A gaban mijina Akpabio ya fara neman kwanciya da ni —Sanata Natasha
Published: 28th, February 2025 GMT
Sanata Natasha Akpoti ta zargi Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswil Akpabio da neman yin lalata da ita.
’Yar Majalisar Dattawa daga Jihar Kogi ta bayyana cewa mijinta ma shaida ne a kan yunkurin Akpabio ne yin lalata da ita.
A wata hira da aka yi da ita a tashar talabijin ta Arise a safiyar Juma’a, Sanata Natasha ta ce tun da ta ki amincewa da buƙatar Shugaban Majalisar ya kafa mata ƙahon zuƙa.
A makon da ya gabata ne Natasha ta yinwa Akpabio wankin babban bargo a zauren Majalisar bayan ya sauya mata kujera ba tare da tuntubar ta ba.
Shin Kwankwasiyya ta kama hanyar wargajewa ne? NAJERIYA A YAU: Yadda Azumi Ke Inganta Lafiyar JikiYa ba da umarnin ne bayan da ’yan majalisar suka kada ƙuri’ar amincewa da hakan, domin tabbatar da dokokin zauren Majalisar.
Daga bisani ya tura lamarin ga kwamitin ladabtarwar majalisar ta gudanar da bincike tare da gabatar da rahoto cikin makonni biyu.
Ana cikin haka ne ’yar majalisar ta maka shi a kotu tana neman diyyar Naira biliyan 100.03.
A wata hira da aka yi da ita a tashar talabijin ta Arise a safiyar Juma’a, Sanata ta ce, tana da hujjoji da hotunan saƙonnin da ya aika mata.
’Yar Majalisar ta ce Akpabio ya sha kiran ta ta manhajar WhatsApp, sa’annan ta buƙaci Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta bibiyi wayar da suka yi domin gano gaskiya.
Ta bayyana cewa ta sha neman gabatar da kudiri kan Masana’antar Mulmula Karfe na Ajaokuta a zauren Majalisar amma Akpabio yana kin sanya batun a jerin abubuwan da za a tattauna a majalisar.
Ta ce daga bisani bayan ta nuna damuwarta wasu sanatoci suka bukaci ta je ta yi masa magana saboda muhimmancin masana’antar.
Ta ce, da ta yi masa magana sai ya ce, “Sanata Natsaha, a matsayina ba shugaban majalisar nan, Ni ke da wuƙa da nama. Ya kamata ki ba ni kulawa, domin idan kika kuka da ni za ki samu alherai masu yawa.”
Ta ce, ko da ta bayyana masa cewa ba ta fahimta ba sai ya ce, “ya rage naki.”
Ta ce, “wannan abun da ke faruwa da ni daidai yake da na malamin da ke wahalar da ɗalibarsa saboda ta ƙi kwanciya da shi.”
Ta bayyana cewa tun a shekarar 2023 Akpabio ya fara yi mata wannan mummunan tayi a lokacin da ita da mijinta suka ziyarce shi domin taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarsa.
Ta ce “yana rike da hannuna muna zagayawa yana nuna mana cikin gidansa, mijina na biye da mu, sai ce zai soma ce na zo gidansa mu huta.
“Mijina da ke biye da mu ya ji maganar, saboda haka ya hana mu tafiya ƙasar waje ni kadai ko in yi tafiya da Akpabio shi kadai.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: kwanciya da ita Majalisar Dattawa
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Isra’ila Tana Ci Gaba Da Hana Masu Jinya Zuwa Kasashen Waje Neman Magani Daga Gaza
Gwamnatin mamayar Isra’ila ta yanke hukuncin kisa kan masu fama da cutar kansa da kuma waɗanda suke fama da matsalar koda na mutuwa a Gaza domin hana fitar da su wata kasa don neman magani
Cibiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Gaza ta bayyana matukar damuwarta game da tabarbarewar lafiyar marasa lafiya da ke fama da cutar kansa da kuma cutar koda a Zirin Gaza. Wadannan cututtuka sun kara ta’azzara ne sakamakon hare-haren sojojin mamayar Isra’ila kan Gaza da kuma ci gaba da killace yankin bayan tsagaita bude wuta, gami da hana shigar dq magunguna da kayayyakin ayyukan likitanci masu muhimmanci cikin yankin. Cibiyar ta kuma yi nuni da tsauraran matakan fitar da marasa lafiya zuwa ƙasashen waje don neman magani.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Lahadi, Cibiyar ta tabbatar da cewa, wannan yanayin ba shi da wata shakka cewa Isra’ila na aiwatar da manufar kisan gilla a kan dubban marasa lafiya ta hanyar hana su ‘yancinsu na rayuwa da magani da gangan, da kuma canza wahalarsu zuwa wani nau’in hukunci na gama gari.
Cibiyar ta ambaci majiyoyin lafiya da ke tabbatar da cewa, akwai marasa lafiya 12,500 da ke fama da cutar kansa a Zirin Gaza, ciki har da ƙananan yara. Ta lura cewa mata sun kai kusan kashi 52% na dukkan masu cutar kansa a Gaza.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kasar Qatar Ta Ba Da Tallafin Gaggawa Ga Al’ummar Sudan Bayan Gumurzun El-Fasher November 2, 2025 IAEA : Babu wata shaida da ke nuna cewa Iran na kera makaman nukiliya November 2, 2025 Amurka : zamu dauki matakin soja idan Najeriya ta gaza kawo karshen kashe Kiristoci November 2, 2025 Hamas ta musanta zargin Amurka na cewa tana sace kayan agaji a Gaza November 2, 2025 Wasu Yan Ta’adda Sun Kashe Dakarun Sa Kai 2 A Kudu Maso Gabashin Iran November 2, 2025 Sojojin Amurka Na Kara Fuskantar Venezuwela Adaidai Lokacin da Trump Ke Musanta Batun Kai Hari November 2, 2025 Isra’ila Ta Kashe Mutane 4 Tare Da Jikkata Wasu Guda 3 A Kudancin Labanon November 2, 2025 Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya November 2, 2025 Shugaban AmurkaTrump ya yi barazanar daukar matakin soji kan Najeriya November 2, 2025 Kamaru: Jagroan ‘Yan Hamayya Ya Yi Kira Da A Tsayar Da Harkoki A Fadin kasar November 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci