Aminiya:
2025-11-02@14:11:18 GMT

Me kuka sani game da ficewar Mali, Nijar, da Burkina Faso daga ECOWAS?

Published: 29th, January 2025 GMT

Kungiyar bunƙasa tattalin arzikin ƙasashen Yammacin Afirka ta ECOWAS ta tabbatar da ficewar ƙasashen Burkina Faso, Mali da kuma Nijar a hukumance.

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da ECOWAS ɗin ta fitar, tana mai cewa har yanzu ƙofa a buɗe take ga waɗannan ƙasashe, a duk lokacin da suka sauya shawarar sake komawa.

Mun kama mutum 46 da miyagun ƙwayoyi a Yobe — NDLEA Kiristoci sun yi addu’ar ɗorewar zaman lafiya a Kudancin Kaduna

A cikin sanarwar, ECOWAS ta ce za a ci gaba da mutunta fasfon jama’ar waɗannan ƙasashen uku da ke ɗauke da tambarin ECOWAS, haɗi da katinsu na shaidar ɗan kasa.

Kazalika, ƙungiyar ta ce za a ci gaba da kallon waɗannan ƙasashe tamkar mambobinta, har ma ta bayyana a cikin sanarwar cewa, harkokin kasuwanci tsakanin ƙasashe mambobin ECOWAS da kuma ƙasashen Nijar, Burkina Faso da kuma Mali za su ci gaba da tafiya kamar yadda suke a baya.

Sanarwar ta kuma buƙaci kasashen ƙungiyar, da su ci gaba da ba wa jama’ar ƙasashen uku damar shiga ƙasashensu ba tare da takardar izinin shiga ba, da kuma zama, har sai baba ta gani.

Kungiyar ta ce an fitar da wannan sanarwa ne, domin kaucewa haifar da zaman tankiya ko kuma dardar tsakanin jama’ar waɗannan ƙasashen uku, musamman ”yan kasuwa, da kuma kwantar musu da hankula.

Mun yi duk mai yiwuwa don ganin hakan ba ta faru ba — Nijeriya

Gwamnatin Najeriya ta ce ta yi duk abin da ya dace don ta dakatar da Jamhuriyar Nijar, Mali da Burkina Faso daga ficewa daga ƙungiyar ECOWAS amma duk yunƙurin ta ya ci tura.

Bayanan na gwamnatin Nijeriya ta bakin Ministan Harkokin wajen kasar Yusuf Tugga, na zuwa ne a ƙarshen wa’adin ficewar ƙasashen a watan nan na Janairu duk da cewa ECOWAS ta ƙara musu wa’adi watanni shida.

Kazalika, ƙasashen uku sun ƙaddamar da matakin buga sabon fasfo don jingine amfani da na ECOWAS da yake ba ‘yan kasashen kungiyar damar zirga-zirga ba shamaki.

Muryar Amurka ta ruwaito Ministan yana cewa sun ɗauki duk matakan ‘yan uwantaka da diflomasiyya don jan hankalin ƙasashen su zauna da dangi amma ba sakamako mai karfafa guiwa.

“Ba irin ƙoƙarin da ba a yi. Ni ɗin nan na yi yunƙuri ba sau ɗaya ba sau biyu ba, in tashi in je ko kuma mu ce mun gaiyace su, su ki zuwa,” inji Yususf Tugga.

Duk da su na ƙarƙashin mulkin soja, Yusuf Tugga ya ce an yi wa ƙasashen tayin kuɗin tallafin tsaro da kayan aiki don a nuna musu cewa ana tare da su, duk da tankiyar da ke tsakanin su da uwar ƙungiya ECOWAS.

Dangane da zargin da Nijar ta yi kan cewa Nijeriya tana haɗa kai da Faransa don birkita Nijar, Tugga ya ce zargin ya ba Gwamnatin Nijeriya mamaki kuma ba shi da tushe balle makama.

Mali, Nijar da Burkina Faso sun zama ƙawaye

A ranar ta 29 ga watan Janairun 2024 ne ƙasashen guda uku da shugabannin mulkin soji ke jagoranta suka sanar da ƙungiyar ECOWAS a hukumance dangane da buƙatar ficewar tasu.

Yanzu dai ƙasashen na Burkina Faso da Mali da Nijar sun zama ƙawaye inda suka cure wuri guda ƙarƙashin ƙungiyar da suke kira Haɗakar Ƙasashen Sahel (Alliance of Sahel States (AES).

Shugabannin mulkin sojin ƙasashen dai sun zargi ECOWAS da ƙaƙaba musu takunkumi na “rashin imani kuma haramtattu” bayan juyin mulkin da ya kawo su kan karaga.

Sun kuma yi amannar cewa ƙungiyar ta Afirka ta Yamma ba ta ba su cikakkiyar gudunmawa ba wajen yaƙar ’yan ta’adda. Sun kuma yi amannar cewa ECOWAS ɗin ’yar kanzagin tsohuwar uwar gijiyarsu ce wato Faransa.

Faransa ta kasance abokiyar hamayyar wannan ƙasashen da sojoji ke jagoranci da a yanzu haka suka gwammace yin hulɗa da ƙasashe irin su Rasha da Turkiyya da Iran.

‘Ficewar ƙasashen zai yi wa ECOWAS illa’

Ƙasashen uku za su fito da nasu fasfo a ranar Larabar kuma sun sanar da samar da rundunar sojin haɗin gwiwa guda 5,000 da za su yaƙi masu iƙirarin jihadi a yankin nan ba da jimawa ba.

Ficewar ƙasashen guda uku za ta yi wa Ecowas “illa musamman ta fuskar rikicin siyasa a yankin” kamar yadda Gilles Yabi, shugaban ƙungiyar Wathi ta ƙwararru a Afirka ta Yamma, ya shaida wa AFP.

“Haɗakar ƙasashen guda uku na yankin Sahel, AES da wasu ƙasashen ECOWAS na zaman tankiya.

“Misali Nijar ta ƙi amincewa ta buɗe iyakokinta ga jamhuriyar Benin wadda take zargi da bai wa ’yan ta’adda mafaka inda suke yin atisaye. Ta kuma zargi Nijeriya da kasancewa wani “filin daga na bayan gida” da ka iya yi mata illa.”

Dukkanin ƙasashen biyu na Benin da Nijeriya sun musanta zarge-zargen maƙwabciyar tasu.

 

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: ECOWAS Nijar Nijeriya ficewar ƙasashen ar ƙasashen

এছাড়াও পড়ুন:

Kisan Kiristoci: Za mu kai hari Najeriya — Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar amfani da ƙarfin soji kan Najeriya matuƙar gwamnatin ƙasar ba ta dakatar da kisan da ’yan ta’adda masu iƙirarin jihadi ke yi wa Kiristoci ba.

A yammacin jiya Asabar ne Trump ya umarci Ma’aikatar Yaƙin Amurka ta Pentagon da ta soma tsara yadda za a kai hari Nijeriya bayan da ya yi zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a ƙasar.

Cikin wani saƙo da ya wallafa  a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce Amurka a shirye ta ke ta aike da sojoji da manyan makamai cikin Najeriya don bai wa Kiristocin kariya.

Barazanar shugaban na Amurka na zuwa ne kwana guda bayan ya yi iƙirarin cewa an kashe Kiristoci aƙalla 3,100 a Nijeriya ba tare da ya bayyana takamaimai inda ya samu waɗannan alƙaluma ba.

“Muddin gwamnatin Nijeriya ta ci gaba da bari ana kashe Kiristoci, Amurka za ta dakatar da dukkan tallafin da take bai wa Nijeriya nan-take, kuma mai yiwuwa za ta shiga wannan ƙasƙantacciyar ƙasar, cike da ƙarfin gwiwa domin kawar da ’yan ta’adda masu kaifin kishin Musulunci waɗanda ke yin wannan ta’asa,” in ji Trump.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu zai gana da Trump kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya 
  • Jamus ta shiga sahun ƙasashen da ke neman kawo ƙarshen yaƙin Sudan
  • Kisan Kiristoci: Za mu kai hari Najeriya — Trump
  •  Gaza: Daga Tsagaita Wuta Zuwa Yanzu Fiye Da Mutane 200 Ne Su Ka Yi Shahada
  • Zargin Kisan Kiristoci: Maganar Trump a kan Najeriya tsagwaron ƙarya ce — Shehu Sani
  • Kwamitin Tsaron MDD ya goyi bayan shirin Morocco game da yankin Yammacin Sahara
  • Amurka ta sanya Najeriya cikin ƙasashen da ake yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi
  • M D Duniya Tayi Gargadi Game Da Gwajin Nukiliya Da Amurka Ta Sanar Za ta yi
  • NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa
  • Borno ta fara fitar da kayan robobi zuwa ƙasashen waje – Zulum