Aminiya:
2025-07-31@17:50:02 GMT

Ramadan: Coci ya ciyar da Musulmi 1,000 a Kaduna

Published: 3rd, March 2025 GMT

Cocin Christ Evangelical & Life Intercessory Ministry da ke yankin Sabon Tasha a Ƙaramar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna, ya raba wa makarantun Islamiyya Musulmi masu ƙaramin ƙarfi akalla 1,000 hatsi albarkacin watan Ramadan.

Shugaban Cocin, Fasto Yohanna Buru, ya ce sun yi haka ne domin yauƙaƙa dangantaka da kuma wanzar da zaman lafiya a tsakanin Musulmi da makwabtansu mabiya wasu addinai a yankin.

Ya ce, “muna mayar da biki ne bisa alherin da Hajiya Ramatu Tijjani, wadda ta tsaya kai da fata wajen rabon shinkafa, kuɗi, da tufafi ga marayu da zawarwan cocinmu a lokacin Kirsimeti da Sabuwar Shekara da kuma Ista.”

Fasto Buru, ya ce cocin janyo irin wannan rabon abinci ga Musulmi a jihohi biyar a tsawon shekaru 19, domin sama musu sauƙi a watan Ramadan.

Ɓacewar bindigogi 4,000: Sakaci ne dalili —’Yan sanda Yadda ’yan bindiga suka sace ɗalibai 4 a Jami’ar Tarayya ta Dutsinma

“Bana mun tsara tallafa wa Musulmi 1,000 kuma mun riga mun tanadi buhunan hatsi domin raba musu,” in ji shi.

Ya buƙaci masu hannu da shuni su taimaka wa mabuƙata, tare da roƙon ’yan kasuwa da su guji tsawwala farashin kayan masarufi a watan Ramadan.

Ya ce fastoci da limamai kimanin 30 sun sadaukar da kansu domin gudanar da gangamin kiran ’yan kasuwa su daina ƙara farashin kayan masarufi a watan Ramadan.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Kayan Masarufi Ramadan watan Ramadan

এছাড়াও পড়ুন:

Nijar da Rasha sun ƙulla yarjejeniyar makamashin nukiliya

Jamhuriyar Nijar da ƙasar Rasha a ranar Litinin, 28 ga watan Yulin 2025 sun ƙulla yarjejeniya game da makamashin nukiliya da kuma haƙar yuraniyom.

Kamfanin dillancin labaran Nijar (ANP) ya ruwaito cewa ƙasashen biyu sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar ce bayan ganawar shugaban Nijar, Janar Abdourahamane Tiani, da wata babbar tawagar Rasha ƙarƙashin jagorancin Ministan Makamashi, Mista Sergei Tsivilev.

Ambaliya ta yi ajalin mutum 30 a China Jami’ar Jihar Gombe za ta fara sabbin darussa 6 a fannin noma

“Muhimmiyar manufarmu ita ce mu ƙara inganta rayuwar mutanen Nijar da na Rasha,” in ji Sergei, kana ya bayyana cewa sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya game da makamashin nukiliya da haƙar yuraniyom.

“Mun amince cewa za mu horar da manyan jami’ai waɗanda za su iya aiki a fannonin tallafinmu irin na makamashi da noma da lafiya da ilimi, kuma za mu horar da injiniyoyi tun a makarantu domin su ci gaba da karatunsu a jami’o’in da ke Tarayyar Rasha,” in ji shi.

Ganawar ta mayar da hankali ne kan dangantaka tsakanin Tarayyar Rasha da Nijar, in ji rahoton na ANP.

Bayan ganawar dai Ministan na Rasha ya bayyana godiyarsa ga shugaba da mutanen Nijar domin irin tarbar da aka yi masa.

“Mun ga bayanai da dama game da damarmakin da ke akwai a cikin Nijar, kuma a halin yanzu mutanenmu na ƙoƙarin aiki kan damarmakin da ke nan a Nijar,” in ji Mista Sergei Tsivilev, wanda shi ne shugaban ɓangaren Rasha a hukumar haɗakar gwamnatoci da ƙasashen AES.

“Shugaban ƙasar ya kuma sanar da mu cewa shi zai zaɓi shugaba na ɓangare ɗaya na hukumar haɗakar gwamnatocin nan ba da jimawa ba domin ayyukanmu da ‘yan uwanmu na Nijar su yi ta tafiya babu tangarɗa,” in ji shi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Faransa Za Ta Fara Jefa Kayan Agaji Ta Sama A Gaza
  • Za a kammala shimfiɗa layin dogo daga Kaduna zuwa Kano a 2026 — Gwamnatin Tarayya
  • Za A Bude Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Koli Na 20 Na JKS A Watan Oktoban bana
  • Gidauniyar ‘Ya’yan Sarakunan Arewa Sun Marawa Sarkin Musulmi A Matsayin Shugaban Majalisar Sarakuna
  • Kwamandan NDA Ya Bukaci Dalibai Su Dage da Karatu a Taron FGC Malali
  • Gwamnan Kaduna Ya Sauke Kwamishinan Yaɗa Labarai, Ya Maye Gurbinsa Da Maiyaki
  • An Kaddamar da Makon MNCH na 2025, Ya Rarraba Fakitin Bayarwa 6,000, Kayan C/S 500
  • Nijar da Rasha sun ƙulla yarjejeniyar makamashin nukiliya
  • Tsohon Ɗan Takarar Mataimakin Gwamnan Kaduna Na PDP Ya Koma ADC
  • An fara shigar da kayan agaji a Gaza