2025-06-16@08:51:44 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2298

«Allah Ya ba shi»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    A gaskiya wannan matsalar takan faru ne a tsakanin ma’auratan da basa son juna sosai, hadin gida (auren dangi), ko babbar matsala na karya alkawari tsakaninsu, abu ne kuma wanda bai kamata ana yi wa yara hukuncin da ba laifinsu, wannan a bayyane cin zali ne da shirin maida yaro kangarerre. Ba shi da wani amfani sai illah, dan ya kan maida yaro ya zamo baya tausayin iyayenshi, kullum yana cikin jimamin rayuwarsa a duk sanda iyayensa suka samu sabani to, a kanshi ko a kansu za a huce haushi. Babbar matsala ma, dan zai sanya kokwanto a zuciyar yaransu na cewa iyayen nasu anya suna sonsu kuwa? Ko su kadai Allah ya bawa irin wadannan iyayen?, za su kasance...
    Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya nada sabon Galadima na Kano, Alhaji Munir Sanusi Bayero, tare da wasu manyan ‘yan Majalisar Sarki Masarautar su hudu.       Sabbin masu rike da mukaman gargajiya da aka yi wa rawani sun hada da Wamban Kano, Alhaji Kabir Tijjani Hashim, Turakin Kano, Alhaji Mahmud Ado Bayero, Tafidan Kano, Adam Lamido Sanusi, da Yariman Kano, Alhaji Ahmad Abbas Sanusi.     Da yake jawabi bayan bikin nadin, Sarki Sanusi ya shawarci sabbin sarakunan da aka nada da su kasance masu koyi da shugabanni, inda ya ce sun riga sun nuna biyayya, tawali’u da tausayin talaka.       Ya bayyana irin gudunmawar da suke bayarwa ga al’umma, ya kuma bukace su...
    Rundunar sojojin Najeriya ta 1 karkashin jagorancin Birgediya Janar Timothy Opurum ta samu gagarumar nasara a yakin da take yi da ta’addanci da ‘yan bindiga a jihar Zamfara, musamman a kananan hukumomin Talata Mafara da Kaura Namoda.   A wata sanarwa da mukaddashin mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar soji, Kyaftin Sulaiman Omale ya fitar tace a farkon farkon watan Mayun 2025, dakarun su da ke sintiri na yaki sun ci karo da dimbin ‘yan ta’adda da suka kutsa kai kauyen Mai Kwanugga a karamar hukumar Talata Mafara.   Ya yi bayanin cewa, ‘yan ta’addan sun rika kai hari kan mutanen yankin tare da kona gidaje kafin isowar sojojin, inda ya ce, bayan tuntubar rundunar, sojojin sun yi nasarar...
    Kyari ya mayar da martani ne a shafinsa na X a daren ranar Asabar 3 ga watan Mayun 2025.   Wata jarida ta yanar gizo ce ta yi ikirarin cewa, Mele Kyari yana tsare a hannun EFCC domin amsa tambayoyi game da zarge-zargen almundahana. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
      Karin Bayanai Za ki samu kankana ki markada a blender ki saka garin ridi a ciki da madara da zuma ku sha ku biyu.   Maganin sanyi Hulba na mutukar kashe kwayoyin cuta da hana zubar ruwa, shan sa a ruwan zafi da zuma, ko diban garin a hadiye da ruwa ko yoghurt yana mutukar kashe kwayoyin cuta. Haka a jika da ruwa na minti ko a dafa a riga tsarki ko zama da shi sau biyu a rana yana kashe cututtukan sanyi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko...
    Dakta Abdulmalik ya ce, a halin yanzu gwamnatin jihar na da likitoci 99 kadai ne, wadanda ke kan tsarin albashi, ya kara da cewa; adadin da ake bukata kuma sun kai kimanin 180 zuwa 200.   “Likitoci ukun da suka bar aiki, sun dawo bayan karin albashin likitocin da gwamnan ya yi a baya-bayan nan. Don haka, a da muna da likitoci 96, amma bayan karin albashin da gwamnan ya yi, uku da suka bar aikin sun dawo. Saboda haka, a halin yanzu muna da likitoci 99. Kazalika, muna da bukatar kari, domin kuwa kimanin likitoci 180 zuwa 200 muke bukata.”   Saboda haka, hukumar ta ce; tana kokarin samar da wata manhaja da za ta bai wa marasa lafiya,...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya yaba da sadaukarwar da ‘yan jarida suka bayar da suke ba da labaran irin wahalhalun da Falasdinawa ke ciki A wani sako da ya wallafa a shafinsa na twitter na ranar ‘yancin ‘yan jarida ta duniya, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana jin dadinsa ga irin sadaukarwar da ‘yan jarida suka yi, wadanda suka rubuta irin wahalhalun da al’ummar Falastinu suke yi da kuma laifukan da yahudawan sahayoniyya suka yi a tsawon shekaru biyu da suka yi a zirin Gaza. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya rubuta a shafin sada zumunta na “X” a jiya Asabar cewa: Ranar ‘yancin ‘yan jarida ta duniya ta tuna da jarumtakar ‘yan...
    Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon ta yi Allah wadai da harin wuce gona da irin da ‘yan sahayoniyya suke yi kan kasar Siriya Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon ta yi Allah-wadai da harin bam da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai a Siriya a ranar Asabar. A cikin wata sanarwa da kungiyar ta Hizbullahi ta fitar ta ce: Tana jaddada tofin Allah tsine da yin Allah wadai da zaluncin yahudawan sahayoniyya da suka addabi kasar Siriya a wani mummunan hari da suka kai kan yankunan kasar, tare da fakewa da munanan kalamai da take-take na aiwatar da ayyukanta na fadadawa da wargaza kasar Siriya da nufin rusa hadin kan kasar da kuma haifar da...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bukaci matasan kasarsa da su zage damtse, wajen bayar da gudummawar cimma nasarar zamanantar da kasa, ta hanyar yin dukkanin sadaukarwa da kasar ke bukata daga gare su.   Shugaba Xi, ya yi wannan tsokaci ne cikin martanin wasikar da ya aike ga rukunin malamai masu aikin sa kai, a wata makaranta dake yankin kan iyakan kasar mai nisa, karkashin jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kai dake arewa maso yammacin kasar Sin. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe ...
    A yanzu kuma, Amurka na son kawar da dimbin gibin kudaden asusunta, ta hanyar amfani da kare-karen haraji. A baya Amurka ta yi kokarin hakan ba tare da cimma nasara ba, kuma a yanzu ma hakan ne zai sake faruwa. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ana ci gaba da yin kiraye-kiraye ga HKI da ta kawo karshen hare-haren da take kai wa kasar Syria,jim kadan bayan da sojojin HKI su ka sanar da cewa; a karon farko jirgin sama maras matuki na ‘yan sahayoniya ya sauka a Suwaidah.  A daren jiya Juma’a ne dai HKI ta kwana tana luguden wuta akan yankuna mabanbanta na kasar ta Syria da su ka hada da birnin Damascuss har da daura fa fadar shugaban kasa.  HKI tana kai wannan hare-haren ne dai da sunan bayar da kariya ga ‘yan Duruz domin hana sojojin Syria ci gaba da kai musu hare-hare. Jami’in diplomasiyyar MDD mai kula da kasar Syria Geir Otto Pedersen ya rubuta a shafinsa na X sakon yin...
    A daya bangaren kuma, sashen sufurin jiragen kasa na Sin, ya gudanar da zirga-zirga kusan miliyan 23.12, adadin da ya karu da kaso 11.7 bisa dari, kamar dai yadda alkaluman kamfanin sufurin jiragen kasa na Sin suka nuna.   Har ila yau, idan an kwatanta da tafiye-tafiye masu cin gajeren zango da Sinawa suka fi gudanarwa cikin kwanaki 3 na bikin sharar kaburbura na Qingming, an gudanar da zirga-zirga zuwa wurare masu nisa, tare da lekawa wuraren dake kusa da kan iyakokin kasar a ranakun hutun murnar ranar ‘yan kwadago ta duniya a bana.   Wasu alkaluma na daban, daga shafin hidimar tafiye-tafiye na Qunar.com, sun nuna cewa, a ranar Alhamis, adadin wuraren da masu yawon bude ido suka ziyarta...
    Ta ce: “Zargin da aka yi na cewa na shirya ficewar matan daga bikin Uwargidan Gwamna a ranar 2 ga Mayu 2025, karya ce kawai. Ba ni da hannu a cikin wannan lamirin kuma wannan ƙarya ce ta masu tada hankali.   “Na kasance na mai da hankali ne kan karatuna na digiri na uku a lokacin da aka dakatar da ni, ba tare da shiga cikin wani yunkuri ba. Ina kira ga duk masu ruwa da tsaki su taimaka wajen inganta zaman lafiya a jihar.”   Ta kara da cewa ta kasance tana aiki don ci gaban jihar kuma ta bukaci mutane su guji yada jita-jita maras tushe. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...
    Saleh ya ce, kaddamar da injin kyankyasar, musamman saboda jajircewar ma’aikatan sashen kan wannan aiki, tuni Jami’ar ta fara ganin sakamako mai kyau.   Ya kara da cewa, samar da wannan inji, ya kara nuna irin mayar da hankali da Jami’ar ta yi, wajen habaka fannin aikin noma ta hanyar amfani da kimiyyar zamani da kuma samar wa daliban fannin kimiyyar Jami’ar kayan aikin zamani da za su rika gudanar da ilimin yin gwaje-gwaje da kuma bayar da gudunmawa wajen kara samar da wadataccen abinci a kasar.   Kazalika, wannan nasara ta kuma nuna a zahiri irin kyakkyawan shugabancin Shugabar Jami’ar, Farfesa Maimuna Waziri, duba da irin kokarinta na dora Jami’ar a kan turba mai dorewa, musamman a bangaren samar...
    Wasu daga cikin manoman a wadanan yankuna sun bayyana cewa, sun koma neman wasu gonakin da za su yi shuka ko dai a cikin jihar ko kuma a wasu guraren daban, musamman duba da cewa; sun dogara ne a kan wadannan sana’o’i na noma da kamun Kifi. Koda-yake dai, gwamnatin tarayya ta yi wani gini mai tsawon zurfin kimanin mita bakwai da nufin dakile ambaliyar ruwan daga Kogi, amma tuni ginin ya rushe tun daga farkon aikin. An dai gaza sake yin aikin ginin, yau kusan shekara uku zuwa hudu. Bugu da kari, tuni wasu gonaki, musamman a yankin na Muye da ake da kadada 2.6, aikin yin noma ya tsaya cak, inda kuma mazauna yankin a halin yanzu ke...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Edo ta kama mutane 95 da ake zargi da ayyukan ƙungiyoyin asiri. An kama mutanen ne a wani farmaki da aka kai kan masu aikata laifukan da suka shafi kungiyoyin asiri a garin Benin City da kewaye a makon da ya gabata. Kwamishinan ’yan sanda, Monday Agbonik, ya bayyana cewa an gurfanar da 64 daga cikin wadanda ake zargin suna da alaka da kungiyoyin Maphites, Eiye, da Aye kuma ake zarginsu da kisan gilla da aka yi kwanan nan a rikicin kungiyoyin asiri. Kayan da aka ƙwato sun hada da bindigogi biyu ƙirar gida, bindiga guda mai tashi daya, da harsashi 24. ’Yan sandan sun shawarci iyaye da su kula da ayyukan ’ya’yansu kuma sun gargadi...
    Shugaba Bola Tinubu ya yi alƙawarin ƙwato dazuzzuka da sauran yankuna a Arewa-Maso-Yamma da sauran sassan Nijeriya, yayin da yake jawabi a wata liyafa da tsofaffin shugabannin Katsina suka shirya. Ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ƙara amfani da fasahar sa ido don yaƙar ta’addanci da ƴan fashi. A cewar sanarwar kakakin shugaban ƙasa, Tinubu ya ce: “Za mu zuba hannun jari a fasaha domin kwato dazuzzuka. Tsaro batu ne na ƙasa baki ɗaya, ba na yanki ko gunduma kawai ba.” Shugaban ya kuma yi alƙawarin inganta filin jirgin sama na Katsina domin samar da ayyukan yi. Gidauniyar TY Buratai Ta Yi Kira Ga Tinubu Ya Ƙarawa Ma’aikata Albashi Kasar Sin Ta Goyi Bayan Rawar Da Hukumar IAEA Ke Takawa...
    “Manchester United ce fa kowane dan wasa na hankoron taka wasa a cikinta kuma idan kuka duba kungiyar a yanzu, kamar akwai matsaloli, ciki har da sauya koci da aka yi amma duk da haka muna da masaniyar abin da ya kamata, kuma abu ne mai sauki a ganar da dan wasa” in ji Amorim, wanda ya koma United daga Sporting Lisbon.   Ya kara da cewa magana ce ta karshen kaka kuma komai zai iya sauyawa. Amma dai suna so su fara komai da wuri kuma sun san yadda za su yi hakan. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na...
    Ya ci gaba da cewa, tuni aka fara gudanar da wasu manyan ayyukan a Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar, musamman a ta Lekki da ta Tin Can Island. Shugaban ya bayyana cewa, an kuma samar da kafar sadarwa ta zamani ga masu ruwa da tsaki a daukacin Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar, domin a rinka yin musayar Data, har da lokacin da ya dace, a fara gudanar da aiki. Ya sanar da cewa, idan an kammala wannan aikin, za su kara taimaka wa wajen kara inganta ayyukan Hukumar, na tsawon sa’oi 24. Dantosho wanda Manajan Sashen Tashar da ke a jihar Legas Lawal Ibrahim ya wakilce shi a wajen taron ya bayyana cewa, Hukumar ta kuma yi hadaka da Rundunar Sojin Ruwa,...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A cewar kakakin shugaban INEC, Rotimi Oyekanmi, “Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ba ta fitar da jadawalin ayyuka na babban zaben shekarar 2027 ba, inda ta kayyade lokacin da jam’iyyun siyasa za su yi yakin neman zabe a bainar jama’a, don haka bai dace ba, kuma ya saba wa doka, a ce wata jam’iyyar siyasa ta fara yakin neman zaben 2027.” Sai dai wasu lauyoyin da suka zanta da LEADERSHIP sun ce amincewa da ‘yan takara ba magana ce da za a ayyana a matsayin kamfe ba. A cewarsu, cin zarafin dokar zabe ne kowa ya fara yakinn neman zabe a yanzu. A nasa jawabin, Dr Wahab Shittu (SAN) ya danganta lamarin da rashin bin doka da...
    Sojoji sun hallaka wasu manyan ’yan ta’adda tare da yaransu masu yawan gaske a wata arangama a Ƙaramar Hukumar Talata Mafara da ke Jihar Zamfara. Shugabannin ’yan bindiga da suka haɗa da Auta Jijji da Dankali da Sagidi da Kachallah Rijaji da kuma Kachallah Suza sun sheƙa lahira ne a yayin musayar wuta da sojojin a ranar Alhamis. Kakakin Birget na 1 ta Sojin Ƙasa ta Najeriya, Kyaftin Suleiman Omale, ya ce sojojin sun ƙaddamar da aikin ne bayan samun rahoton cewa ’yan bindiga sun kai hari ƙauyen Mai Kwanugga inda suke ta ƙone gidajen al’umma. Ya bayyana cewa, “dakarun da ke sintiri suka yi artabu da dandazon ’yan bindiga, inda a yayin musayar wuta suka kashe shugabannin ’yan bindiga...
    Ministan harkokin wajen Iran ya sanar da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ci gaba da ake samu a shawarwari makamashin nukiliyar Iran tsakanin Amurka da Iran amma ana buƙatar gaskiya da hangen nesa daga ɗayan ɓangaren A yammacin jiya Juma’a ne ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Araqchi ya tattauna ta wayar tarho da Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres, inda suka yi musayar ra’ayi da musayar mahanga da kuma tattaunawa kan ci gaban yankin da kuma kasa da kasa. Araqchi ya kuma yi wa Guterres bayani kan sabbin abubuwan da ke faruwa a shawarwarin da ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, da kuma shirye-shiryen da masarautar Oman ta yi na tsara zagaye na...
    Jiragen saman yakin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai hare-hare kan yankunan birnin Damascus fadar mulkin Siriya da kuma yankin yammacin kasar Majiyoyin cikin gida na kasar Siriya sun bayyana cewa: Jiragen saman yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai hare-hare ta sama kan sansanonin sojin Siriya bayan da suka yi shawagi a kan garuruwan Hama, Dar’a, Damascus, yankin kan iyakar Siriya da Lebanon da kuma gabar tekun Siriya. Wadannan su ne fitattun abubuwan da suka faru a lokacin da jiragen saman yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai wa kasar Siriya hare—haren wuce gona da iri a yammacin ranar Juma’a. Rahotonni sun kara da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun kaddamar da hare-hare guda biyu kan birnin Al-Tall da ke cikin...
      Shugaban INEC ya jaddada muhimman ci gaban da ya samo asali daga sauye-sauyen da suka gabata da suka hada da fadada jaddawalin zabe, gyare-gyare don ba da damar kwanaki 180 tsakanin zaben fid da gwani na jam’iyya da zabe daga kwanaki 60 ya warware jinkirin kayan aiki. Ya ce wannan ya tabbatar da cewa an gudanar da babban zaben 2023 ba tare da jinkirta ba, a karon farko tun 2010.   Ya ce wani ci gaba kuma ya hada da samar da kayan aiki na cikin gida, yana mai cewa a karon farko tun 1999, an buga dukkan kayan zabe masu muhimmanci a Nijeriya,   Farfesa Yakubu ya bayyana kalubalen da ke bukatar kulawar majalisa, da suka hada da...
    Babban darektan hukumar kula da tattara bayanai da yada su ta bangaren teku ta kasar Sin, Shi Suixiang, ya bayyana cewa, manufofin tallafi da aka bullo da su a matakai na tsakiya da na kananan hukumomi sun karfafa ci gaban yawon shakatawar.   Ya kara da cewa, gwamnatin tsakiya ta inganta fadada hanyoyin jiragen ruwa da kayayyakin yawon shakatawa yayin da kuma ake kara daidaita tsarin rajistar jiragen ruwa da kuma shigar da su cikin hada-hada.   Wasu manazarta dai sun bayyana cewa, a sa’ilin da lokacin goshin damina ke gabatowa, ana sa ran yawon shakatawa na bakin teku da tsibirai a yankin kudu maso gabashin kasar Sin ya bunkasa, tare da kara samun balaguro ta ruwa da nufin cin...
    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya isa Jihar Katsina domin ziyarar aiki ta kwana biyu, inda zai ƙaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin jihar ta yi. Gwamnan Jihar Katsina Dikko Radda, da tsohon Gwamna jihar Bello Masari na cikin manyan mutanen da suka tarɓe shi tun daga filin jirgin Umaru Musa. Tinubu zai yi shekara takwas yana mulki – Afenifere Yadda aka yi bikin yaye sabbin matuƙa jiragen Rundunar Sojin Saman Najeriya Bayan isarsa ne kuma ya yi wa rundunar sojin ƙasar jawabi.
    Limamin da ya jagoranci sallar Jumma’a a nan Tehran Hujjatul Islam kazim Sadiki ya bayyana cewa kasar tana da kwararru wadanda suke da kwarewa a sanin fasahar nukliya da kuma hanyoyin dublomasiyya a tattaunawar da Iran take da Amurka dangane da shirin Nukliyar kasar. Tashar talabijin ta Al-alam a nan Tehran ta nakalto limamin yana fadar haka a khudubobinsa na sallar Jumm’a. Ya kuma kara da cewa, lalle tawagar kasar Iran a tattaunawar suna ci gaba da tattaunawa, sannan suna matukar iyawarsu don kare hakkin Iran na mallakar Fasahar Nukliya wacce take da matukar muhimmanci. Hujjatul Islam Sadiki ya kara da cewa tawagar Iran a wannan tattaunawar, suna amfani da tajruban da suke da shi a tattaunawar baya, sannan sauran...
    Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta yaye sabbin matuƙa jiragen sama 35 bayan sun kammala samun horo. Babban Hafsan Rundunar, Iya Mashal Hassan Abubakar, ne ya sanya sabbin matuƙa jiragen anini a yayin bikin da aka gudanar a Makarantar Tukin Jirgi na rundunar (401 FTS) da ke Kaduna. Yayen nasu ya zo ne watanni kaɗan bayan rundunar ta mallaki sabbin jiragen yaki guda 12, waɗanda suka ƙara mata ƙaimi wajen ayyukan samar da tsaro da kuma ta’addanci. A wani taro da ya gudanar da tsofaffin sojojin rundunar a Kaduna, Iya Marshal Hassan Abubakar ya shaida musu cewa rundunar tana jiran karin jiragen yaƙi guda 34. Ya buƙaci waɗanda aka yayen nasu da su yi amfani da wannan dama wajen cika...
    “Siyasar da na sani ba ita ce abin da ke faruwa a yau ba. Siyasar da na sani ita ce gwagwarmayar muradun jama’a don tabbatar da cewa suna da kyakkyawar rayuwa a duk fannoni kamar ilimi, ruwa, kiwon lafiya, da sauransu. “Na kasance a siyasa tsawon shekaru 48 da suka gabata,” in ji shi. Ya bayyana yanayin siyasa a matsayin wanda ke cike da rudani da son kai, yana mai jaddada cewa ‘yan siyasa da talakawa sun rikice. “Saboda wannan, akwai rudani ga masu nema da kuma wadanda ake nema. Masu neman suna makancewa, ba su da imani ko tausayi. Manufarsu kawai ita ce tabbatar da matsayi a gare su. A halin yanzu, talakawa sun tsunduma ciki yunwa, talauci, da...
    Kalli ya da Kwamishinan ’Yan Sanda na Babban Birnin Tarayya, Ajao Saka Adewale, ya yi hole ababen hawa da sauran kayan laifi da rundunarsa ta kama a gaban ’yan jarida a ranar Juma’a. Hotuna: Abubakar Sadiq Isah.
    Layukan dogo na kasar Sin sun gudanar da sufurin kusan fasinjoji miliyan 23.12 a jiya Alhamis, ranar farko ta bikin ranar ‘yan kwadago ta duniya da aka saba yi duk shekara a watan Mayu, kamar yadda kamfanin sufurin layin dogo na kasar Sin ya bayyana.   A cewar alkaluman da kamfanin ya fitar a yau Jumma’a, wannan adadi ya nuna karuwar kashi 11.7 cikin dari na adadin da ake samu a mizanin shekara-shekara. (Abdulrazaq Yahuza Jere)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin jin kai da rage radadin talauci na UNOCHA, Farfesa Nentawe Goshwe, ya sanar da yunkurin hukumar na ficewa daga Nijeriya. Ya shaida hakan ne a yayin taron kara wa juna sani kan tsarin da za a dauka a Nijeriya, wanda aka gudanar a cibiyar yaki da ta’addanci ta kasa, ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro a Abuja. A cikin wata wasika da aka yada a shafin intanet na hukumar a ranar 11 ga Afrilu, shugaban hukumar ta UNOCHA, Tom Fletcher ya ba da sanarwar yanke ayyuka sakamakon karancin kudade na kusan dala miliyan 60 a shekarar 2025. Hukumar ta ce za ta rage ayyukanta a Nijeriya, Kamaru, Kolombiya, Eritriya, Iraki, Libya, Pakistan, Turkiyya da Zimbabwe,...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wata ƙungiyar matasa mai suna “North-East Coalition Against Terrorism” ta yi maraba da Major General Abdulsalam Abubakar, sabon kwamandan yakin Operation HADIN KAI (OPHK), inda ta bayyana cewa tana fatan zaman lafiya ya dawo yankin. A cikin wata sanarwa da Ismail Mustapha da Sakatare Danlami Bukar suka rattaba hannu, ƙungiyar ta ce Sojojin Nijeriya a ƙarƙashin babban Hafsan Soja Janar Chris Musa za su ci gaba da matsa lamba kan mayakan. Ta kuma yi kira ga al’ummar yankin su ba sabon kwamandan goyon baya. Boko Haram Sun Kashe Masu Kamun Kifi 18 A Borno Sojoji Sun Harbe Mutane Biyu Har Lahira Da Ake Zargi Ɓarayin Mota Ne A Filato  Ƙungiyar ta gargadi matasa su ƙi tayin shiga ƙungiyoyin da ba...
    Kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC reshen jihar Kano ta yabawa gwamnatin jihar Kano kan kudirin ta na daidaita bashin da ake bin ‘yan fansho da ya haura naira biliyan 16.       Da yake jawabi yayin bikin ranar ma’aikata da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha da ke kofar Mata a Kano, shugaban kungiyar kwadago ta NLC, Kwamared Kabiru Inuwa, ya bukaci ma’aikatan Nijeriya da su jajirce wajen tabbatar da adalci da walwala.     Kwamared Inuwa ya bayyana cewa duk da nasarorin da gwamnatin ta samu wajen horas da ma’aikata, har yanzu akwai bukatar karin ma’aikata masu tallafawa a ma’aikatun gwamnati da na kananan hukumomi.     Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatin sa...
    Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya ce gwamnatinsa ta himmatu wajen gina jihar da ma’aikata za su bunkasa, samar da ayyukan yi masu nagarta, da baiwa kowane bangare damar bayar da gudunmawa mai ma’ana ga ci gaban jihar.   Gwamna AbdulRazaq a cikin sakonsa na bikin ranar ma’aikata ta duniya na shekarar 2025, a Ilorin, ya mika sakon gaisuwa ga maza da mata da jama’a da kungiyoyi masu zaman kansu wadanda kokarinsu ke karfafa tattalin arziki da samar da makomar al’ummarmu.   Ya yaba da gagarumar gudunmawar da ma’aikata ke bayarwa a kowane fanni na sadaukarwa, juriya, da fasaha wanda ya sa su zama ginshiƙan girma da ci gaba.   Gwamnan ya jaddada kudirin gwamnatin na aiwatar da manufofin da...
    Gwamnatin jihar Kebbi, ta baiwa ma’aikatan jihar tabbacin ci gaba da jajircewa wajen kyautata jin dadin su da kuma kare hakkokinsu.   Gwamna Nasir Idris wanda ya ba da wannan tabbacin a lokacin da yake jawabi ga ma’aikata domin bikin ranar watan Mayu a Birnin Kebbi, ya jaddada cewa ma’aikata aminai ne masu kima wajen ci gaban jihar Kebbi, kuma su kasance masu ruwa da tsaki da ba za a yi watsi da su ba.   Gwamna Idris, wanda ya bayyana bikin ranar Mayu a matsayin wani muhimmin lokaci, ya yabawa ma’aikatan bisa jajircewarsu da irin gagarumar gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban jihar.   “Kwazonku da jajircewarku sune kashin bayan tattalin arzikinmu. Ina yaba muku kan kokarinku na...
    Gwamna Umar Namadi ya bi sahun kungiyoyin kwadago domin tunawa da irin gudunmawar da ma’aikata ke bayarwa wajen ci gaban jihar Jigawa.   Da yake gabatar da jawabinsa, Gwamna Namadi ya yaba da jajircewar ma’aikatan Jigawa, inda ya bayyana ma’aikata a matsayin masu kawo ci gaba.   Ya bayyana cewa, ma’aikata a dukkan bangarori suna aiki da gaske a matsayin injin da ke ba da kuzarin motsa al’umma zuwa ga ci gaba.   Ya kuma kara jaddada kudirin gwamnatinsa na samar da walwalar ma’aikata, inda ya bayar da misali da nasarorin da aka samu da suka hada da aiwatar da mafi karancin albashi na Naira 70,000, gina gidaje masu saukin kudi ga ma’aikatan gwamnati, da kuma shigar da sama da...
    Shugaban Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’in Najeriya (SSANU), Comr. Muhammad Haruna Ibrahim ya bukaci gwamnatin jihar Taraba da ta gaggauta biyan ‘yan kungiyar SSANU, jami’ar Jalingo ta jihar Taraba alawus-alawus da suke bi bashi.   Comr. Haruna ya yi wannan bukata ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron majalisar zartarwa na shiyyar karo na 11 da ya gudana a Jalingo.   Shugaban SSANU ya dage cewa ya kamata a yi wa ’ya’yan kungiyar adalci, domin wadanda ba aikin koyarwa ba na daga cikin bangarori hudu da suka kafa jami’a.   Sai dai ya yi gargadin cewa kungiyar ba za ta goyi bayan duk wani memba da ya sabawa ka’idojin jami’a ba.   Tun da farko, Comr. Bitrus Joseph Ajibauka,...
    A wurin mu Malikawa, mun dauki watannin nan guda uku a matsayin lokacin Hajji, wasu kuma sun ce a’a, daga kwana goman farkon nan na Zhul-hijja, lokacin ya kare, to amma kuma idan aka yi la’akari za a ga cewa akwai sauran ibadodin Hajjin da suka shige wadannan kwanakin goma irin su Jifa da ake dawowa Mina a yi bayan Sallar Idi da Dawafin bankwana. Shi ya sa Malikawa muka dauki watannin ukun baki daya a matsayin lokacin Hajji. Kuma Ibn Hazan ya goyi bayan haka, don ba za a dauki wata biyu da kwana goma a ce musu watanni uku ba.   Kamar yadda bayani ya gabata, Hajji ba a ko ina ake daura haramar yin sa ba, yana...
    Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umar Bago ya bayyana dangantakarsa da mataimakinsa, Kwamared Yakubu Garba a matsayin cikakkiya da jituwa.   Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai kan dangantakarsa da mataimakinsa bayan bikin ranar ma’aikata a Minna.   A cewarsa, “mu kungiya ce, ba za su iya karya mu ba, hankalinmu yana kan manufa, kuma za mu cimma ta.”   Gwamnan ya bukaci al’ummar jihar da su ci gaba da marawa gwamnatinsa baya, tare da tabbatar da cewa wata sabuwar Nijar za ta yiwu.   Binciken da aka gudanar ya nuna cewa mataimakin gwamnan jihar Neja, Kwamared Yakubu Garba bai halarci bikin ranar ma’aikata ta bana a Minna ba wanda wasu al’ummar Nejar din...
    Jami’an tsaron sa kai sun kama wasu abokai biyu masu sana’ar  acaba, bisa zargin yin fyaɗe ga wata Bafulatana mai tallar fura da nono a Yankin Babban Birnin Tarayya Abuja. Wani jami’in tsaron sa kai, Usman Dantala, ya ce abokan biyu sun yi wa Bafulatanar fyade ne da tsakar rana a yankin Ikwa da ke Ƙaramar Hukumar Gwagwalada. Ya bayyana cewa ranar Asabar da misalin karfe 2:12 na rana ne abokan biyu suka yaudari mai faurar ’yar kimanin shekaru 19 zuwa daƙin wani abokinsu inda suka yi mata fyade. Jami’in ya ce, sun kira Bafulatanar ne da cewa za ta sayar musu da nono a gidan wani abokinsu. A can ne suka yaudare ta shiga daƙin suka kuma yi mata...
    Binciken LEADERSHIP ya nuna cewa, duba mara lafiya guda daya tak da ke dauke da cutar Maleriyar da ba ta yi karfi sosai ba a asibitin gwamnati, na lashe kimanin Naira 17,000, tsakanin ganin likita, yin gwaje-gwaje da kuma magunguna.   Wadannan kudade sun kai kimanin Naira tiriliyan 1.156 da ake kashewa a kan wannan cuta, amma asalin kudaden sun zarta haka, musamman idan Maleriyar ta yi kamari, za a iya kashe ninki uku ko sama da haka na wannan kudi.   Yayin da duniya ke yin wannan biki na ranar Maleriya, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta nanata cewa, cutar na ci gaba da zama barazana, musamman a yankuna masu fama da zafi, duk da cewa; cuta ce da...
    Kamar yadda firaministan kasar Malaysia Anwar bin Ibrahim ya fada a kwanan baya cewa, yayin da kasa da kasa ke fuskantar mawuyacin hali, suna bukatar samun tabbaci da wani nagartaccen shiri na samun ci gaba. Don haka, ana ganin yadda kasar Sin ta samu nasarori, an nuna yabo ga kasar ta Sin, kasar Sin ta kawo tabbaci da kuma kyakkyawar makoma ga duniya. (Zainab Zhang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: An dage zaman tattaunawan Iran da Amurka ne bisa shawarar kasar Oman Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi nuni da cewa: Ministan harkokin wajen kasar Oman ne ya sanar da sauyin lokacin zaman tattaunawan ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, yana mai bayanin cewa, dage shawarwarin ya zo ne bisa shawarar ministan harkokin wajen kasar, kuma za a sanar da wata sabuwar rana daga baya. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya sanar da manema labarai cewa: An canja ranar da za a gudanar da zaman shawarwarin ba na kai tsaye ba na gaba tsakanin Iran da Amurka, wanda aka shirya gudanarwa a...
    Ministan Tsaron kasar Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin yahudawan sahayoniyya ta zama babbar alamar ta’addanci a duniya Ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh, yayin da yake yin Allah wadai da kisan gillar da yahudawan sahayoniyya suke yi wa al’ummomin Falastinu da na Lebanon a daidai lokacin da kungiyoyin kasa da kasa da tarurrukan kasa da kasa suka yi shiru, yana mai cewa: A yau al’ummar yahudawan sahayoniyya ta zama wata babbar alama ta ta’addancin kasa a duniya. Birgediya Janar Nasirzadeh ya furta haka ne a ganawarsa da ministan tsaron Jamhuriyar Zimbabwe Uba Muchinguri Kashiri a lokacin ziyararsa a kasar Iran, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi kasashen biyu. A cikin wannan ganawar, ministan tsaron na Iran ya...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Kimanin Naira biliyan ɗaya ce aka ƙiyasta ta salwanta sakamakon gobarar da ta ƙone wani sashe na babbar kasuwar da ke tsakiyar garin Jos, babbar birnin Jihar Filato. An rawaito cewar gobarar ta laƙume shaguna fiye da ɗari biyar, galibinsu na masu sayar da kayan gwanjo. Mutane da dama dai sun rasa hanyar cin abincinsu, kasancewar galibinsu sun dogara ne da samun da suke yi a kullum a wannan kasuwa don ciyar da iyalansu. Ko a wane hali waɗanda suka tafka wannan asara suke ciki bayan wannan ibtila’i? NAJERIYA A YAU: Dalilan Kamuwa Da Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Magance Ta DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya Wannan na...
    Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi Allah wadai da matsayin Amurka na goyon bayan haramta hukumar kula da ‘yan gudun hijira falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi Allah wadai da matsayin Amurka na goyon bayan haramtacciyar kasar Isra’ila kan haramta hukumar kula da ‘yan gudun hijiran Falasdinawa da ayyukan ba da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya “UNRWA”, tana daukan wanan a matsayin Amurkia na ci gaba da nuna son kai da goyon bayan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ‘yar mamaya da kuma rashin mutunta dokokin kasa da kasa da yarjejeniyar jin kai. A cikin wata sanarwar manema labarai da ta fitar jiya Alhamis, kungiyar Hamas ta yi nuni da cewa: Shigar da Amurka...
    Ana sa alamar tambayar cewa: Shin gobarar da ta tashi a birnin Kudus… shin sako ne na ranar tunawa da kafuwar gwamnatin ‘yan sahayoniyya? Gobarar da ta tashi a tsaunin Kudus da aka mamaye ta bazu zuwa manyan yankuna a cikin haramtacciyar kasar Isra’ila, inda ta kewaye wani sansanin soji tare da cinye filayen masu girma da tsayi. Hakan ya sa hukumomin gwamnatin mamayar Isra’ila suka kafa dokar ta baci tare da neman taimakon kasashen duniya. Yayin da Ministan tsaron cikin gidan Isra’ila Itamar Ben-Gvir yake neman dora wa Falasdinawa, alhakin tashin gobarar. Gobarar ta kunno kai ne a daidai lokacin da yahudawan sahayoniyya suka fara gudanar da bukukuwan cika shekaru 77 da kafuwar gwamnatinsu ta mamaya a kasar Falasdinawa,...
    Haka kuma, kasar Sin ta yi nuni da cewa, matakan kasar Amurka kan harajin kwastam sun kawo illa ga cinikayyar duniya, da moriyar kasashe masu tasowa, amma kasar Sin a nata bangaren kokari take yi wajen tabbatar da bunkasar cinikayya ta duniya, da kuma tsayawa tare da kasashe masu tasowa. (Zainab Zhang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Faɗin ginin, wanda ya haura sukwaya mita 13,000, ya ƙunshi babban ginin tashar da ababen da ke tattare da shi, kuma zai kasance tashar da ta fi kowace girma a layin dogon da ake kira Kaka Reluwe.   Kaka Reluwe na nufin hanyar dogo daga KAduna zuwa KAno.   Kamfanin CCECC ya ce idan an gama aikin, zai taimaka gaya wajen haɓaka harkokin sufuri kuma ya kawo matuƙar sauƙi ga miliyoyin matafiya a ɓangaren Kano na hanyar jirgin.   Shi dai wannan layin dogo na Kaka Reluwe, hanya ce mai tsawon kilomita 204. Ta tashi daga Kaduna, ta bi ta Zariya, zuwa Kano.   Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ne ya ƙaddamar da ita a ranar 15 ga Yuli, 2021, sannan...
    Gwamnan ya kara da bayyana biyan Biliyan 16 na basussukan fansho, da kuma sauya mafi karancin fansho daga ₦5,000 zuwa ₦20,000, da kuma fitar da Naira miliyan 100 domin tallafawa ayyukan ’yan fansho.   A wani mataki makamancin haka, gwamnan ya sanar da kafa sabbin ma’aikatu 4 da hukumomi 2 da za su zaburar da samar da ayyukan yi da kirkire-kirkiren fasaha a jihar.   Wadannan sun hada da ma’aikatun raya gidaje, tsaron cikin gida, daskararrun ma’adanai, da wutar lantarki da makamashi mara illa, sannan kuma ya kafa hukumomar bunkasa ICT ta jihar Kano da hukumar kula da kanana da matsakaitan masana’antu.   Gwamna Yusuf ya kuma ba da sanarwar umarnin fara aiwatar da shirin mafi karancin albashi na ₦71,000...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wasu ’yan bindiga da ake zargin ’yan fashi ne sun kai hari kan wani jirgin ruwa da ke jigilar mata ’yan kasuwa zuwa Ƙaramar hukumar Ijaw ta Kudancin Jihar Bayelsa, a kan hanyar ruwan Lobia/Foropa. Rahotanni sun ce maharan sun yi garkuwa da wasu mata huɗu a lokacin da lamarin ya faru a ranar Talata. NAJERIYA A YAU: Dalilan Kamuwa Da Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Magance Ta Najeriya za ta karɓi baƙuncin Gasar Karatun Alkur’ani ta Duniya a karon farko  Wata majiyar unguwar da lamarin ya faru ta shaida wa Daily Trust a safiyar ranar Alhamis, maharan sun kai harin ne ’yan mintuna kaɗan bayan jirgin ruwan fasinjan ya tashi daga gaɓar ruwan Swali a Yenagoa, babban birnin jihar....
    Zargin sabani tsakanin Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, da mataimakinsa, Kwamred Yakubu Garba, ya karu a yau Alhamis bayan da mataimakin gwamnan ya kaurace wa bikin Ranar Ma’aikata a birnin Minna, babban birnin jihar. LEADERSHIP ta ruwaito cewa Kwamred Garba, wanda shi ne tsohon shugaban reshen jihar na ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC), bai taɓa kin halartar bikin Ranar Ma’aikata ba tun bayan da ya zama mataimakin gwamna. Sabanin shekarar da ta gabata, Kwamred Garba bai bayyana a wannan shekarar ba duk da cewa Gwamna Bago da Sanata mai wakiltar mazabar Neja ta Gabas, Sani Musa, sun halarta, lamarin da ya ƙara zafafa zargin rikici tsakaninsa da gwamnan. Wasu majiyoyi sun ce yana wajen gari, yayin da wasu ke...
    Babu tabbacin ko ya rasu sakamakon rashin lafiya ko kuwa an kashe shi. An ce ‘yan bindigar sun fara neman Naira miliyan 20 a matsayin kudin fansa, amma iyalansa sun iya haɗa Naira miliyan 11 ne kacal. Sun kuma buƙaci sabon babur da kayan abinci, duk a matsayin kuɗin fansa. Bayan da matar da ta tsere ta shaida wa jama’a abin da ya faru a ranar Litinin, sai aka yi masa sallar jana’iza a ranar Talata kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Rundunar ‘yansandan Jihar Zamfara, ta bakin kakakinta DSP Yazid Abubakar, ta ce har yanzu ba ta samu labarin tabbacin mutuwar limamin da iyalansa daga hukumomi ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
    Ya kai wannan mataki ne bayan lashe Copa del Rey a wasan ƙarshe da Real Madrid a filin wasa na La Cartuja a Seville. Yamal ya fara buga wasa a Barcelona a shekara ta 2023, inda ya fara a gasar La Liga a wasan da suka buga da Betis, yana da shekaru 15 da watanni tara a lokacin. Tun daga wannan rana, ya ci gaba da kafa tarihi a ƙungiyar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya kai wannan mataki ne bayan lashe Copa del Rey a wasan ƙarshe da Real Madrid a filin wasa na La Cartuja a Seville. Yamal ya fara buga wasa a Barcelona a shekara ta 2023, inda ya fara a gasar La Liga a wasan da suka buga da Betis, yana da shekaru 15 da watanni tara a lokacin. Tun daga wannan rana, ya ci gaba da kafa tarihi a ƙungiyar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Amma shugaban EFCC ya ce hakan ba gaskiya ba ne. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sakataren Majalisar koli ta tsaron kasar Iran wanda ya halarci taron kungiyar “Brics” a kasar Brazil ya bayyana cewa; Makaman Nukiliya ba su cikin akidar tsaron kasar Iran. Ali Akbar Amhadiniyan ya kuma kara da cewa; Iran ba za ta amince da kin aiki da hakkokinta na cin moriyar fasahar makamashin Nukiliya a fagagen zaman lafiya ba. Da yake Magana akan Falasdinu kuwa, sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya ce: “Amfani da karfi domin kai wa ga sulhu” da “Diflomasiyya ta dole” akidun siyasa ne masu hatsarin gaske, yana mai kara da cewa; ta hanyar shimfida adalci ne ake kai wa ga sulhu,haka nan kuma yin furuci da hakokin da suke halartattu. Akan barazanar da wasu kasashe suke...
      Cikin adadin, masu bayyana ra’ayoyi daga kasashen Saudiyya da Serbia, suna cikin mafiya bayyana matukar baiken matakin na Amurka, da karin kaso 28.5 bisa dari. Yayin da a daya bangaren al’ummun Malaysia, da Isra’ila, da Australia, da Singapore, da Philippines, da Najeriya, da Portugal, da Pakistan, da Afirka ta kudu, kasonsu na nuna baiken matakan kara harajin na Amurka ya karu da sama da kaso 20 bisa dari. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin jihar ta ce, matakin na daya daga cikin kokarin gwamnati mai ci na inganta ayyukanta domin samar da romon dimokuraɗiyya ga al’ummar jihar Sokoto. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A ko da yaushe Sin tana himmatuwa wajen wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tekun kudancin kasar Sin, tare da kira da a warware rikici ta hanyar tattaunawa. A sa’i daya kuma, aniyarta ta kiyaye ikon mulkin kasa, da hakki da moriyarta a tekun kudancin Sin ba za ta sauya ba. Ita kasar Philippines kuma za ta dandana kudarta bisa ga yadda ta aiwatar da mummunan mataki kan batun zirin tekun Taiwan, da nufin biyan bukatun Amurka game da dabarunta a yankunan tekun Indiya da na fasifik. (Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin...
    A ganin gwamnatin Amurka, manufar ramuwar haraji za ta taimaka wajen farfado da masana’antu a kasar da kara samar da guraben aikin yi, amma yadda ta daidaita matsalolin tattalin arzikinta ba ta hanyar da ta dace ba, da kuma gazawa wajen bin ka’idojin tattalin arziki, ya haifar da damuwa a zukatan al’umma da kuma tsoro a kasuwanni, lamarin da ya sa Amurka ta kara shiga mawuyacin hali.   Cikin kwanaki 100 da suka shude, wasu kasashen duniya sun ki mika wuya ga cin zalin Amurka ta fuskar manufar ramuwar haraji. Misali, kasar Sin ta fara mayar da martani, a kokarin kiyaye halastattun hakkokinta da tsarin tattalin arziki da cinikayya da ma na adalci a duniya. Kana kuma kungiyar tarayyar Turai...
    Ya kara da cewa, shugaban kasa Bola Tinubu da sojojin Nijeriya suna aiki tukuru domin ganin an ga sauye-sauye a yaki da ta’addanci da ake yi, a fili kuma a bayyane. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A cewarsa, wajibi ne shirin ya mayar da hankali kan burin cimma zamanantarwa irin ta gurguzu da nufin gina babbar kasa da samun ci gaba wajen farfado da ita. Shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar, wanda shi ne daftarin dake zaman jigon jagorantar ci gaba na matsakaici da dogon zango a bangaren tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin, yana zayyana baki dayan burikan kasar da manyan ayyuka da manufofin da ake aiwatarwa a dukkan bangarori cikin shekaru 5. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
    Rayukan al’umma gami da dukiya musamman na ababen hawa na ci gaba da salwanta a Mahadar hanya ta yankin Tipper-garage da ke Dutse-Baupma, da ke kan titin da ya tashi daga garin Dutsen-Alhaji ya nufi garin Bwari, a yankin Birnin Tarayya Abuja. Titin da ke mastayin tagwaye ya haɗa yankin da garin Jere da ke Jihar Kaduna. Hanyar na ci gaba da ganin ƙaruwar kwararan motoci a sakamakon ingancinta da kuma karancin matsalar tsaro, idan a ka kamanta ta da babban titi Abuja zuwa Kaduna. Rawar da Arewa za ta taka a Zaɓen 2027 An ɗaure ’yar shekara 80 a kurkuku saboda dukan jikarta da silifas Adadin motoci da ke bin titin ya kara dagawa a bayabayan nan a dalilin...
    Sun ce suna tafiya daga Yola zuwa Lafia ne lokacin da wasu mutane da ake zargin ‘yan fashi ko masu garkuwa da mutane ne suka kai musu hari, lamarin da ya sa suka tsere zuwa daji don tsira rayukansu. Sojojin sun taimaka wajen gyara tayar motar sannan suka tabbatar da cewa fasinjojin sun ci gaba da tafiyarsu cikin tsaro. Shugaban Runduna ta 6, Birgediya Janar Kingsley Uwa, ya yaba wa sojojin bisa saurin ɗaukar mataki da kuma tsayin daka kan aiki. Ya kuma buƙaci jama’a da su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro haɗin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai a kan lokaci domin taimakawa wajen yaƙi da laifuka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun...
    Rahotannin da suke fitowa daga kasar Yemen na cewa katafaren jirgin ruwa mai daukar jiragen saman yaki malakar klasarAmurka wato USS Harry Truman zai fice daga tekun red sea da nan kusa saboda makaman kasar Yemen da suka fada mata. Tashar talabijin ta Almasirah ta kasar Yemen ta nakalto wani jami’in ma’aikatar tsaron kasar wanda baya son a bayyana sunansa yana cewa, saboda yawan hare haren da sojojin Yemen suka kaiwa jirgin, wadanda suka hada da amfani da makamai masu linzami samfurin Crusse da kuma Balistic, har ila yau da jiragen yaki masu kunan bakin waken da suka fada a kansa. A yanzun ya zama dole jirgin ya fice daga tekun. Tun cikin watan Maris da ya gabata ne gwamnatin...
    A Kaduna, an kama wasu mutane uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, ciki har da wani da ya ce ya koma jihar ne domin kafa sabuwar ƙungiya bayan an kama abokan aikinsa a Kwara. Haka kuma, an kama wasu biyu da ke ɗauke da bindigogi. ‘Yansanda sun gano makamai da dama, ciki har da bindigogi ƙirar AK-47 da AK-49, da kuma wasu makamai da aka ƙera a gida. Wannan aiki na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na yaƙar garkuwa da mutane da safarar makamai a faɗin ƙasar. Kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya ce ana ci gaba da bincike, kuma za a gurfanar da waɗanda ake zargi a kotu da zarar an kammala binciken. Ya kuma yaba da goyon...
    Haka kuma wasu hukumomin gwamnati sun taimaka, ciki har da Hukumar ‘Yan Gudun Hijira ta Ƙasa, Hukumar Shige da Fice, Hukumar Tsaro ta DSS, Hukumar Lafiya ta Tashar Jirgin Sama da Rundunar ‘Yansanda. Mutane biyu daga cikin waɗanda aka dawo da su na fama da matsananciyar rashin lafiya, kuma an garzaya da su asibitin New Ikeja don a duba lafiyarsu. Bayan an yi musu rijista da ɗaukar bayanan yatsunsu, an mayar da su cibiyar mazauna ‘yan gudun hijira da ke Igando, a Jihar Legas, inda za su samu taimako don ci gaba da rayuwa. NEMA ta ce wannan wani ɓangare ne na ƙoƙarinta na tallafa wa ‘yan Nijeriya da ke cikin mawuyacin hali a ƙasashen waje da kuma taimaka musu...
    A yammacin ranar Talata Arsenal ta karbi bakuncin PSG a matakin wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin zakarun Turai na bana. An dai barje gumi ne a filin wasa na Emirates, inda PSG ta yi wa Arsenal ci daya mai ban haushi har gida. DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya ISWAP ta ɗauki alhakin kashe mutum 26 a Borno PSG ta fara cin ƙwallo ta hannun Ousmane Dembele a minti na huɗu da take leda, haka suka je hutu har da zagaye na biyu, amma Gunners ba ta farke ba. Wannan shi ne karo na biyu da suka fuskanci juna a Champions League a kakar nan, inda Gunners ta yi nasarar cin 2-0...
    Kakakin kwamitin tsaron kasa a majalisar shawarar musulunci ta Iran ya bayyana cewa; ” Ya zuwa yanzu ba za mu iya yin hukunci akan dalilan da su ka haddasa fashewar abubuwa a tashar ruwa ta Shahid Raja’i ba, amma za mu iya cewa babu hannu waje a ciki. Kakakin kwamitin tsaron kasar ta Iran Ibrahim Rizai wanda ya halarci taron da aka yi a Majalisa akan fashewar da aka samu a tashar ruwan ta shahid Raja’i, ya kuma kara da cewa; Fahimtata da abinda na ji daga abokan aikina dangane da abinda ya faru a tashar ruwa ta Shahid Raja’i, da kuma rahotannin da su ka iso mana, shi ne cewa abinda ya farun ba shi da alaka da waje.”...
    Wani bon kirar hannu da aka dasa akan hanyar dake hada Rann da Gamboru a jihar Borno ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 6. Daga cikin wadanda su ka rasa rayukansu sanadiyyar tashin bom din sun hada mata da kananan yara kamar yadda majiyar ‘yan sanda ta sanar. Kungiyar nan mai suna; gwamnatin musulunci a yammacin Afirka ce ta sanar da daukar alhakin kai hari na ranar Litinin din da ta gabata. Bugu da kari sauran wadanda su ka rasa rayukan nasu manoma ne da suke cikin motar a-kori-kura da ta taka nakiya. Baya ga wadanda su ka rasa rayukansu, wasu mutanen su 3 sun jikkata,kuma tuni an dauke su zuwa asibiti domin yi musu magani. Wani dan sintiri da yake...
    Shugaban tawagar baƙin, Alhaji Ibrahim Abdullahi Yar’adua, ya ce sun zo Yobe domin nazarin halin tsaro da tattara bayanai da za su taimaka wajen tsara manufofin tsaron ƙasa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Mista Mark Joseph Carney murna bisa zaɓensa a matsayin Firaiminista na 24 na ƙasar Kanada, bayan nasarar jam’iyyar Liberal a zaɓen majalisar dokokin da aka kammala kwanan nan.   A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya bayyana zaman Carney a wannan matsayi a matsayin wani muhimmin ci gaba, musamman a wannan lokaci da Kanada ke bukatar gogaggen shugaba domin fuskantar ƙalubale da dama.   Carney, wanda fitaccen masani ne a fannin tattalin arziki, ya taba rike mukamin Gwamnan Babban Bankin Kanada daga shekarar 2008 zuwa 2013, sannan ya ci gaba da zama Gwamnan Babban Bankin Ingila daga 2013...
    Hukumar Fensho ta Jihar Jigawa da Kananan Hukumomin jihar ta shirya fara aikin tantance ‘yan fansho da ke cikin tsarin. Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, Alhaji Muhammad K. Dagaceri ne ya bayyana haka yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Gidan Fansho, inda shugabannin kungiyar ‘Yan Fansho ta Najeriya reshen Jigawa suka halarta. A cewarsa, an shirya fara aikin tantancewar ne daga ranar Litinin, 5 ga Mayu, 2025. Alhaji Dagaceri ya bayyana cewa, an shirya hakan ne da nufin sabunta tsarin biyan fansho tare da tabbatar da ingancin bayanai. Ya ce, aikin tantancewar zai gyara wasu ‘yan kura-kurai da suka kunno kai a cikin shekaru uku da suka gabata, da kuma tabbatar da ingantattun bayanai a jadawalin...
    “Gwamnati ta amince da hada hannu da shugabannin al’umma na cikin gida domin tabbatar da tsaro.   “Muna gode muku kan abin da kuke yi. Amma muna bukatar Sarakuna su yi magana da mutanenmu kan kokarin da dukkanmu muke yi don kare al’ummominmu daga masu kutse.”   Gwamnan ya yi kira da a inganta hadin gwiwa a tsakanin al’umma da hukumomin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyi.   Mataimakin Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kwara, Alhaji Ibrahim Bologi II, wanda shi ne Etsu Patigi, ya yaba wa gwamnan bisa hada gwiwa da su domin tabbatar da tsaro a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
    Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ya bayyana kalaman gwamnatin ‘yan sahayoniyya a matsayin wani rudu da ba shi da amfani da har zai yi tasiri a zaman tattaunawan Iran da Amurka Wanda ba na kai tsaye ba, yana mai cewa duk wani hari ko da karami ne za a kai kan Iran zai zama tamkar tartsatsin wuta da zai iya janyo tashin gobara da zai iya kona yankin gaba daya. A jawabin da ya gabatar yayin taron kolin majalisar shawarar Musulunci ta Iran a yau Talata, Muhammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa: Firai ministan gwamnatin yahudawan sahayoniyya mai laifi ne mai zubar da jinin fararen hula, saboda neman hana mutuwarsa a fagen siyasa, kuma yanzu yana yin barazana ga al’ummar Iran...
    Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta bayyana cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila’ tana aiwatar da kisan kiyashi kan Falasdinawa ana gani kai tsaye a tauraron dan Adam Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International a yau Talata ta yi Allah wadai da shirun da duniya ta yi game da yadda gwamnatin yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya take aiwatar da kisan kiyashi a zirin Gaza, kai tsaye duniya na gani ta hanyar tauraron dan Adama. A yayin gabatar da rahoton shekara-shekara na kungiyar ta Amnesty kan kare hakkin bil’adama a duniya Agnes Callamard, sakatariyar kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International, ta ce tun ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023, duniya ke kallon yadda ake aiwatar...
    Jaridar The Guardian ta Buga Labarin Cewa: Gidajen yarin Girka sun cika makil da ‘yan gudun hijirar Sudan Jaridar The Guardian ta kasar Britaniya ta ruwaito cewa: Mahukuntan kasar Girka na tsare da daruruwan bakin haure ba bisa ka’ida ba a karkashin wata doka mai tsauri da ta fara aiki a shekara ta 2014 kuma dokar ta kunshi hukunta masu laifin daurin shekaru 25 a gidan yari. Jaridar ta The Guardian ta ruwaito cewa: Masu fasakwaurin mutane da aka yanke wa hukunci sun zama rukuni na biyu mafi girma a gidajen yarin Girka, bayan masu safarar miyagun kwayoyi. Jaridar ta bayyana cewa ‘yan Sudan su ne rukuni na hudu mafi girma na masu neman mafaka a kasar Girka, inda suka...
    Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi, ya amince da nadin Aisha Shehu Mujaddadi a matsayin shugabar Hukumar Kula da Zuba Jari ta Jihar Jigawa (InvestJigawa). Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya fitar ga manema labarai. Sanarwar ta ce “Aisha Mujaddadi ta samu digirinta na farko a fannin tattalin arziki a Jami’ar Maiduguri a shekarar 1996, ta kara inganta iliminta da samun digiri na biyu a fannin Gudanar da Kasuwanci (MBA) daga Jami’ar Bayero, Kano a shekarar 2011.“ Malam Bala Ibrahim ya bayyana cewa Aisha Mujaddadi ta samu  gogewa na tsawon shekaru 19 a fannin aikin shawarwari na ci gaban kasa da kasa, inda ta yi aiki a kan muhimman...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    kauyuka a China, ana nufin yankunan da suka bunkasa, wadanda suka kasance, sun yi kamance-ceniya da sun anguwanin GRA a Nijeriya da kuma a nahiyar Afirka.   A yankin na Hero Bay, an tanadar da tituna inganciyyar wutar lantarki, tsaftatattacen ruwan sha da kuma kafar Inernet   Akwai manyan bene masu tsawo a yankin, wadanda tsawonsu ya dara na bene mai hawa biyar, inda kuma aka tanadar wa da yankin, ababen more rayuwa.   kananan hukumomi ne, suka gina wadannan matsugunnan, musamman donin a dakile barazanar kwararowa alumma daga kauye, zuwa cikin birane.   A gwajin da aka yi na yankunan da su habaka sosai a China, ana buga misali da Hero Bay kan yadda gwamnati ke bai wa alumma...
    Wannan ya sa wasan yau zai zama mai ɗaukar hankali, domin kowanne daga cikinsu na burin ɗaukar kofin a karo na farko, domin a dakatar da yawan dariyar da ‘yan adawa ke musu. A zagayen rukuni da suka haɗu a farkon wannan kakar, Arsenal ta lallasa PSG da ci 2-0. Kocin Arsenal yanzu, Mikel Arteta, ya taɓa buga wasa a duka ƙungiyoyin. Yana fatan ya zama kocin farko da zai jagoranci Arsenal ta lashe kofin Zakarun Turai. Wannan ya sa magoya bayan Arsenal ke fatan ganin ƙungiyarsu ta yi abin mamaki a wasan da za a fara da misalin ƙarfe 8 na dare agogon Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
    Kalli yadda aka karɓi ’yan Najeriya guda 203 da aka dawo da su daga ƙasar Libya. (Hoto: Onyekachukwu Obi).
    Michael, wanda ke zaune a Phase 4, ya yi ƙoƙarin ceton abokinsa, amma shi ma makiyayin ya sare shi da adda. An garzaya da Michael zuwa Asibitin Mararaba domin ceto rayuwarsa, amma likita ya tabbatar da mutuwarsa bayan isar su. ‘Yansanda sun bayyana cewa an adana gawar Michael a asibitin domin gudanar da bincike. Kwamishinan ‘yansandan jihar, ya umurci a tura jami’an tsaro domin kare rayuka da dukiya a yankin, tare da umartar Mataimakin Kwamishinan Sashen Binciken Laifuka da ya fara bincike da kuma kamo wanda ake zargi domin gurfanar da shi a kotu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na...
    Sanata Ali Ndume, mai wakiltar yankin Borno ta Kudu, ya bayyana cewa hare-haren na ƙara ƙamari a yankin abun takaici ne. Ya ce ya samu rahoto tsakanin Hawul da Garkida inda aka ce an kashe ’yan sa-kai sama da 10 a ranar Litinin. A cewarsa, sama da mutane 100 aka kashe cikin wata guda a hare-hare da aka kai Sabon Gari, Izge, Kirawa, Pulka, Damboa, Chibok, Askira Uba da wasu garuruwa da dama. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wakilin falasdinawa a kutun kasa da kasa ta ICJ da ke birnin Haque na kasar Nerthelands yace HKI tana amfani da hana kayakin agaji daga ciki har da abinci shiga gaza a matsayin makami kan Falasdinawa don kashesu. Tashar talabijib ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Ammar Hijazi jakadan kasar Faladinu a cibiyoyin MDD a kasashen Turai yana fadar haka a gaban alkalai a kotun ta ICJ a jiya litinin. Ya ce  HKI tana kisa ta sama da makamai, sannan tana kisa ta kasa da yunwa banda haka tana ci gaba da korar  Falasdinawa daga yankin yamma da kogin Jordan tun fiye da watanni 3 da sua habata. Kutun ta bude wannan zaman ne bisa bukatar MDD ta shekara...
    Ana ci ga ba da zaman dar-dar a kasar Burkina faso, bayan da shugaban kasa mai ci Ibrahim traure ya sake tsallaka rijiya da baya, a wani kokarin juyin mulki wanda bai sami nasara ba a makon da ya gabata. Shafin yanar gizo na labarai ‘Africa News’ya nakalto radiyo Faransa RFI yana fadar cewa an bankado juyin mulkin ne bayan da dukkan bakin da aka gayyata a ranar 22 ga watan Afrilu zuwa wani taro sun kasa halattan taron. Wanda ya nuna shakku kan abinda aka kulla a cikin taron. Labarin ya kara da cewa a cikin yan kwanaki masu zuwa mutanen kasar zasu fito zanga-zanga don nuna goyon bayansu ga shugaban Traore. Har’ila yau ana gudanar da bincike a...
    Shugaban  kungiyar hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’imKasim ya bayyana cewa, kungiyarsa tare da Sojojin kasar da kuma mutanen kasar ne zasu tabbatar da ci gaban kasar Lebanon a wannan halin da ake ciki. Tashar talabijin ta Al-Mayadeen ta nakalto sheikh Na’im kasim yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar a jiya Litinin, jawabinda kafafen yada labarai da damaa suka watsa kai tsaye. Sheikh Qasim kasar Lebanon zata ci gaba da zama mai karfi idan gwamnatin kasar ta dakatar da hare-haren da HKI take  ci gaba da kawowa a kan kasar, da kwato dukkan yankunan kasar da aka mamaye, har’ila yau da kuma ci gaba da hadin kai tsakanin masu gwagwarmaya, sojoji da kuma mutanen kasar. Shugaban kungiyar...
    Wata majiya kuma ta bayyana cewa adadin mutanen da suka mutu na iya fin haka, duba da yawan mata da yara da lamarin ya rutsa da su. A lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomin soji da ‘yansanda ba su fitar da wata sanarwa ba dangane da lamarin ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban Putin Na Rasha Ya Bada Sanarwan Tsagaita Wuta Da Ukraine Na Bangaren Guda kuma na sa’o’ii 72 ko kwanaki 3, daga 8-10 na watan Mayu mai zuwa. Jaridar Daily Trust ta Najeriya nakalto jakadan kasar Rasha a Abuja yana fadar haka a wani taro baje kolin hotinan yaki Rasah da Nazi a dai dai lokacinda kasar take cikar shekaru 80 da samun nasara a kan sojojin Nazi a karshen yakin duniya na II a Abuja. Andrey Podelyshev yace idan kasar Ukraine ta zami da tsagaita wuta a cikin wadannan kwanaki ba laifi, amma kuma idan sojojinta sun kai wani hari a kan rasha ta zata rama da hare-hare masu tsanani. Shugaban Volodimir Zelesky dai tuni ya yi watsi da...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Rahotanni suna nuna cewa farashin shinkafa, ɗaya daga cikin nau’ukan abincin da ’yan Najeriya suka fi ci, ya karye a wasu sassan ƙasar. Sauyin farashin ya sa ana tambayoyi — shin me ya haifar da wannan sauyi? Kuma me hakan ke iya haifarwa a rayuwar talaka? NAJERIYA A YAU: “Dalilin da muke sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki” DAGA LARABA: Dalilan Rashin Wutar Lantarki A Wasu Jihohin Arewa A kan wannan sauyi da dalilansa ne shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari. Domin sauke shirin, latsa nan
      Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi, ya amince da nadin Mai Martaba Sarkin Kazaure, Alhaji Dr Najib Hussaini Adamu, a matsayin Amirul Hajj na Jihar Jigawa, kuma shugaban tawagar Gwamnatin jihar domin gudanar da aikin Hajjin 2025. Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya sanya wa hannu kuma aka raba wa manema labarai. Gwamnan ya kuma amince da nadin mambobin tawagar Amirul Hajjin. Malam Bala Ibrahim ya bayyana cewa, mambobin sun hada da Dr. Yusuf Abdurrahman, Babban Limamin Masarautar Hadejia da Alhaji Lawan Ya’u Roni, Talban Kazaure. Sauran su ne Dr. Mahmoud Yunusa, Sa’in Dutse da kuma Alhaji Adamu Dauda Zakar, Durbin Hadejia. Sanarwar ta bayyana cewa an yi wadannan...
    Shugaban kasar Iran ya nuna murnarsa da yin maraba lalai da masu zuba hannun jari daga kasashen waje a Iran Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana Iran a matsayin dandalin da ta dace wajen zuba hannun jari da gudanar da harkar kasuwanci, yana maraba da masu zuba hannun jari na kasashen waje da ‘yan kasuwa na duniya da su shiga harkokin tattalin arziki da zuba hannun jari a Iran. A yayin bikin bude baje koli karo na bakwai na baje kolin kayayyakin da Iran ke fitarwa zuwa kasashen ketare (Iran Expo 2025) a safiyar yau Litinin, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi maraba da baki na kasashen waje da suka halarci wannan baje kolin, yana mai cewa, “Ko...
    Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Duk wani harin wuce gona da iri kan Iran zai fuskanci mayar da martani daidai da shi cikin gaggawa Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa Iran na da kwarin gwiwa kan iya dakile duk wani yunkuri da wasu bangarorin ke yi na kawo cikas ga manufofinta na ketare. Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araqchi ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa: Rudun gwamnatin yahudawan sahayoniyya, wadda take ganin za ta iya gindaya wa Iran abin da ya kamata ko kuma bai kamata ba, rudun tunani ne da ya yi nesa da hakikanin gaskiya, ta yadda bai cancanci mayar da martani ba. Araqchi ya kara da cewa: “Duk da haka,...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Ci gaba da killace Gaza da kuma kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, laifi ne da ba a taba yin irinsa ba a tarihin dan Adam A wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Masar Badar Abdel Ati a yammacin jiya Lahadin da ta gabata, Araqchi ya bayyana ci gaba da killace yankin Gaza da rashin abinci da magunguna, tare da kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, a matsayin wani laifi da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin dan Adam. Ya dauki Amurka da sauran masu goyon bayan ‘yan sahayoniyya a matsayin masu hannu a kisan kiyashi da laifukan yaki...