NAJERIYA A YAU: Me Sakamakon Zaben Ribas Ke Nunawa Game Da Sulhun Wike Da Fubara?
Published: 1st, September 2025 GMT
Yadda Gwamnan Jihar Ribas da aka dakatar, Siminalayi Fubara, da magoya bayansa suka kaurace wa zaben kananan hukumomin jihar, da yadda APC ta lashe kujeru 20 a cikin 23 sun haifar da muhawara a tsakanin ’yan Najeriya.
Shin wannan sakamako alama ce ta yarjejeniyar sulhu da aka cimma a tsakanin Gwamna Fubara da Minsitan Abuja Nyesom Wike a Fadar SHugaban Kasa?
NAJERIYA A YAU: “Abin Da Ya Sa Muka Dawo Daga Rakiyar Kirifto” DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son HaihuwaAmsar wannan tambaya shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci za iyi yunkurin bicikowa.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Ribas siminilaye Fubara
এছাড়াও পড়ুন:
Kisan Kiristoci: Za mu kai hari Najeriya — Trump
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar amfani da ƙarfin soji kan Najeriya matuƙar gwamnatin ƙasar ba ta dakatar da kisan da ’yan ta’adda masu iƙirarin jihadi ke yi wa Kiristoci ba.
A yammacin jiya Asabar ne Trump ya umarci Ma’aikatar Yaƙin Amurka ta Pentagon da ta soma tsara yadda za a kai hari Nijeriya bayan da ya yi zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a ƙasar.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce Amurka a shirye ta ke ta aike da sojoji da manyan makamai cikin Najeriya don bai wa Kiristocin kariya.
Barazanar shugaban na Amurka na zuwa ne kwana guda bayan ya yi iƙirarin cewa an kashe Kiristoci aƙalla 3,100 a Nijeriya ba tare da ya bayyana takamaimai inda ya samu waɗannan alƙaluma ba.
“Muddin gwamnatin Nijeriya ta ci gaba da bari ana kashe Kiristoci, Amurka za ta dakatar da dukkan tallafin da take bai wa Nijeriya nan-take, kuma mai yiwuwa za ta shiga wannan ƙasƙantacciyar ƙasar, cike da ƙarfin gwiwa domin kawar da ’yan ta’adda masu kaifin kishin Musulunci waɗanda ke yin wannan ta’asa,” in ji Trump.