An harbe masu garkuwa da mutane 3 a Kebbi
Published: 24th, August 2025 GMT
’Yan sanda sun samu nasarar kashe wasu mutum uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, tare da ƙwato bindigar AK-47 bayan musayar wuta da su a yankin Shanga na Jihar Kebbi.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, CSP Nafiu Abubakar, ya fitar.
Mutum 6 sun rasu yayin tsere wa ’yan bindiga a Sakkwato An tsinci gawar saurayi a gefen kudiddifi a KalabaSanarwar ta bayyana cewa lokacin da lamarin ya faru, DPO na Shanga ya gaggauta haɗa jami’an ‘yan sanda da ‘yan sa-kai waɗanda suka fafata da ‘yan bindigar, inda aka kashe uku daga cikinsu, sauran kuma suka tsere cikin daji.
Kakakin ’yan sandan ya ce wannan nasara na da nasaba da bayanan sirrin da suka tattara cewa wata tawagar masu garkuwa da mutane ta ɓulla a dajin da ke kan hanyar Tungargiwa zuwa Saminaka, suna shirin yin garkuwa da matafiya.
A wani lamari daban, sanarwar ta ce wasu gungun masu garkuwa ɗauke da makamai masu haɗari sun afka garin Kesan a Ƙaramar Hukumar Shanga, inda suka yi garkuwa da wani matashi mai suna Abdulmumini Alhaji Ahmadu, mai shekaru 25.
Shi ma dai bayan samun rahoton ne, DPO na yankin ya tura tawagar jami’an tsaro wadda ta bi sawun masu garkuwan har suka ceto matashin da aka sace.
Sai dai yayin aikin ceton, an harbi matashin a ƙafarsa ta hagu, inda yanzu haka yana samun kulawa a wani asibiti da ke yankin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: garkuwa da mutane Jihar Kebbi masu garkuwa
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jigawa Ta Kara Samar da Shirye-shiryen Inganta Rayuwar Masu Buƙata ta Musamman
Daga Usman Muhammad Zaria
Hukumar kula da masu bukata ta musamman a jihar Jigawa za ta gudanar da aikin gyaran gidajen gajiyayyu na shiyyar Birnin Kudu da Gumel a sabuwar shekara.
Shugaban hukumar, Malam Sale Zakar Kafin Hausa, ya bayyana haka lokacin kare kiyasin kasafin kudin 2026 a gaban kwamatin harkokin mata na majalisar dokokin jihar Jigawa.
Ya ce gidan gajiyayyu na shiyyar Birniwa yana cikin kyakkyawan yanayi da kulawa sosai ta fuskar abinci da sutura da kayan wanka da na wanki da sauran bukatun rayuwa, dan haka gwamnati ta kuduri niyyar gyara sauran gidajen gajiyayyun domin kyautata yanayinsu.
Malam Sale Zakar ya ce an Kara yawan mata masu juna biyu da masu shayarwa da ke amfana da Shirin kula da lafiyar iyali daga 20 zuwa 30 a mazabun jihar 287.
Ya kara da cewa za kuma a kara yawan masu amfana da tallafin masu bukata ta musamman daga 150 zuwa 200 a kowacce karamar hukuma, inda masu bukata ta musamman 540 ke samun tallafin naira 10, 000 a duk wata.
A nasa jawabin shugaban kwamatin harkokin mata na majalisar dokokin jihar Jigawa kuma wakilin mazabar Birnin Kudu Alhaji Muhammad Kabiru Ibrahim ya bayyana gamsuwa da tanade tanaden da aka yiwa mata da yara da tsoffi da marasa galihu da mata masu juna biyu da masu shayarwa da nakasassu.
Ya kuma yi addua’ar Allah Ya sa kasafin kudin ya yi tasiri wajen inganta rayuwar masu karamin karfi da marasa galihu a sabuwar shekara.