya tabbatar da faruwar hare-haren a ranar Laraba. A cewarsa, lamari na farko ya faru ne a daren Talata, 8 ga Afrilu, 2025, lokacin da ’yan bindiga suka kai hari kauyen Mashigi Boka-Libere, wani matsugunin Fulani, da misalin karfe 10 na dare. Maikori ya ce maharan sun kwashe garken shanu guda 12, inda kowanne garke yake da kimanin shanu 100, wanda ya kai jimillar dabbobi 1,200. Dangote: Har yanzu gidajen mai ba su rage farashin mai ba Najeriya da gwamnatin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tsohon shugaban jam’iyyar APC a Jihar Enugu, Dr. Ben Nwoye, ya ajiye muƙaminsa daga jam’iyyar. Nwoye, wanda ya sanar da haka a wani taron manema labarai ranar Alhamis, ya ce wannan shawara ta biyo bayan rushewar jagorancin jam’iyyar a jihar. Kafin yanke wannan shawara, Nwoye ya ce ya tattauna da magoya bayansa da sauran masu ruwa da tsaki, amma bai bayyana wacce sabuwar jam’iyyar da yake shirin shiga ba. Masu Gida Sun Yi Ruwan Kwallaye A Enugu Mutane Da Dama Sun Rasu Sakamakon Bindigar Tankar Mai A Enugu Nwoye ya bayyana cewa jagorancin APC a Kudu maso Gabas sun koma siyasar keta haƙƙoƙin juna, inda ya ce ba su da sha’awar ƙara wata jiha a cikin jihohin da jam’iyyar...
    Ya bayyana cewa shiga wani yanki da ba a fahimtar yaren juna ɗauke da makamai na iya janyo fargaba da tashin hankali. “Ka yi tunanin idan wasu daga Kudu sun shigo ƙauyanku ɗauke da makamai kuma ba ku fahimtar yaren juna — za ku ji tsoro. Haka nan idan mutanenmu suka shiga yankin Kudu da makamai, su ma za a ji tsoro,” in ji shi. Rurum ya ce zai gana da shugabannin ƙungiyoyin masu farauta a jihar domin daƙile wannan ɗabi’a, ya kuma buƙace su da su nemo hanyar nema wa kansu asiri . “Wasu su tafi farauta su dawo ba tare da sun kamo ko ɓeran daji ba. Bai dace su ci gaba da haka ba. Ya kamata mu...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Farfesa Bello ya ce gwamnatin jihar ta dage wajen bai wa ’yan mata masu tasowa ingantaccen ilimi da tallafa musu domin su zama masu amfani ga iyalansu da al’ummominsu.   Ya bayyana godiyarsa matuka bisa gudunmuwar da Bankin Duniya ke bayarwa, yana bayyana aikin AGILE a matsayin wani gagarumin sauyi wajen canja ra’ayin al’umma game da ilimin ’ya’ya mata.   “Kalma ba za ta isa ta bayyana yadda muke jin wannan taimako daga Bankin Duniya ba, musamman game da aikin AGILE. Kungiyar aikin a jihar, karkashin jagorancin Maryam Sani Dangaji, ta yi kokari sosai wajen fadakar da iyaye cewa AGILE yana kokarin taimaka wa yarinya ta gane cikakken kwarewarta,” in ji shi.   Farfesa Bello ya kara da cewa gwamnatin...
    Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya yi kakkausar suka dangane da yawaitar kashe-kashen da ake yi a jihar Filato da sauran sassan Arewacin Nijeriya, inda ya dora laifin kitsa tashe-tashen hankula da nufin tada zaune tsaye a Nijeriya. A wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, Fani-Kayode ya yi ikirarin cewa wadanda ke haddasa tashe-tashen hankula ba wai kawai ’yan tada kayar baya ba ne, a’a, wasu ‘yan kasashen waje ne da ake zargin suna shigowa Nijeriya ta kan iyakokin kasar, da nufin raba kan al’ummar kasar ta hanyar addini da kabilanci. Hadin Gwiwar Kasashen Asiya Da Afirka Na Habaka Karfinsu Na Dogaro Da Kai Da Cin Moriya Tare Yaukaka Zumunci Da Makwabta A Aikace...
    Ministan Harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya je kasar Rasha a safiyar yau Alhamis don isar da sakon jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminaei zuwa shugaban kasar Rasha Vladimir Putin. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa wannan sakon na zuwa ne rana guda da amincewar majalisar dojojin kasar Rasha ta dangantaka ta musamman tsakanin kasashen biyu, mai tsawon shekaru 20. Har’ila yau da kuma kwanaki biyu kafin a gudanar da tattaunawa na biyu tsakanin Iran da Amurka dangane da shirin ta na makamashin Nukliya a birnin Roma na kasar Italiya. Masana dai sun bayyana cewa kasashen Rasha da Iran suna kara dankon zumunci a tsakaninsu ne a dai-dai lokacinda al-amura da dama...
    An tabbatar da cewa, tashin hankalin ya barke ne jim kadan bayan da alkalin wasa ya busa tashi daga wasan, kawo yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance da rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta fitar har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto a safiyar ranar Alhamis, kuma kawo yanzu babu tabbacin ko an samu raunika a yayin rikicin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da wani babban kwamiti kan kidayar jama’a da gidaje mai zuwa, inda ya umurci mambobin su gabatar da rahoton farko cikin makonni uku. Shugaban wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan fadar sa, Femi Gbajabiamila, a wajen taron da aka gudanar a fadar gwamnati da ke Abuja, ya ce kidayar na da matukar muhimmanci ga ci gaban kasa da kuma tsare-tsare na gaskiya.   Ya lura cewa ingantaccen bayanan yawan jama’a yana da mahimmanci don yanke shawara mai inganci a cikin manyan sassan kamar kiwon lafiya, ilimi, tsaro, da kuma tsara tattalin arziki. Shugaban ya jaddada cewa, an gudanar da kidayar jama’a ta karshe a shekarar 2006, wato kusan shekaru ashirin da suka wuce,...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Dr. Isma’ila Baka’i ya bayyana cewa; Yanayin da mutanen garin al-fasha na Sudan suke ciki ya yi muni, tare da yin kira da a kawo karshe killace garin da aka yi da kuma bai wa fararen hula kariya.  Mayakan “Rundunar Kai Daukin Gaggawa” dake fada da sojojin Sudan ta shimfida ikonta akan sansanin ‘yan hijira na “Zamzam’ bayan kwanaki na barkewar fada a kusa da birnin al-fasha. Daruruwan mutane ne su ka rasa rayukansu yayin da wani adadi mai yawa na ‘yan hijirar  ya jikkata. Dr. Isma’ila Baka’i ya bayyana matsayar jamhuriyar musulunci ta Iran na nuna cikakken goyon bayan Sudan a matsayin dunkulalliyar kasa. A bisa kididdigar MDD a kalla mutane 300 aka kashe...
    Bakori ya ce, makaman da ake zargin an dauko su ne daga jihar Filato, ana shirin kaddamar da wani mugun nufi ne acikin Kano da kuma jihohin da ke makwabtaka da ita. Ya kara da cewa, bisa ga sahihan bayanan sirri, jami’an sun kai samame a wata maboya da ke Kuntau da Gwale, inda suka bankado yadda kungiyar ke gudanar da muggan ayyukanta.   A wani samame da jami’an ‘yansandan suka gudanar sun kama wata babbar mota makare da buhunan siminti amma kuma an boye kwalaye shida wanda ake zargin kwayar tramadol ce da kudinsu ya haura Naira miliyan 150. An kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu akan safarar kwayar da aka dauko daga Sokoto...
      A wannan rana har ila yau, Xi Jinping da Anwar sun halarci bikin musayar takardun hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu. (Mai fassara: Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    An tabbatar da mutuwar mutane bakwai a wani sabon harin da ‘yan ta’adda suka kai a kauyen Garaha Lar da ke jihar Adamawa. Shugaban karamar hukumar Hong, Honarabul Usman Wa’aganda ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa, wani mazaunin garin ya ɓata yayin da maharan suka lalata gidaje da kadarori. An Gudanar Da Harkokin Cudanya Da Musayar Al’adu Tsakanin Sin Da Malaysia A Birnin Kuala Lumpur  Jigawa Za Ta Zama Cibiyar Binciken Lafiya Nan Ba Da Jimawa Ba – Gwamna Namadi Wa’aganda ya kuma bayyana cewa, wani Ɗan banga na yankin ya mutu bayan da wani bam ya tashi a lokacin da yake ƙoƙarin tabbatar da tsaron yankin. A cewarsa, motar ‘yansandan da ke sintiri ta ofishin ‘yansanda...
    Ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Maitama Tuggar ya jogoranci wata ziyarar aiki zuwa makobciyuar kasar Jamhuriyar Nijar. Wannan it ace ziyara irinta ta farko da ministan harkokin wajen Najeriya ya kai a Jamhuriyar Nijar tun bayan da sojoji karkashin jagorancin Janar Abdourahmane Tiani suka kifar da mulkin farar hula na Mohamed Bazoum a watan Yulin shekarar 2023. Juyin mulkin da sojojin sukayi a Nijar ya haifar da takaddamar diflomasiyya sosai tsakanin Nijar da kuma kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ke jagoranta a wannan karon. Batun mayar da hambararen shugaban Nijar Bazoum da kin lamuncewa juyin mulkin daga gwamnatin Najeriya da kuma kungiyar ta ECOWAS, shi ne a sahun gaba a...
    Yan tawaye a kasar Sudan sun sanar da kafa tasu gwamnati, bayan shekara biyu ana gwabza fada a kasar. Shugaban rundinar kai daukin gaggawa ta (RSF), Mohamed Hamdan “Hemedti”, ya ce an kafa gwamnati a yankunan da kungiyarsa ke iko da su, musamman a yammacin Darfur. Dagalo ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya yi a ranar Talata, inda ya ce, “A wannan ranar tunawa, muna alfahari da ayyana kafa gwamnatin zaman lafiya da hadin kai.”  Ya kuma ce za a kafa majalisar shugaban kasa mai mambobi 15 da ke wakiltar dukkan yankunan Sudan. Janar din wanda tuni Amurka ta kakabawa takunkumi bisa zarginsa da hannu a kisan kiyashin da aka yi a yankin Darfur, ya ce wasu...
    Alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar a yau Laraba 16 ga wata cewa, mizanin hada-hadar tattalin arziki da aka fi sani da GDP na kasar Sin ya karu da kashi 5.4 bisa dari kwatankwacin makamancin lokacin bara a cikin rubu’in farko na shekarar 2025. A tsakanin wannan lokacin, alkaluman hukumar sun kuma bayyana cewa, mizanin ya nuna hada-hadar tattalin arzikin kasar ta kai yawan adadin kudin Sin yuan tiriliyan 31, da biliyan 875 da miliyan 800, kwatankwacin dala tiriliyan 4. 42.   Har ila yau, kamar yadda alkaluman mahukuntan suka nuna, karuwar darajar kayayyakin da masana’antu suka samar ta kai kaso 6.5 bisa dari duk dai a rubu’in farkon na bana. An samu wannan bunkasa ce...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kasar Sin ta kuma nuna aniyarta ta lale marhabin ga shigar da karin kayan amfanin gona masu inganci na Malaysiya zuwa katafariyar kasuwarta inda ta kuma nemi kasar ta Malaysiya ta kara bai wa kamfanoninta kwarin gwiwar zuba jari a kasar.   Kasar Malaysiya ta san irin alheran da kamfanonin Sin suke ci gaba da kawo mata wajen raya tattalin arziki da ci gaban masana’antunta. Wannan ya sa Sultan Ibrahim ya bayyana cewa, Malaysiya tana dora fifiko sosai a kan zumuncinta da kasar Sin, kuma za su ci gaba da yin aiki tare domin samun nasara ga kowane bangare, tare da kara matsa kaimi ga gina al’umma mai makoma ta bai-daya a karkashin ingantattun manyan tsare-tsare kuma a duk wani...
    Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta fitar da bayani da ya kunshi yin Allawadai da keta hurumin masallacin kudus da ‘yan sahayoniya su ka yi a cikin kwanaki uku a jere. “Yan sahayoniyar dai sun rika shiga cikin  harabar masallacin na Kudus, suna yin ibadunsu na yahudanci, tare da kariyar ‘yan sandan HKI. Kungiyar ta Hizbullah ta kuma ce; Abinda ‘yan sahayoniyar suke yi nuna kiyayya ne, da keta hurumin masallacin kudus. Bugu da kari sanarwar ta kara da cewa; Abinda ;yan sahayoniyar suke yi, ya  isa bakantawa musulmi al’ummunsu da gwmanatocinsu, ya kuma sa su yunkurawa domin hana ci gaba da abinda yake faruwa. Hizbullah ta kuma ce; Al’ummarmu ta larabawa da musulmi tana da cikakkiyar masaniya akan bukatar...
    Jaridar “Yadiot-Ahranot” ta rubuta cewa, jami’an Amurka sun sanar da sojojin Isra’ila a lokacin da za ta janye sojojinta daga kasar Syria. Jaridar ta ce, jami’an tsaron kasar ta Amurka sun fada wa sojojin Isra’ila cewa, janye sojojin nata zai fara ne nan da watanni biyu masu zuwa. Rahoton jaridar ta ‘yan sahayoniya ya ce, Shirin janyewar sojojin na Amurka bai zama abin mamaki ba,domin tun farkon rantsar da Donald Trump ne ya bayyana aniyarsa na janye sojojin kasar daga Syria. HKI tana jin cewa, idan har Amurkan ta janye daga kasar Syria, to Turkiya za ta kara azamarta ta shimfida ikonta a cikin kasar. Tun a Zangon shugabancinsa na farko ne dai Donald Trump ya bayyana cewa Idan kungiyar...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jam’iyyar Hamayyar siyasa ta “Chadema” a kasar Tanzania ta ki amincewa da matakin gwamnatin kasar na haramta mata shiga manyan zabukan da za a yi a watan Oktoba. Hukumar zaben kasar ta Tanzania ta zargi jam’iyyar Chameda’ da cewa ta ki amincewa ta rattaba hannu akan dokokin zabe, tana mai yin kira gare ta da ta girmama hukumar zaben kasar. A ranar Asabar din da ta gabata ne dai babbar jam’iyyar adawa ta kasar Tanzania ta kauracewa halartar taron da aka yi wanda ya kunshi dukkanin jam’iyyun siyasa da su ka rattaba hannu akan dokokin zabe. Rattaba hannu akan dokokin dai yana a matsayin daya daga cikin sharuddan shiga cikin zabe da jam’iyyu za su yi,kamar yadda Ramadhani Kalima, daraktan...
    Haka kuma a ƙaramar hukumar Ringim ta Jihar Jigawa, ya amsa cewa ya kashe wani mutum sannan ya sayar da babur ɗinsa wanda ya sace a kan kuɗi Naira 300,000. Rundunar ‘yansanda ta ce yanzu haka suna ci gaba da bincike a kansa a Sashen Binciken Manyan Laifuka (CID), don tabbatar da gaskiyar iƙirarin da ya yi da kuma gano ko akwai wasu da suke tare da shi. Kwamishinan ‘yansandan Jihar Kano, CP Ibrahim Bakori, ya yaba da matakin da Umar ya ɗauka na miƙa kansa, tare da kira ga sauran masu laifi da su kwaikwayi irin wannan mataki. Ya kuma tabbatar da cewa rundunar ‘yansandan za ta ci gaba da ƙoƙari wajen kawar da masu aikata laifi a faɗin...
    Ya ce suna ci gaba da bincike a cikin dazuka da ke kusa da garin. Ɗan majalisar dokokin Jihar Benuwe mai wakiltar mazaɓar Otukpo-Akpa, Kennedy Angbo, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce harin ya faru da misalin ƙarfe 5:30 na yamma kuma jama’a da dama sun tsere daga garin saboda tsoro. Wani mazaunin Otobi, Edwin Emma, ya ce wannan ne karo na biyu da ake kai musu hari cikin wata guda. “Matata da ’ya’yana sun tsere a kafa yanzu haka. Muna buƙatar taimako,” in ji shi. Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yansandan Jihar Benuwe, Catherine Anene, bai yi nasara ba domin wayarta a kashe ta ke. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
    Reshen soja na kungiyar Hamas wato rundunar Izzuddin Qassam, ya gargadi iyalan fursinonin yahudawan Sahyoniyya wadanda take tsare da su a Gaza kan cewa yayansu zasu koma hannunsu gawaki, saboda irin yadda HKI take kara yawaita Jefa boma-boman a kan Falasdinawa a Gaza. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto  wani mai magana da yawan dakarun yana fadar haka a wani fai-fai bidiyo da rundunar ta watsa a yanar gizo a jiya talata. Dakarun suna kira ga iyalan yahudawan da su yi shirin karban gawakin yayansu a cikin akwatunan gawaki, wannan kuma saboda yadda jiragen yakin HKI suke kai hare-hare babu kakkautawa kan gaza ba tare da bambanta tsakanin  yara da mata da sauransu ba. Sakon Bidiyon yana...
    A wani taron manema Labarai a nan birninTehran, kakakin sojojin kasa na dakarun IRGC a nan JMI,  Burgediya Janar Ali Muhammad Naeini ya fadawa yan jaridu cewa, tsaron JMI da kuma makamanta baa bin tattaunawa ne da makiya ba. Ya kuma kara da cewa, tsaron kasar Iran jan layi ne,  haka ma, karfin sojojin kasar. Janar Naeini ya ka ra da cewa, rawar dajin da sojojin IRGC suka yi a baya-bayan nan ya na tabbatar da hakan. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, Burgediya Janar Naeini yana maida martani ne ga gwamnatin Amurka wace ta fara maganar cewa, zata tattauna da kasar ta Iran ne a kan shirinta na makamai masu linzami, da kuma shirin ta...
    Jami’an diblomasiyya daga kasashen duniya da dama, da kuma wakilan kungiyoyin agaji daban-daban sun hadu a birnin London na kasar Burtania don tattauna batun yakin da ke faruwa a kasar Sudan wanda a halin yanzu yake cika shekaru 2 ke nan. Shafin yanar gizo na labarai ‘Afrika New” ya bayyana cewa, taron na kwana guda ya tattara wakilai daga kasashen Faransa,  Burtaniya,  Jamus da kuma kungiyar tarayyar Turai, har’ila yau da kasashen da suke makobtaka da kasar ta Sudan. Labarin ya kara da cewa, yakin na Sudan wanda yake cika shekaru biyu, ya zuwa yanzu ya lakume rayukan mutane akalla 20,000, sannan ya yi sanadiyar kauracewar mutane kimani miliyon 14 zuwa cikin kasar da kuma kasashe makobta, sannan wasu da...
    Zulum ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki da su maida hankali wajen samar da damammaki ga matasa a arewacin Nijeriya.   A nasa jawabin, Shugaban Majalisar Sarakunan Arewa kuma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya bayyana cewa, taron da aka yi a Jihar Borno an yi shi ne domin karfafa hadin kan jihohin Arewa da kuma tattaunawa kan halin da yankin ke ciki domin tallafa wa shugabannin siyasa wajen magance matsalolin da ke addabar Arewa.   Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA) da babban hafsan tsaro (CDS) da babban sufeton ‘yansanda (IGP) duk sun samu wakilci a taron sarakunan.   Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da shugaban kungiyar gwamnonin jihohin Arewa...
    A cewar Ministan, samun wannan ƙwarewar ya zama wajibi a wannan zamani da kowa da kowa – wato daga masana hulɗa da jama’a zuwa shugabannin kamfanoni – yake taka rawa a matsayin mai magana da yawun wani.   Idris ya ce: “Yau a wannan zamani da kowa ke zama mai magana da yawu – ko ɗan hulɗa da jama’a ne ko shugaban kamfani a ɓangaren gwamnati da masu zaman kan su – wajabcin samun ilimi kan kafofin watsa labarai ya zama abu mai matuƙar muhimmanci, domin yana ba da damar fahimta, nazari da tantance sahihancin saƙonnin da ke yawo a kafafen watsa labarai, wanda hakan zai ba da damar yanke sahihin hukunci da mu’amala da labarai yadda ya kamata.  ...
    Ya kuma jaddada cewa, “An yi duk wani shiri don kauce wa hakan, amma duk da haka mun gaza, a madadin gwamnati da hukumomin tsaro ku yafe mana”.   Gwamnan ya yi Allah-wadai da ci gaba da hare-haren da suka addabi yankin Irigwe, ya kuma yi alkawarin sabunta alkawarin kawo karshen tashe-tashen hankula a jihar.   Mutfwang ya bukaci al’umma da su dawo da tsare-tsaren tsaro na iyaye da kakanni, ya kuma yi kira ga matasa da su sa ido sosai, musamman a lokacin damuna mai zuwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Ba su kallon tattaunawa tsakanin Iran da Amurka na kasar Oman da kyakkyawan fata ko ganin rashin amfaninsa kwata-kwata Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya karbi bakwancin wakilan gwamnati da dama, da wakilan majalisar shawarar Musulunci, da manyan jami’an shari’a, da jami’ai daga cibiyoyi daban-daban a yau Talata, a daidai lokacin da ake bukukuwan shiga sabuwar shekara ta hijira Shamsiyya. A yayin wannan taron, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Tattaunawar kasar Oman na daya daga cikin ayyuka da dama da ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta aiwatar, bai kamata mu alakanta matsalolin kasar da wadannan shawarwari ba. Ya kara da cewa: Ba su kallon wadannan...
    Lauyoyin Landan suna tattara bayanai kan ‘yan Birtaniya da suka yi aiki a cikin rundunar sojojin mamayar Isra’ila Kwararru kan harkokin shari’a na kasar Biritaniya sun ce gurfanar da wasu ‘yan kasar masu takardar ‘yan kasa biyu da ke aiki a cikin sojojin mamayar Isra’ila a gaban kuliya bisa zargin hannu a tafka laifukan yaki a Gaza, zai yi tasiri ga wadanda ke tunanin shiga cikin sahunsu. Hakan ya biyo bayan gabatar da rahoto ga rundunar ‘yan sandan birnin Landan ne mai kunshe da shaidun da suka shafi ‘yan Birtaniya guda 10 da suka yi aikin soja karkashin rundunar mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila da ake zargi da aikata laifukan yaki a Gaza. A cewar wani rahoto da kamfanin dillancin labarai...
    A kwanakin nan da suka gabata kuma, an kaddamar da bikin baje kolin kayayyakin masarufi na kasa da kasa karo na 5, da bikin baje kolin kayayyakin shige da fice wato Canton Fair karo na 137 a nan kasar Sin, inda yawan kamfanonin da suka halarce su suka kai matsayin koli a tarihi. Shugabar kwalejin nazarin tattalin arzikin Sin bisa salon kirkire-kirkire ta kasar Brazil madam Claudia Jannuzzi, ta ce Sin na matukar bude kofarta ga sauran sassa, tare da ba da tabbaci ga bunkasar tattalin arzikin duniya.   Cinikin shige da ficen Sin na samun bunkasuwa mai dorewa a gabanin duk wani kalubale. Ba shakka duniya za ta ga hakikanin halin da ake ciki, wato babu mafita a aiwatar da...
    A sakamakon haka, an gurfanar da wanda ake tuhuma a gaban kuliya bisa tuhumarsa kan wannan laifin wanda kuma ya amsa laifin lokacin da aka karanta masa tuhumar.   A hukuncin da ya yanke, Alkalin Kotun, Mai shari’a Nasir Ahmad ya yanke hukuncin ɗaurin shekaru biyu a gidan yari, da tarar Naira 20,000, da karin ɗaurin watanni shida a gidan yari, da kuma bulala arba’in.   Kotun ta ce, an yanke wannan hukuncin ne don ya zama izini ga masu shirin aikata irin wannan laifin a nan gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake...
    A nasa bangare kuwa, To Lam cewa ya yi Vietnam a shirye take ta yi aiki tukuru don kyautata tsare-tsare da hadin gwiwa da bangaren Sin ta yadda za a daga martabar cudanyar sassa daban daban, da nacewa ka’idoji 5 na zaman jituwa, da kare dokokin gudanar da cinikayya na kasa da kasa, da martaba yarjejeniyoyin da aka cimma tsakanin sassan biyu, da hada hannu wajen ba da gudummawa ga wanzuwar zaman lafiya da ci gaban daukacin bil’adama. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
    A yammacin yau ranar 15 ga watan Afrilu ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa birnin Kuala Lumpur ta jirgin sama na musamman, domin gudanar da ziyarar aiki a kasar Malaysia.   Xi Jinping ya gabatar da rubutacciyar jawabi a filin tashi da saukar jiragen sama, inda ya ce, yana fatan daukar wannan ziyara a matsayin wata dama ta kara zurfafa dadadden zumuncin dake tsakanin kasashen biyu, da kara amincewa da juna a fannin siyasa a tsakanin bangarorin biyu, da sa kaimi ga yin hadin gwiwa a fannin ayyukan zamanantarwa, da sa kaimi ga yin mu’amala da fahimtar juna a tsakanin al’ummomi, da inganta gina al’umma mai kyakkaywar makomar bai daya tsakanin Sin da Malaysia zuwa wani sabon...
    ’Yan Najeriya da suka rabauta da sayen shinkafar kasar waje da Gwamnatin Tarayya ta karya farashinsa sun koka bisa rashin ingancin wata wadda ake sayarwa a Jihar Kogi. Wadanda suka sayi rukunin farko na shinkafar sun yaba da ingancinta da dandanonta, wasu kuma na korafi a kan yanayi da kuma dandanon wadda suka samu daga wani kamfani daga wata kasar Asiya. Wasu suka samu shinkafar mai matsala sun yi ikirarin samun kwari a cikinta kuma tana yin kumfa idan ana dafa ta, sa’annan idan ta nuna tana yin danko sosai, sabanin yadda aka san shinkafar kasar waje. Wani dan kasuwar shinkafar cikin gida a Najeriya ya yi zargin rukunin shinkafar da ta samu matsalar ta jima a ajiye ne kafin...
    Ya ce sama da mutane 150 ne aka kama da laifin faɗan ɗaba da tashin hankali, tare da ƙwato makamai, miyagun ƙwayoyi da kayan sata. Ya ƙara da cewa matsalolin faɗan ɗaba da shaye-shaye barazana ce ga zaman lafiyar jama’a da makomar matasa. Duk da yake kame na da muhimmanci, Bakori ya ce dole ne a bai wa matasa damar samun ilimi, koyon sana’o’i da kuma wasu ayyuka da za su riƙa shagaltar da su zuwa hanya mafi dacewa. Ya kuma shawarci shugabannin ‘yansanda na ƙananan hukumomi da su riƙa haɗa kai da sarakunan gargajiya da al’ummar yankinsu wajen gano matsalolin tsaro a yankunansu. “Idan muka haɗa kai da goyon bayan jama’a, babu yadda ‘yan daba za su ci gaba...
    Ya ce sama da mutane 150 ne aka kama da laifin faɗan ɗaba da tashin hankali, tare da ƙwato makamai, miyagun ƙwayoyi da kayan sata. Ya ƙara da cewa matsalolin faɗan ɗaba da shaye-shaye barazana ce ga zaman lafiyar jama’a da makomar matasa. Duk da yake kame na da muhimmanci, Bakori ya ce dole ne a bai wa matasa damar samun ilimi, koyon sana’o’i da kuma wasu ayyuka da za su riƙa shagaltar da su zuwa hanya mafi dacewa. Ya kuma shawarci shugabannin ‘yansanda na ƙananan hukumomi da su riƙa haɗa kai da sarakunan gargajiya da al’ummar yankinsu wajen gano matsalolin tsaro a yankunansu. “Idan muka haɗa kai da goyon bayan jama’a, babu yadda ‘yan daba za su ci gaba...
    Majiyar Falasdinawa a Gaza sun bada labarin kissan wasu sojojin HKI  a unguwar Shuja’iyya kusa da Gaza a jiya Litini,  inda wasu kuma suka ji rauni. Kafafen yada labarai da yahudawan da kuma larabawa sun bayyana cewa kungiyar Jihadul Islami a Gaza ta ce nayakanta masu farautar yahudawa daga nesa sun bayyana cewa suk halaka wasu yahudawa wadanda suka boye a wani gida a garin Rafah kudancin Gaza, inda suke halakasu. Sannan a sauran wuraren kuma sojojin yahudawan da dama ne  suka ji rauni. Kuma sun ga jiragen yakin masu sauran ungulu na yahudawan sun zo sun tafi da wadanda abin ya shafa. Wannan dai kadan Kenan daga hare-haren maida martanin da dakarun falasdinawan suke mayarwa ga sojojin yahudawan, tun...
    A zantawarsa ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Kuwait, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya ce tattaunawarsa da Abdullah Ali Al-Yahya ya fi bada karfi kan al-amuran yankin Asiya ta kudu musamman tattaunawa tsakanin Iran da Amurka kan shirinta na makamshin nukliya da kuma dagewa kasar takunkuman tattalin arzikin da aka dora mata. A cikin tattaunawar dai ministan harkokin wajen kasar Kuwai y ace, kasashen yankin da dama sun ji dadin ganin cewa Iran da Amurka suna tattaunawa a tsakaninsu, kuma fatansu shi ne ya zama daga karshe kasashen biyu sun cimma dai-dato don warware matsalolin da ke tsakaninsu ta hanyar tattaunawa. Aragchi ya bayyana cewa a halin yanzu ba zamu iya fadar menen sakamakon tattaunawar ba,...
    Ministan harkokin noma na JMI Ghulan Reza Noori Ghezelji ya jagoranci wata tawagar jami’an gwamnatin kasar zuwa kasar Brazil don halattan taron ministocin noma na kungiyar BRICS da kuma tattauna al-amura masu muhimmanci wadanda suka shafi ayyukan noma a duniya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa gwamnatin JMI ta fara aiki a matsayin mamba a kungiyar raya tattalin arziki na kasashen BRICS, wacce ta zama cikekken maba a farkon wannan shekara. Ta fara aiki tare da sauran kasashen kungiyar wadanda suka kafa ta, wato Brazil, Rasha, India, China,da kuma Afirka ta kudu.. Halattar wannan taron ba kawai zai kara karfin JMI a cikin kungiyar BRICS ba, sai dai zai kara inganta matsayin kasar a fagen noma...
    Bayan da hukumar zaben kasar Gabon ta tabbatar da nasarar da Brice Oligui yayi a zaben shugaban kasa na karshen makon da ya gabata, shugaban ya gabatar da jawabinsa na farko ga mutanen kasar, inda ya bayyana masu kan cewa, babu jin dadi sai tare da wahala. Shafin tanar gizo na labarai ‘Africa News” ya nakalto shugaban yana cewa muhimman al-amuran da zai sa a gaban a shugabancin kasar sun hada da sauya tsarin tattalin arzikin kasar daga dogaro da man fetur zuwa harkokin kasuwanci,  har’ila yau zai yaki cin hanci da rashawa. Brice ya ce, ya zo ne a matsayin mai gina kasa, kuma yana son taimakon su don samun nasara a wannan gagarum,in aikin. A ranar lahadin da...
    A kalla tsoffin sojojin rundunar “Gulani” ta HKI 150 ne su ka rattaba hannu akan takardar yin kira da a dawo da fursunoni gida daga Gaza. Ita dai rundunar “Gulani” ce mafi karf a tsakanin rudunonin sojan HKI,kuma tun da aka kafa ta, ta shiga dukkanin yake-yaken da HKI ta yi. Wadanda su ka rattaba hannu akan wasikar sun bayyana goyon bayansu ga wasikar da sojan sama su ka rubuta a ranar 9 ga watan Aprilu da ake ciki,ko da kuwa sakamakon hakan shi ne kawo karshen yaki. A cikin sa’o’i 48 da su ka gabata,dubban sojojin HKI sun rattaba hannu akan wasika wacce take yin kira da a kawo karshen yakin Gaza da kuma dawo da fursunonin da suke...
    A jiya Litinin daruruwan yahudawa ‘yan share wuri zauna sun kutsa cikin masallacin kudus, suna masu bayar da take na tsokana ga Musulmi. Har ila yau ‘yan share wuri zauna din sun kuma gudanar da na’u’oin ibadu na addinin yahudanci a cikin farfajiyar masallacin na Kudus. Ma’aikatar  da take kula da wuraren ‘wakafi’ na musulunci, ta bayyana cewa; Adadin yahudawa ‘yan share wuri zauna din da su ka kutsa cikin masallacin na Kudus sun kai 765,kuma ‘yan sanda sun rika yi musu rakiya. A lokaci daya kuma jami’an tsaron na ‘yan sahayoniya sun tsaurara matakan kuntatawa Falasdinawa masu shiga cikin masallacin na Kudus domin yin salla. Wannan tsokanar ta ‘yan share wuri zauna a masallacin Kudus, tana faruwa ne a...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A yanzu haka, al’ummar Filato na cikin fargaba da tashin hankali sakamakon jerin hare-haren da suka afku a wasu sassan jihar, inda daruruwan mutane suka rasa rayukansu, wasu kuma suka tsere daga muhallansu. Ko mene ne dalilin sake dawowar rikice-rikicen da suka dabaibaye yankin da ake ganin an fara samun zaman lafiya? NAJERIYA A YAU: Dalilan Farfaɗowar Boko Haram A Jihar Borno DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ‘Matar Bahaushe Ba Ta Iya Kiran Sunan Mijinta’ Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan rikice rikicen Jihar Filato da dalilan aukuwarsu. Domin sauke shirin, latsa nan: https://www.buzzsprout.com/1822045/episodes/16978635-dalilan-rikice-rikice-a-jihar-filato.mp3?download=true
    “Abin takaici ne cewa, a maimakon yin amfani da gagarumin goyon baya da yunƙurin da ƴan ƙasa ke ginawa, Onanuga ya zaɓi fitar da wata sanarwa mai takurawa. Fahimtar da ya yi wa dokar zabe yana da tsauri fiye da kima kuma ya kasa gane bambanci tsakanin yakin neman zabe ba bisa ka’ida ba da kuma furuci na siyasa na gaske na ‘yan kasa.   “Ƙungiyar gamayyar matasan Arewa ta yi watsi da wannan mataki. Goyon baya ga Shugaba Tinubu na halitta ne kuma a duk faɗin ƙasar, Ginin siyasa ba laifi ba ne.   “Don haka, muna kira da a gaggauta maye gurbin Bayo Onanuga, mai bayar da shawara kan harkokin siyasa da kuma mai bayar da shawara ga...
    Wasu kafofin yada labarai a duniya na ganin cewa, idan gwamnatin Amurka ta ci gaba da saka shingayen haraji, to sauran kasashe za su maye gurbinta a bangaren samar da hidimomi. Abin da gwamnatin ta yi biris da shi yayin da take kididdigar harajin da za ta kakabawa sauran sassa, har yanzu wannan bangare na shiga gogayyar ciniki.   Bisa bayyanan da aka fitar, Amurka ta dade tana cin rarar kudin ciniki a bangaren ba da hidimomi. Alal misali a shekarar 2024, yawan rarar kudin da ta samu a wannan bangare ya kai dala biliyan 300. Kuma Abin lura shi ne, cinikin hidimomi na matukar dogaro da cinikin kayayyaki. Gibin kudin cinikin da Amurka ta samu a bangaren cinikin kayayyaki...
    Wani ƙazamin rikici da ya janyo salwantar rayukan fiye da mutum 50 a Jihar Filato ya tayar da ƙura a faɗin Nijeriya. Aƙalla mutane 51 ne aka kashe a wasu hare-hare biyu da aka kai a yammacin Lahadi a Jihar Filato da ke Arewa maso tsakiyar Nijeriya. Mahukunta a Filato sun ce an kai harin ne a cikin daren Litinin a garin Zike da ke yankin Kwall a Ƙaramar Hukumar ta Bassa. Mai bai gwamnan jihar shawara kan harkokin tsaro, Admiral Shipi Gakji mai ritaya, ya tabbatar wa BBC cewa an kai harin ne a cikin dare, wayewar garin Litinin kuma adadin waɗanda aka kashe “ya zarce 40.” Sai dai Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar ta Filato ta...
    Shugaba Bola Tinubu ya bayyana bakin cikinsa kan harin da aka kai  Jihar Filato wanda ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 40. A cikin wata sanarwa, Shugaban kasa ya la’anci wannan tashin hankali tare da mika ta’aziyyarsa ga Gwamna Caleb Mutfwang, Gwamnatin Jihar, da al’ummar Filato. Sanarwar da Mai ba Shugaban Kasa shawara na musamman kan Harkokin Yada Labarai Mista Bayo Onanuga, ya sanya wa hannu, ta bukaci Gwamnan da ya nuna cikakken ikonsa wajen warware rikicin da tabbatar da zaman lafiya mai dorewa. Shugaba Tinubu ya jaddada muhimmancin soyayya da hadin kai a maimakon  bambancin addini da kabila. Ya bukaci shugabannin al’umma, da na addinai, da ma na siyasa a ciki da wajen jihar, da su hada kai...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rundunar ‘Yansandan Jihar Adamawa ta kama Umar Shaibu bisa zargin cin zarafin wata mata a yankin Jimeta a jihar. An kama Shaibu ne bayan wani bidiyo mai tayar da hankali ya yadu a kafafen sada zumunta, kamar yadda Jami’in hulda da Jama’a na ‘Yansandan Jihar Adamawa, SP Suleiman Nguroje, ya bayyana. Salamatu Yakubu, matar mai shekaru 22 daga Angwan Tana, an ce wanda ake zargin ya yi ma ta dukan jakin ne mai tsanani, Shaibu, wanda ake cewa shi ne dan uwanta. Wannan lamarin ya janyo zarge-zargen daga al’umma da kuma kiran da aka yi wa Yansanda daga mutanen gari, da kungiyoyin fararen hula, da sauran masu rajin kare hakkin bil’adama domin a kama wanda ake zargi. Ƴansanda Sun...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin jihar Jigawa ta bada kwangilar sanya kwalta akan hanyar Dolen kwana zuwa Garin Gabas zuwa Hadejia, kan naira miliyan dubu bakwai da miliyan dari takwas. Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan a wajen bikin kaddamar da aikin sanya kwaltar. Ya ce aikin hanyar mai tsawon kilomita 29, ana sa ran kammalawa nan da watanni 12 masu zuwa. Malam Umar Namadi ya kara da cewar, an bada aikin sanya kwaltar ne da kuma sauran ayyukan inganta hanyoyi domin saukakawa manoma da sauran al’umma harkokin sufuri. A don haka, ya yi kira ga al’ummar jihar da su rinka sa ido akan kayayyakin da hukuma ta samar musu domin gudun lalacewa da kuma barnatarwa. A jawabinsa na maraba,...
    Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana alhininsa akan rasuwar Dr. Akbar I’itimadi wanda shi ne na farko da ya kafa hukumar makamashin Nukiliya ta Iran. Wasikar ta’aziyyar da shugaban kasa ta kunsa ta ambaci cewa:  Shakka babu hidima mai kima da wannan masanin ya yi, ya share fagen gina da ci gaban fasahar makamashin Nukiliya a Iran da kuma mayar da kasar mai cin gashin kanta a wannan fage. Har ila yau, shugaban kasar ta Iran ya mika sakon ta’aziyyarsa ga masana na Iran, da kuma iyalansa. Ya kuma yi addu’a da rokon Allah madaukin sarki da ya lullube shi da rahamarsa da kuma gafararsa, sannan ya bai wa iyalansa na hakuri.