Dakarun “IRGC” Sun Bayyana Cewa: Takunkumin Da Turai Ta Kakaba Kan Iran Daukan Fansa Kan Al’ummar Kasar
Published: 3rd, September 2025 GMT
Dakarun kare juyin juya halin Musulunci sun bayyana cewa: Takunkumin kasashen yammacin Turai kan Iran wani yunkuri ne na daukar fansa kan tsayin dakan al’ummar Iran
Kakakin dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Ali Muhammad Na’eini ya tabbatar da cewa: Amurka da kasashen Turai na neman daukar fansa a yakin kwanaki 12 da suka yi da al’ummar Iran mai girma ta hanyar mayar da takunkumi kanta.
Na’eini ya bayyana cewa, dogaron da makiya suke da shi a kan lissafi na son abin duniya kawai ya sanya su jahilci hakikanin bangarori na karfin Iran kamar al’adun tsayin daka, ruhin jihadi da shahada, jagoranci mai hikima, imani na addini, nasarar Ubangiji, da hadin kan kasa.
Na’eini ya zayyana misalan wadannan kura-kurai, yana mai cewa: Shugaban Amurka Donald Trump ya sanya Iran a tsakanin yaki da tattaunawa don tilasta mata mika wuya, yayin da Netanyahu, fira ministan gwamnatin yahudawan sahayoniyya ya yi ikirarin cewa, za a yi galaba a kan Iran cikin sa’o’i 24, har ma ya yi magana kan ficewa daga birnin Tehran.
Na’eini aa kara da cewa: Makiya sun kaddamar da yaki na wanzuwa a kan kasar Iran ta hanyar shirya wani faffadan yakin hadin gwiwa mai sarkakiya da kuma tattara dukkanin sojojin kasashen yammacin duniya, to sai dai martanin Iran ya rusa dukkanin lissafinsu da suka yi, kuma makiya sun yi tunanin cewa kashe manyan jagorori zai kai ga rugujewar tsarin shugabancin Iran, amma akasin haka ya faru.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Qalibaf: Ya Bukaci Gwamnatocin Kasashen Musulmi Su Fito Su Yi Allah Wadai Da Ayyukan Isra’ila A Gaza September 3, 2025 Zaftarewar Kasa Ta Kashe Al’ummar Kauye Gaba Daya Sai Mutum Guda Da Ya Tsira September 3, 2025 Iran Ta Shiga Cikin Tsirarun Kasashen Masu Fasahar Gina Kataparen Motocin Dakon Ma’adinai September 3, 2025 Iran Ta Yabawa Dan Majalisar Dokokin Kasar Irish Kan Yin Tir Da Laifukan Isra’ila September 3, 2025 IRIB, Sashen Kasashen Waje Ta Yi Tir Da Kissan Mai Daukan Hotuna Tashar ‘Al-Alam’ September 3, 2025 Qalibaf: Iran Zata Maida Martani Na Bai Daya Kan “Snapback” Nan Ba Da Dadewa Ba September 3, 2025 Larijani: Kofar tattaunawa da Amurka a bude take September 3, 2025 Habasha da Dangote sun rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa ta dala biliyan 2.5 September 3, 2025 Jami’an Iran sun yaba da nasarorin da aka samu a yayin halartar Pezeshkian a taron SCO September 3, 2025 Sojojin Yemen sun kai hare-hare a kan babbar hedikwatar tsaro ta Isra’ila September 3, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Pezeshkian: Ta’addancin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Kan Kasar Qatar Zalunci Ne Ga Diflomasiyya
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Ta’addancin yahudawan sahayoniyya kan Qatar zalunci ne ga diflomasiyya
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Harin wuce gona da iri kan kasar Qatar, wani hari ne da kungiyar yahudawan sahayoniyya ta shirya kai wa, da nufin dakile yunkurin diflomasiyya na kawo karshen kisan kiyashin da ake yi a Gaza.
Shugaba Pezeshkian ya bayyana hakan ne a jiya Litinin a yayin taron gaggawa na shugabannin kasashen kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC da kungiyar hadin kan kasashen Larabawa dangane da harin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai kan Qatar.
Shugaban ya kara da cewa, wannan cin zarafi na diflomasiyya ya wuce matsayin laifi kawai; ya zama sanarwar aikin rashin kunya da ya zama a yanzu rundunar soji ita ce mai yanke hukunci, ba doka ba.”
Ya ci gaba da cewa, “Abin takaici, ‘yan ta’adda a Tel Aviv sun kara jajircewa da dogewa, inda suka samu kariya daga irin wannan cin amanar diflomasiyya ta hanyar kai wani kazamin yaki kan al’ummar kasar Iran.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Baqa’i: Kowace Kasa A Duniya Tana Da Hakkin Mallakar Makamashin Nukiliya Na Zaman Lafiya September 16, 2025 Kungiyar Human Rights Watch; Isra’ila Ta Kashe ‘Yan Jarida Fiye Da 30 A Kasar Yemen Ne Da Gangan September 16, 2025 Kungiyar Kare Hakkokin Bil’Adama Ta Siriya Ta Bankado Karin Fararen Hula Da Aka Kashe A Rikicin Suweida September 16, 2025 Tawagar Yan Wasan Damben Gargajiya Ta Iran Ta Zama Zakara A Damben Ta Duniya September 16, 2025 An Fara Taron Hukumar Makamashin Nukliya Ta Duniya IAEA Karo Na 69 A Birnin Vienna September 16, 2025 Espania Ta Soke Cinikin Makamai Na EUR Miliyon 700 Da HKI Saboda Kissan Kiyashi A Gaza September 16, 2025 Makaman ‘Drons’ Na Yemen Sun Fada Kan Wurare Masu Muhimmanci A HKI September 16, 2025 Taron Doha: Daga matakin Allawadai zuwa matakan kalubalantar laifukan Isra’ila September 16, 2025 Ministan Tsaron Venezuela Ya Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Juyin Mulki A Kasar September 16, 2025 Pezeshkian: Ya kamata kasashen musulmi su yanke alaka da gwamnatin sahyoniya September 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci