An tsare mutane shida a gidan yari saboda karya dokar kare muhalli ta Taraba.
Published: 26th, January 2025 GMT
Shugaban kotun tafi da gidanka na jihar Taraba, Useni Galadima, ya tasa keyar wasu mutane shida gidan yari bisa samunsa da laifin karya dokar zartarwa mai lamba biyar, 2023, wanda gwamna Agbu Kefas ya bayar.
Wanda ake zargin, Suleiman Musa mai shekaru 30, daga Jos, jihar Filato; Adamu Umar mai shekaru 40 daga Bauchi, jihar Bauchi; Usman Umar Danburam, 35, daga Darazo, Jihar Bauchi; Ibrahim Abdullahi, mai shekaru 50, daga Mina, Jihar Neja; Aminu Mohammed, 40; da Adamu Abdul’aziz mai shekaru 46 daga jihar Taraba, an kama su ne a ranar 17 ga watan Janairun 2025.
An same su dauke da kayayyaki dama da kuma wasu duwatse ake zargin masu daraja ne a wani sansani hakar ma’adinai dake Karamar hukumar Gashaka dake jihar Taraba.
Useni Galadima ya ce ikirari na wadanda ake tuhuma da kuma abubuwan da aka gabatar sun isa a gurfanar da su gaban kuliya.
Babban lauya mai shigar da kara, Barista Neirus Johnson, ya bukaci kotun da ta kwace kayayyakin tare da zartar da hukunci kamar yadda doka ta tanada.
An dage sauraron karar zuwa ranar 27 ga watan Junairu, 2025, domin ci gaba da wannan shari’a.
KARSHE/JAMILA ABBA/Wababe
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Makafi 37 Sun Zana Jarabawar JAMB A Bauchi
Gwamnatin tarayya ta ɗauki nauyin dukkanin buƙatun ɗaliban na zana jarabawar, ciki har da abinci da wurin kwana, har na tsawon kwanaki uku. Kwamishinan ilimi na jihar Bauchi, Dakta Lawal Mohammed Rimin Zayam, ya yaba da wannan mataki na JAMB, yana mai kira ga iyaye da su tura ‘ya’yansu dake da lalura ta musamman makaranta domin samun ilimi.
Kwamishinan ya kuma yi kira ga al’umma da iyaye su fahimci muhimmancin ilimi, musamman ga yara masu naƙasa, yana mai cewa gwamnati za ta ci gaba da wayar da kan iyaye don ganin suna tura ‘ya’yansu makaranta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp