Simon Ekpa: An ɗaure ɗan Nijeriya kan laifin ta’addanci a Finland
Published: 1st, September 2025 GMT
Wata kotu a ƙasar Finland ta yanke wa ɗan Najeriya mai rajin ɓallewar ƙasar Biyafara, Simon Ekpa, hukuncin ɗaurin shekara shida a gidan yari bisa laifukan da suka shafi ta’addanci, zamba da karya doka.
Kotun ta tabbatar da cewa Ekpa ya aikata laifuka da suka haɗa da ƙoƙarin hargitsa jama’a da nufin ta’addanci da kuma shiga cikin ayyukan ƙungiyoyin masu ɗaukar makami.
Haka kuma, kotun ta ce an same shi da laifin zamba ta haraji da keta wasu dokokin Finland.
A cewar kotun, daga watan Agusta 2021 zuwa Nuwamba 2024, Ekpa ya yi amfani da kafafen sada zumunta wajen yaɗa shirye-shiryen neman ɓallewar Biyafara daga Najeriya, da kuma ingiza mabiyansa su aikata laifuka.
Rahoton kotun ya ce ƙungiyoyin da yake jagoranta sun kafa wasu tsageru masu ɗaukar makami, waɗanda aka bayyana a matsayin ƙungiyoyin ta’addanci. Har ila yau, an tabbatar da cewa ya samar musu da makamai, harsasai da abubuwa masu fashewa ta hannun wasu mabiyansa.
An ce duk waɗannan ayyukan Ekpa ya ke gudanarwa ne daga garin Lahti na ƙasar Finland, duk da cewa shi ya musanta zarge-zargen a kotu.
Sai dai alƙalin ya bayyana cewa hukuncin ba shi ne na ƙarshe ba, inda ake tsammanin Ekpa zai iya ɗaukaka ƙara zuwa kotu mafi girma.
Martanin Gwamnatin NajeriyaBayan yanke hukuncin, Gwamnatin Tarayya ta bayyana jin daɗinta, tana mai cewa wannan hukunci “babban lamari ne” wajen tabbatar da adalci da kuma ƙarfafa dangantaka tsakanin Najeriya da Finland.
A wata sanarwa da Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya fitar a ranar Litinin, ya ce: “Tsawon wasu shekaru wutar da Ekpa ya rura ta haddasa bala’i kan rayukan ɗaruruwan ‘yan Najeriya.
“Iyalai sun tarwatse, kasuwanci sun lalace, yara sun zama marayu, al’umma kuma sun riƙa rayuwa cikin tsoro.
“Saboda haka wannan hukuncin ya tabbatar da matsayar da Najeriya ta riƙa, tare da nuna wa masu tsattsauran ra’ayi cewa duniya na kallonsu, kuma doka za ta cim musu.”
Ya ƙara da cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu za ta ci gaba da kare mutuncin Najeriya da ɗaukakar ‘yan ƙasa ta kowace fuska—ta hanyar diflomasiyya, soja, shari’a da sauran hanyoyin da suka dace.
Ministan ya kuma yi kira ga duk wanda ya bi hanyar Ekpa ko sauran masu tayar da zaune tsaye su ajiye makami ya rungumi zaman lafiya, yana mai cewa: “Najeriya ƙasa ce mai faɗi, kuma za ta iya ɗaukar kowa, amma ba a samun ci gaba a kowace al’umma da ke fuskantar tashin hankali da rarrabuwar kawuna.”
A ƙarshe, gwamnatin ta gode wa ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, rundunar soji, ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro, bisa jajircewa wajen kare ƙasar daga duk wani ƙalubale.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Biyafara tabbatar da
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa
A cewarsa, ta hanyar wadannan shirye-shirye, kasar Sin ta nuna goyon baya mai dorewa ga kasashe masu tasowa kuma tana ba da gudummawa mai ma’ana ga ci gaban duniya a karkashin tsarin hadin gwiwar kasashe masu tasowa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA