Junbilat: ‘Yan Sahyoniya Suna Son Tarwatsa Kasar Syria
Published: 3rd, March 2025 GMT
Fitaccen dan siyasar kasar Lebanon Walid Junbilat ya bayyana cewa, ‘yan sahayoniya suna son yin amfani da kungiyoyin da ake da su a Syria domin tarwatsa hadin kan kasar.
Walid Junbilat wanda shi ne tsohon shugaban jam’iyyar “ al-takaddumil-Ishtiraki” ya ce zai ziyarci kasar Syria domin ganawa da mahukuntanta akan hatsarin dake tattare da tsoma bakin Isra’ila a cikin harkokin wannan yankin, musamman abinda yae faruwa a kudancin Syria.
Dan siyasar na kasar Lebanon wanda ya yi taron manema labaru a jiya Lahadi ya yi gargadi akan yanayin da ake ciki a yankin “Jabalu-Duruz” da tsoma bakin HKI domin haddasa rashin tsaro a cikin wannan yankin.
Haka nan kuma ya yi tuni da yabo akan tarihin gwgawarmayar ‘yan Duruz’ da yadda su ka tabbatar da zaman Syria a matsayin kasa daya dunkulalliya a karkashin Sultan Pasha Atrash’ yana mai kara da cewa; ‘yan Duruz ba za su taba mika kai ga manufofin Benjamin Netanyahu ba.
Har ila yau ya yi ishara da yadda mafarkin ‘yan sahayoniya yake na fadada ikonsu a ko’ina ba tare da iyaka ba.
Dangane da kudancin Lebanon, Walid Junbilat ya ce abinda yake faruwa mamaya ce, yana mai kara da cewa; Zai ci gaba da adawa da duk wani sulhu da Isra’ila, matukar ba a kafa wa Falasdinawa kasarsu ba.”
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Zaɓen Tanzania: Shugaba Samia Suluhu Hassan ta yi tazarce
Shugaba Samia Suluhu Hassan ta kasar Tanzania ta sake lashe zaɓen shugaban ƙasar mai cike da ruɗani.
Hukumomin zaɓen ƙasar sun sanar da cewa Shugaba Samia Suluhu ta lashe zaɓen ne da kashi 97 na kuri’un da aka jefa.
Hukamar zaɓen ƙasar ta bayyana cewa mutum 31,913,866 ne suka kaɗa kuri’a a zaɓen, wanda ya gudana a yayin da kasar ke fama da ƙazamar zanga-zanga.