Nazarin CGTN: Mutane Da Dama A Duniya Sun Yaba Da Salon Shugabancin Gwamnatin Kasar Sin
Published: 9th, March 2025 GMT
A bara, alkaluman tattalin arziki na GDP na kasar Sin sun kai yuan triliyan 134.9, inda aka samu karuwar kaso 5 cikin dari, lamarin da ya sa shi kasancewa tattalin arziki mafi saurin ci gaba cikin kasashen duniya masu karfin tattalin arziki. Ci gaban da ake samu na ingantuwar tattalin arzikin kasar ya haifar da tarin alfanu ga jama’a.
Wani nazari da ya samu amsa daga mutane 25,883 daga kasashe 41 da kafar yada labarai ta CGTN ta gudanar, ya nuna cewa, sama da kaso 80 na wadanda suka bayar da amsa, sun yaba da tsarin ci gaban kasar Sin dake mayar da hankali kan moriyar al’umma, tare kuma da amincewa da ingancin salon shugabancin gwamnatin kasar Sin.
A shekarar 2024, mizanin aikin yi da na farashin kayayyaki sun kasance kan wani mataki mai daidaito, inda aka samar da guraben ayyukan yi miliyan 12.56 a birane, kana kudin shigar kowanne dan kasa ya karu da kaso 5.1. Baya ga haka, an karfafa tsare-tsaren bayar da ilimin tilas da kula da tsoffi da kiwon lafiya da sauran harkokin al’umma.
Ban Ji Dadin Zaman PSG Ba, Messi Manchester United Na Son Lashe Firimiya A Shekarar 2028Cikin nazarin da CGTN ta gudanar, masu bayar da amsa sun yaba matuka da ingancin shugabancin gwamnatin kasar Sin, inda kaso 78.8 suka ce an cimma gagarumar nasara a harkar bayar da ilimi, kaso 70.1 sun yaba da yadda aka samu karuwar kudin shigar jama’a, kaso 63.4 kuma, sun yaba ne da ingantuwar muhallin rayuwa. Haka kuma, kaso 61 sun yaba da ingantuwar tsarin kiwon lafiya yayin da kaso 58.1 suka yaba da ingantuwar yanayin muhallin halittu. Wasu kaso 62.7 kuma sun ce fa’idojin da manufofin Sin ke da su na da muhimmanci wajen bayar da tabbaci ga ingantaccen tsarin shugabanci a kasar.
An samu wadannan alkaluma ne daga nazarce-nazarce biyu da kafar CGTN da jami’ar Renmin ta kasar Sin suka gudanar ta hannun cibiyar bincike kan harkokin kasa da kasa a sabon zamani, inda suka mayar da hankali kan “Yanayin Zama a Kasar Sin” da “Zamanatar da Kasar Sin”. Masu bayar da amsar sun hada da mutanen yankin arewacin Amurka da nahiyar Turai da Afrika da Oceania da kudu maso gabashin Asiya da gabashi da kudu da tsakiyar Asiya da kuma yankin Gabas ta Tsakiya. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: sun yaba da
এছাড়াও পড়ুন:
Wa Ke Dandana Kudar Matakin Harajin Kwastan Da Gwamnatin Amurka Ta Dauka
Tun lokacin da Donald Trump ya hau mukaminsa na shugaban kasar Amurka a watan Janairu na bana, sau da dama gwamnatinsa ta dauki matakan kakaba harajin kwastan kan abokan cinikinta. A ganinsa, matakan za su tilasta kamfanoni da su maido da tsarin samar da kayayyaki zuwa Amurka, matakin da zai gaggauta bunkasuwar masana’antun kasar. Ko abin ya tafi kamar yadda Trump ya yi tsamani?
Alal hakika, manufofi marasa dorewa da gwamnatin Trump ta dauka na illata amanar Amurka, har ma hakan ya yi ta dakushe kwarin gwiwar masu zuba jari na ketare da na kamfanonin cikin gidan kasar. Babban mizanin wasu muhimman hannayen jarin Amurka ya yi matukar raguwa kwanan baya, abin da ya shaida damuwar masu zuba jari a duniya kan rikicin ciniki da tafiyar hawainiya a bangaren bunkasuwar tattalin arziki. Ban da haka kuma, kamfanonin kasar Amurka da kamfanoni masu jarin waje dake kasar za su iya fuskantar hauhawar kudaden kashewa, da katsewar tsarin samar da kayayyaki da dai sauran kalubaloli. A idanun masu zuba jari, Amurka ba ta zama wuri mai inganci na zuba jari a halin yanzu. Ke nan yaya za a kai ga kare masana’antun cikin gidan kasar?
Mun Yi Watsi Da Ayyana Dokar Ta-Ɓaci Da Tinubu Ya Yi A Ribas – Shugabannin Adawa Cikar NUJ Shekaru 70: ‘Yan Jarida Abokan Hulɗa Ne Wajen Aza Kyakkyawar Makoma – Gwamnan GombeBaya ga haka, yanzu al’ummar kasar Amurka na fuskantar hauhawar farashin kayayyaki, har ma bisa nazarin da jami’ar Yale ta yi, an ce ko wane iyalin Amurkawa zai biya karin kudi da yawansa ya kai dala 1600 zuwa 2000 a ko wace shekara, sakamakon karin harajin kwastan da gwamnatin kasar ke bugawa a kan kayayyakin da ake shigar da su daga Mexico, da Canada da Sin.
Kamfanonin dake Amurka da al’ummar kasar, su ne suka fi yin asara karkashin manufar da Trump ya dauka, amma abun tambayar shi ne me ya sa ya yi haka? Kuma wa zai ci gajiyar hakan? (Mai zane da rubutu: MINA)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp