Aminiya:
2025-09-18@06:57:25 GMT

Cibiyar bincike ta nemi a tabbatar da dokar kare haƙƙin mata a Arewa

Published: 28th, February 2025 GMT

Cibiyar Bunƙasa Ayyukan Bincike za ta gudanar da gangami domin nazarin dokokin da suka shafi zamantakewar Musulmi a jihohin da ta ke aiki, domin inganta haƙƙoƙin mata da ƙananan yara.

Shugaban tawagar cibiyar, Dokts Taofik Abubakar daga Jami’ar Bayero Kano ne, ya bayyana hakan yayin wata ziyarar girmamawa da suka kai wa Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, a fadarsa da ke Zariya.

Rage Albashi: Abba ya dakatar da muƙaddashin shugaban ma’aikatan Kano NAJERIYA A YAU: Yadda Azumi Ke Inganta Lafiyar Jiki

Dokta Taofik, ya ce sun je fadar ne, domin neman albarka da shawarwari kan hanyoyin magance cin zarafin mata.

Ya kuma bayyana cewa cibiyar ta ɗauki nauyin malamai da limamai zuwa Jami’ar Al-Azhar da ke Masar don ƙaro ilimi kan matsayin Musulunci game da cin zarafin mata.

A cewarsa, cin zarafin mata al’ada ce da aka gada daga tsohuwar ɗabi’a, ba addinin Musulunci ba.

Ya ƙaryata fahimtar da wasu ke da ita cewa Musulunci yana goyon bayan miji ya doki matarsa, inda ya jaddada cewa Annabi Muhammad (SAW), ya haramta hakan.

Cibiyar za ta gudanar da gangamin tattaunawa da shugabannin jihohin Kano da Kaduna domin nazarin dokokin da suka shafi zamantakewar Musulmi, tare da ƙoƙarin tabbatar da su matsayin doka.

A nasa jawabin, Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, ya buƙaci a sake nazarin dokar zamantakewar Musulmi da aka yi watsi da ita a Kano, domin inganta haƙƙoƙin mata a Arewacin Najeriya.

Ya bayyana cewa haƙƙoƙin mata ba su da ƙarfi a tsarin dokokin shari’a na yankin, wanda ke haifar da cikas ga rayuwarsu.

Ya ce idan aka tabbatar da dokar, zai taimaka wajen kare haƙƙin mata da yara a Arewa.

Sarkin ya kuma buƙaci da a gaggauta tabbatar da dokar a jihohin da ake gudanar da aikin, domin ta zama doka da za a bi a duk faɗin Najeriya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Cibiya Sarkin Zazzau yara Zariya tabbatar da

এছাড়াও পড়ুন:

Arewa Ba Zata Ƙarɓi Mulki A 2027 Ba, Gwamna  Bago

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Karamar Hukumar Malam Madori Ta Horar Da Mata Kare Kai Daga Cututtukan Mahaifa
  • Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Sabon Tsarin Kula Da Lafiyar Mata Masu Juna Biyu Da Kananan Yara
  • Tinubu Ya Janye Dokar Ta-baci A Jihar Rivers
  • Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna
  • Gwamnatin Kano Ta Inganta Cibiyoyin Horas Da Sana’o’i Domin Dakile Aikata Laifuka Tsakanin Matasa
  • Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu Kano
  • Kwamitin bincike na MDD ya zargi Isra’ila da aikata “kisan kare dangi” a Gaza
  • Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabala
  • Ƴan Bindiga Sun Kashe Sarkin Shuwaka Na Kanam A Filato
  • Arewa Ba Zata Ƙarɓi Mulki A 2027 Ba, Gwamna  Bago