Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ta Sha Alwashin Hukunta Masu Almundahana A Shirin Ciyarwar Azumi
Published: 12th, March 2025 GMT
Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta jaddada kudurin ta na tabbatar da gaskiya da adalci a shirin ciyarwa na azumin watan Ramadan da ke gudana a fadin jihar.
Shugaban kwamitin duba rabon abincin buda baki kuma wakilin mazabar Kiyawa, Alhaji Yahaya Muhammad Andaza, ya bada tabbacin haka lokacin da ya kai ziyarar bazata a wasu cibiyoyin ciyarwar.
A yayin ziyarar, kwamitin ya duba yadda ake gudanar da shirin a kananan hukumomin Birniwa da Kirikasamma da Guri da Hadejia, inda aikin kwamatin ya mayar da hankali ga tantance nasarar shirin da gano matsalolin da ke bukatar gyara.
A karshen ziyarar, Alhaji Yahaya Andaza wanda shi ne mataimakin mai tsawatarwa na majalisar, ya bayyana damuwa kan wasu kura-kurai da aka samu a cibiyar bada abincin buda baki ta garin Birniwa ta Farko, inda aka gano wasu matsaloli na rashin bin cikakken tsarin rabon abincin ga masu azumi.
Sai dai kuma, ya yaba da namijin kokarin wasu daga cikin masu dafa abinci a Kirikasamma da Hadejia, da Kasuwar Kofa, da Guri, inda shirin ke tafiya da yadda yakamata.
Wani matashi mai suna Abubakar Idris da ke kula da cibiya ta biyu a garin Guri ya samu kyakkyawan yabo daga ‘yan kwamitin, bisa tsarin da ya bi, inda a cibiyarsa ake samun dafadukar shinkafa mai kyau, hade da kifi da kwai, ko naman kaza, da kuma rarraba kunu da kosai a kullum ga masu azumi 300.
A cewar Usman Zakar Ayuba, jami’in kula da cibiyar Hadejia, sama da mutane 8,000 ne ake sa ran za su ci moriyar shirin a kullum a karamar hukumar Hadejia kadai.
Yana mai cewar, an kara cibiyoyi guda biyar a kan guda 22 da ke aiki a mazabu 11 na karamar hukumar.
Kazalika, Shugaban kwamatin Alhaji Yahaya Andaza ya bukaci duk masu dafa abincin azumi na Gwamnatin jihar Jigawan da su kasance masu gaskiya da adalci wajen gudanar da ayyukan su, tare da yin la’akari da darajar watan Ramadan ta hanyar tabbatar da cewa mabukata sun ci moriyar shirin yadda ya kamata.
A don haka, ya gargadi duk masu kokarin yin almundahana da kayayyakin abinci da aka tanada, yana mai cewar duk wanda aka samu da laifi na rage adadin kayan abinci kamar mudu 10 na gero don kunu, da mudu 10 na shinkafa don dafa-duka, da mudu 10 na wake don kosai, zai bandana kudarsa.
Radio Nigeria, ya bamu rahoton cewar, sama da naira miliyan dubu 4 ne gwamnatin Jigawa ta ware domin a ciyar da al’ummar musulmi da ke azumtar watan Ramadan a jihar.
Kwamitin ya kuduri aniyar ci gaba da sa ido a kan duk cibiyoyin ciyarwa a fadin jihar, domin tabbatar da cewar shirin yana tafiya yadda ya kamata.
Majalisar Dokokin ta kuma jaddada aniyarta na hukunta duk wanda aka samu da laifin yin almundahana, tare da daukar matakan da za su inganta shirin.
Usman Mohammed Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
NLC a Zamfara sun Bada Wa’adin Kwanaki 14 a Aiwatar da Mafi Karancin Albashi
Kungiyoyin kwadagon Najeriya NLC da TUC a jihar Zamfara sun bayar da wa’adin kwanaki 14 ga gwamnatin jihar, inda suka bukaci da a kawo karshen kura-kuran da aka samu wajen aiwatar da mafi karancin albashi na N70,000.
An sanar da wa’adin ne a wani taron manema labarai a Gusau bayan wani taron gaggawa da kungiyoyin kwadago suka yi.
Da yake jawabi a wajen taron, shugaban kungiyar NLC na jihar Zamfara, Malam Sani Halliru, ya bayyana rashin jituwar da ake samu wajen biyan albashin watan Maris a matsayin abin bakin ciki da damuwa ga ma’aikatan gwamnati.
“Ya zama dole mu kira wannan taron manema labarai saboda mun ji takaicin yadda gwamnatin jihar ke aiwatar da mafi karancin albashi,” in ji Halliru.
Ya kara da cewa tun da farko gwamnatin jihar ta kafa kwamitin da zai sa ido a kan yadda za a aiwatar da sabon albashin tare da tabbatar wa ma’aikata cewa za a fara aiki a watan Maris. Sai dai ya lura cewa albashin watan Maris da aka biya a baya-bayan nan ya gaza yadda ake tsammani.
“Wasu ma’aikata sun samu karin Naira 3,000 kacal, yayin da wasu suka samu N4,000, N5,000, ko kuma akalla Naira 7,000. Har ma fiye da haka, an cire wasu ma’aikatan ba bisa ka’ida ba daga cikin albashin ma’aikata.” Ya kara da cewa.
Malam Sani Haliru ya kuma bayyana lamarin a matsayin cin amana, ya kuma yi gargadin cewa, idan gwamnati ta gaza magance wadannan matsalolin nan da makonni biyu, kungiyoyin za su dauki mataki.
Shi ma da yake jawabi, Shugaban TUC, Sa’idu Mudi, ya koka kan yadda har yanzu Zamfara ce jiha daya tilo da ba ta fara aiwatar da mafi karancin albashi na N70,000.
“Dukkan shugabannin kwadago da ma’aikata a jihar sun ji takaicin gazawar gwamnati wajen cika alkawarin da ta dauka.
A cewar Mudi sun ji takaicin kwamitin da aka nada domin aiwatar da sabon albashin yaki yin aikin da ya dace.
Ya yi zargin cewa da gangan wasu mutane a cikin gwamnati ke yin zagon kasa wajen aiwatar da aikin tare da yin kira ga Gwamna Dauda Lawal da ya kaddamar da bincike kan lamarin tare da daukar matakin da ya dace.
COV/AMINU DALHATU