Aminiya:
2025-07-31@16:41:35 GMT

Shigo da hatsi daga ƙetare ya karya farashinsa a Neja

Published: 8th, February 2025 GMT

Kasuwannin hatsi a Jihar Neja suna fama da matsalar faduwar farashi amfanin gona, sakamakon shigo da hatsi daga kasashen makwabta kamar Chadi da Ghana da Jamhuriyar Benin da Burkina Faso.

Wannan yanayi ya haifar da yawan kaya, wanda ke shafar manoma da ‘yan kasuwa da masu samar da kayayyaki a yankin.

Ya yi wa kansa keji don daina shan sigari Amurka ta dakatar da bai wa Afirka ta Kudu tallafi

Manoman da suka tara hatsi don cin riba sun shiga damuwa saboda shaguna da kasuwanni sun cika da buhunhunan hatsi, amma babu masaya.

Wasu daga cikin manoma da ’yan kasuwa sun bayyana wa wakilinmu cewa, wannan yanayi ya rikitar da harkar kasuwanci, inda suke fama da karancin riba saboda farashin hatsi da sauran kayan gona irin su wake da waken soya da dawa da masara da gero na ci gaba da sauka warwas.

Wannan matsalar ta samo asali ne daga yadda wasu kamfanonin sarrafa abinci a Nijeriya ke siyan hatsi daga kasashen makwabta saboda farashi mai rahusa.

Amfanin gona ya yi kyau a wadannan kasashe, manoman suna da damar siyar da hatsinsu ga kamfanoni a Nijeriya a farashin da ya fi araha.

Wani dan kasuwa daga Minna ya koka da cewa, “mun yi tsammanin farashi zai tashi, muka tara hatsi don mu siyar a farashi mai tsada daga baya.

Sai dai shigowar hatsi daga kasashen waje kwatsam ya sa ba za mu iya siyar da kayayyakinmu ba tare da asara ba.”

Masu tara hatsi sun bayyana damuwarsu kan wannan sauyin farashi, inda wasu suka ce shagunan da suka cika da hatsi ba sa samun masu siye.

Idan wannan hali ya ci gaba, ‘yan kasuwa da dama da ke fatan samun riba daga tara hatsi na iya gamuwa da babbar asara.

A gefe guda, masu saye suna jin dadi saboda saukar farashin, amma manoma na korafin cewa wannan raguwar farashi barazana ce ga rayuwarsu da sana’arsu.

Shugaban Kungiyar Manoma da Masu Samar da Hatsi ta Nijeriya, reshen Karamar Hukumar Shiroro, Hassan Ango Abdullahi, ya tabbatar da wannan hali yayin wata tattaunawa a kasuwar Gwada.

Ya ce, “kamfanoni sun fi son siyan hatsi daga Chadi da Ghana da sauran kasashen waje saboda farashinsu yana da sauki.

“Misali, mun sayi wake da waken soya kan farashin Naira 103,000 da Naira 105,000 a kan kowane buhu mai nauyin kilo 100 lokacin girbi, amma yanzu farashin ya sauka zuwa Naira 80,000.

“Masu tara hatsi da suka saya a farashi mai tsada suna cikin wahala yanzu.”

Ya kara da cewa “Shekarar da ta gabata, kamfanoni suna ta siyan masara daga hannunmu, amma wannan shekarar sun daina siyan kayayyaki daga Nijeriya gaba ɗaya saboda sun fi samun rahusa daga kasashen makwabta.

“Muna da buhunan masara masu yawa a ajiye, amma babu masu saye.”

Abdullahi ya yi kira ga gwamnatocin tarayya da na jihohi da su tallafa wa manoma ta hanyar samar da kayan aikin gona masu saukin farashi, irin su taki da sinadaran kashe kwari da injunan noma, domin bunkasa harkar noma.

Ya ce, idan gwamnati ta tallafa wa manoma, farashin abinci zai ci gaba da yin kasa, kuma kowa zai amfana.

Ya kuma bukaci Gwamnatin Jihar Neja da ta samar da wuraren siyar da taki a kowane yanki domin saukaka wa manoma daga karkara.

Ya ce, “ba daidai ba ne manoma daga karkara su yi doguwar tafiya zuwa Minna don sayan taki.

“Ya kamata a samar da wuraren sayar da taki a kowace mazaba.”

A daya bangaren, wasu ba su yarda cewa wannan matsalar raguwar farashi ta yi illa ba.

Sani Usman, Sakataren Kungiyar Manoma da Masu Samar da Hatsi ta Amana, reshen Karamar Hukumar Shiroro, ya ce, “manoma ba sa samun asara. Ko da taki yana kan farashin Naira 40,000 kowane buhu, masara ana sayar da ita a kan Naira 52,000, yayin da waken soya yake kan Naira 80,000.

“Idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, lokacin da masara take kan Naira 30,000 a kan kowane buhu.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Jihar Neja Ƙetare

এছাড়াও পড়ুন:

Kananan Yan Wasan Dabben Gargajiya Na Iran Sun Zama Zakara A Gasar Wannan Shekara

Tawagar kananan yan wasan damben gargajiya na kasar Iran sun zama zakara a wasannin da aka gudanar a na wannan shekara ta 2025 tare da Zinari guda, azurfa guda da kuma Tagullah 4.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jami’an gasar wasan na damben gargajiya na kasar Iaran suna fadar haka a birnin Athen na kasar Girka. Sun kuma kara da cewa tawagar yan wasan zun zama zakara a wannan gasar ne duk da cewa mutum guda daga cikinsu bai shaga wasan ba.

Labarin ya kara da cewa matasan kasar Iran sun kware a wammam wasan gargajiya, wanda ake kiransa damben Roma.

Tawagar ta sami, zinari 1, azurfa 1 da Tagulla 4 , ta kuma sami maki 125 wanda shi ne sama a kan sauran wadanda suka shiga gasar. Kuma Aboufazl Shiri bai sami samar zuwa gasar ba saboda gwamnatin kasar garka ta hana shi Visar shiga kasar.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Canada Zata Amince Da Samuwar Kasar Falasdinu A Taron MDD July 31, 2025  Shugaban Kasar Lebanon Aun Ya Ce Mun Aike Wa  Amurka Sakwanni Akan Dakatar Da Hare-haren HKI July 31, 2025  Sojojin Mamaya Suna Ci Gaba Da Kisan Kiyashi A Gaza July 31, 2025 Kassim: Duk Wanda Yake Neman Hizbullah Ta Ajiye Makamanta Yana Yi Wa Isra’ila Aiki July 31, 2025 Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Yi Allah Wadai Da Takunkumin Da Amurka Ta Kakaba Mata July 31, 2025 Tawagar Iran Ta Fice A Taron Majalisun Dokokin Kasashen Duniya A Lokacin Jawabin Wakilin Isra’ila July 31, 2025 Kasar Iran Ta Bayyana Gushewar Hasashen Raunin Karfin Sojinta Kuma Ba Zai Dawo Ba July 31, 2025 Sojan Amurka Ya Bada Ruwayar Yadda Sojojin Sahayoniyya Suka Kashe Wani Yaro Balasdine July 31, 2025 Sojojin Yemen Sun Kai Zafafan Hare-Hare Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Guda Uku   July 31, 2025 Qolibaf: Barin HKI Ta Yi Abinda Taga Dama Ne Yana Karfafa Mata Giwa July 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kananan Yan Wasan Dabben Gargajiya Na Iran Sun Zama Zakara A Gasar Wannan Shekara
  • Gwamna Namadi Ya Kaddamar da Tallafin Miliyoyin Naira Ga Ƴan NURTW da Mahauta a Jigawa
  • Ma’aikatar Bunƙasa Harkar Kiwo Za Ta Taimaka Wajen Magance Rikicin Manoma Da Makiyaya — Jega
  • Shugabannin Arewa Sun Tattauna Sabon Hanyar Ci Gaba – Minista Uba Maigari Ya Yaba
  • An shawarci Manoman Kwara Da Su Yi Taka-Tsan-Tsan Saboda Hasashen Ruwa Da Tsawa A Jihar
  • Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 45 A Jihar Neja
  • Remi Tinubu ta bai wa waɗanda harin Benuwe ya shafa tallafin Naira biliyan ɗaya
  • Remi Tinubu ta ba da tallafin Naira biliyan ɗaya ga waɗanda harin Benuwe ya shafa
  • An kashe ’yan ta’adda 45 a Neja
  • Gwamna Namadi Ya Biya Sama Da Naira Biliyan Daya Ga Tsofaffin Ma’aikata