Ya kuma tuna da tsohon abokin ajinsu wanda ya kasance tsohon Sufeton ƴansanda, marigayi Solomon Arase, wanda ya rasu a ranar Lahadi a Abuja bayan gajeriyar rashin lafiya. El-Rufai ya bayyana shi a matsayin mutum nagari, yana mai cewa tsarin ƴansanda na yanzu ya sha bamban da lokacin da Arase ya jagoranta.

Daga ƙarshe, ya ce zai sake rubuta ƙorafi ga IGP da kuma hukumar kula da ƴansanda (PSC), yana mai gargadi cewa idan jami’an tsaro suka zama kariya ga masu tada fitina, to hakan zai kai ƙasa ga rugujewa.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu bai shirya gudanar da sahihin zaɓe ba a 2027 – Buba Galadima

Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya yi zargin cewa gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ba ta da niyyar gudanar da sahihi kuma ingantaccen zaɓe a 2027.

Galadima ya bayyana hakan ne ranar Talata a wata hira da aka yi da shi a shirin Prime Time na gidan talabijin na Arise TV, inda ya ce gwamnatin da jam’iyyar APC ke jagoranta ta kankane cibiyoyin gwamnati don amfaninta.

Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu Kano Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo

“Wannan gwamnati ba ta shirya gudanar da zaɓen adalci ba. Daga yadda suke tafiyar da al’amura, za ka gane yadda suke tarwatsa jam’iyyun siyasa. Wannan yana nuna cewa ba sa son a samu hamayya a lokacin zaɓe,” in ji shi.

Galadima ya kuma yi gargadi kan shirin nada wani da ya kira mai lam’a a matsayin sabon shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), yana mai cewa hakan na iya jefa ƙasar cikin rudani.

“Ina fatan ba gaskiya ba ne, domin idan wannan mutumin ya zama shugaban INEC, ka tabbata cewa wannan gwamnati na neman tayar da yaƙin basasa,” in ji shi.

Sai dai bai ambaci sunan mutumin ba.

Dangane da batun fara yaƙin neman zaɓe da wuri da wasu jam’iyyu ke yi, Buba Galadima ya zargi INEC da gazawa wajen aiwatar da tanade-tanaden dokokin zaɓe.

“Wannan batun fara yaƙin neman zaɓe kafin INEC ta ba da izini, gwamnatin da ke kan mulki ce ta fara shi. Wannan yana nuna cewa INEC ba za ta iya zama mai adalci a irin wannan yanayin siyasa da muke ciki ba,” in ji shi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB
  • NECO ta saki sakamakon jarabawar 2025
  • Tinubu bai shirya gudanar da sahihin zaɓe ba a 2027 – Buba Galadima
  • ‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri Da Ɓarayin Kifi A Jihar Neja
  • Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno
  • Peter Obi ya kai wa Obasanjo ziyara
  • An kama tsohon minista kan zargin kisan kai domin tsafi a Nijar
  • Dole sai mun tantance wa’azi kafin a yi —Gwamnan Neja
  • Mutuwar majinyata: Asibitin Aminu Kano na roƙon KEDCO ya dawo da wutar lantarki
  • Tarihin Ƴan Majalisar Farko Kafin Da Kuma Zamanin Mulkin Mallaka (3)