✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ISWAP ta kashe manoma sama da 50 a Borno

Har yanzu babu wata sanarwa daga hukumomin tsaro dangane da harin.

Aƙalla manoma 50 ne suka rasu, sakamakon wani mummunan hari da ‘yan ta’addan ISWAP suka kai garin Malam Karanti da ke Ƙaramar Hukumar Kukawa, a jihar Borno.

Majiyoyi sun ce mayaƙan sun afka wa manoma yayin da suke noma da kamun kifi, duk da cewar suna biyan haraji kafin yin noma.

“Sun mallaki takardun izini daga kwamandan ISWAP da ke kula da yankin Malam Karanti har zuwa Dawashi. Sun jima suna samun kariya daga Amir Akilu, wanda shi ne kwamandan yankin,” in ji wani mazaunin yankin.

Sai dai harin ya faru ne a lokacin da kwamandan bai kasance a yankin ba, inda wasu daga cikin mayaƙan suka zargi manoman da leƙen asiri, inda suka ce suna taimaka wa abokan gabansu.

Wannan ne dalilin da ya sa suka kai harin.

Wani wanda ya tsallake rijiya da baya a harin ya ce: “Mun fara girbin wake ne lokacin da suka zo. Sun kewaye mu, suka ce duk wanda ya yi yunƙurin tserewa za su harbe shi.

“Wasu daga cikinmu sun yanke shawarar guduwa duk da hakan. Sun kashe sama da mutum 50, da yawa daga cikinsu an yanka su.

“Sannan sun kama wasu daga cikinmu. Yau ma sun je Dawashi sun kashe mutane, amma ba a san adadin waɗanda suka kashe ba tukuna.”

Gwamnati da hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa dangane da wannan mummunan hari ba.

Wannan hari ya zo cikin watanni biyar kacal bayan wani makamancin sa da aka kai ƙauyen Dumba, inda manoma aƙalla 40 suka rasa rayukansu.