Hukumar Tsaro Ta Farin Kaya Ta Kama Wasu Mutane 2 Da Yin Sojan Gona
Published: 24th, February 2025 GMT
Hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC) reshen jihar Kano ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da yin sojan gona ga aikin hukumar.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar NSCDC reshen jihar Kano SC Ibrahim Idris Abdullahi ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano.
Ya ce mutanen biyu, Muhammad Sarari da Madaki Zaharaddeen, masu shekaru 43 da 32, mazauna Goron Dutse ne, a karamar hukumar Dala, da Hotoro kwatas a karamar hukumar Nassarawa.
A cewar jami’in hulda da jama’an, wadanda ake zargin suna zuwa hukumomin da ma’aikatun gwamnati ne, inda suke yaudarar manyan ma’aikata tare karbar kudade daga hannunsu.
“Dubunsu ta cika ne a lokacin da suka yi yunkurin tsoratar da wasu manyan ma’aikatan gidan talabijin na jihar, suna neman su basu wasu kudade.” In ji shi.
Jami’an hukumar ta NSCDC reshen Tarauni ne suka kama wadanda ake zargin, inda aka kawo su hedikwatar jihar domin yi musu tambayoyi.
Da aka gudanar da bincike, sun amince da aikata laifin, kuma an sami daya daga cikinsu da katin shaida na bogi da rigar ciki mai dauke da tambarin hukumar NSCDC.
Ya kuma yi nuni da cewa, za a tuhumi wadanda ake zargin ne da laifin shiga harkar aikin gwamnati, da hada baki, da tsoratarwa, da kuma karbar kudi.
Abdullahi ya kara da cewa hukumar NSCDC reshen jihar Kano ta kammala bincikenta, za kuma kuma a kaisu gaban kotu.
Abdullahi Jalaluddeen
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya yabawa Hukumar Makarantun Kimiyya da Fasaha ta Jiha bisa ƙirƙirar Kyautar Malami Mafi Nagarta, yana mai bayyana hakan da ɗaya daga cikin manyan manufofin da za su ƙarfafa koyo da koyarwa a fadin jihar.
A cikin wata sanarwa da Babban Jami’in Yaɗa Labaran sa, Hamisu Mohammed Gumel, ya fitar, gwamnan ya bayyana cewa bikin na farko na bada lambar yabo da aka gudanar a Dutse ya dace domin girmama malamai da suka yi fice ta hanyar jajircewa da sadaukar da kai.
Ya ƙara da cewa wannan mataki zai ƙara kwarin gwiwa, ya samar da gasa mai kyau, tare da inganta darussa a makarantu.
Namadi ya jaddada cewa ingancin ilimi bai tsaya kan gina makarantu kawai ba, yana ta’allaka ne ga ingancin malamai, kayan koyarwa da kuma yanayin makarantu.
Ya bayyana cewa gwamnatinsa ta fara ɗaukar malamai tare da horas da su akai-akai domin rage cunkoson ɗalibai da malamai da kuma horar da su sabbin dabarun koyarwa.
“Wannan shiri ɗaya ne daga cikin mafi kyawu da muka gani. Idan wani ya yi kuskure, sai a hukunta shi, yayin da duk wanda ya yi fice, wajibi ne a yaba masa. Wannan shi ne yadda ake samun cigaba,” in ji gwamnan.
Ya bukaci sauran hukumomin ilimi kamar Hukumar Gudanar da Makarantun Sakandare, Hukumar Ilimin Addinin Musulunci, da Ma’aikatar Ilimin Firamare su yi koyi da wannan tsari domin ƙara ƙarfafa gwanintar malamai a dukkan matakai.
Gwamnan ya kuma sake jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da maida hankali wajen gina makarantu, horar da malamai, da walwalar su.
Ya tabbatar da cewa za a ci gaba da baiwa bangaren ilimi goyon baya don inganta sakamakon koyo a makarantu a fadin Jihar Jigawa.
Usman Muhammad Zaria