Rashin tsaro: Ba za mu miƙa wuya ga ’yan ta’adda ba — Tinubu
Published: 3rd, May 2025 GMT
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci sojoji da su ƙara ƙaimi wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro da ke addabar Najeriya yana mai jaddada alkawarin cewa ƙasar ba za ta miƙa wuya ga ’yan ta’adda ba.
Da yake jawabi ga sojojin a lokacin ziyararsa a Katsina, Shugaba Tinubu ya nuna damuwa game da ƙalubalen tsaron da ake fuskanta a ƙasar a halin yanzu, inda ya bayyana su a matsayin wani lokaci mai muhimmanci a tarihin Najeriya.
Tinubu ya yi kira da a nuna jajircewa wajen kare ikon Najeriya da kuma dawo da zaman lafiya a faɗin ƙasar.
Ya tabbatar wa sojojin da kudirinsa na kula da jin daɗinsu, inda ya yi alƙawarin biyan alawus-alawus a kan lokaci, tabbatar da kula da lafiya, da kuma tallafa wa iyalansu.
2027: Mene ne mafita ga ’yan adawa? Yadda sojoji suka kashe manyan ’yan bindiga 5 a ZamfaraYa jaddada jarumtaka da sadaukarwarsu, yana mai cewa su ne “garkuwar Najeriya.” Ya jaddada cewa yaƙin ba wai kawai na yankuna ba ne, har ma da yaƙin neman ran kasar.
Tinubu ya tabbatar da ƙudirin gwamnatinsa na tallafa wa sojoji da ayyuka da zuba jari, yana mai gargaɗin masu kawo cikas na cikin gida da na waje cewa Najeriya ba za ta miƙa wuya ba.
Ziyarar tasa ta kuma hada da ƙaddamar da titin mota mai hannu biyu mai tsawon kilomita 24 da cibiyar aikin gona ta zamani a Katsina.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno
Sojojin Najeriya sun kashe aƙalla mayakan ƙungiyar ISWAP 8, ciki har da manyan kwamandojinta biyu a Jihar Borno.
Wata majiyar leƙen asiri daga rundunar haɗin kai ta OPHK ta bayyana cewa an kashe ’yan ta’addan ne a wata arangama da suka yi da sojojin a kan hanyar Maiduguri zuwa Baga a safiyar ranar Litinin.
DSS ta maka Sowore da Facebook a Kotu kan cin zarafin Tinubu Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabalaA cewar majiyoyin, an yi arangamar ce a kusa da Garin Giwa da ke gab da ƙauyen Kauwa, lokacin da ’yan ta’addan suka yi wa dakarun da ke sintiri kwanton ɓauna.
“A yayin wannan artabu, an kashe ’yan ta’adda takwas, ciki har da Munzirs biyu (kwamandojin filin daga na ƙungiyar) da kuma Qaid ɗaya (shugaban sashe).
“An kashe Modu Dogo, Munzir daga Dogon Chukun, wani Munzir da ba a bayyana ba, da Abu Aisha, shugaban sashe (Qaid) daga Tumbun Mota,” in ji wata majiya.
Majiyar ta ƙara da cewa wasu mayaƙa da dama sun samu raunuka, musamman waɗanda suka tsere da ƙafa bayan sun yi watsi da babura 14 da sojojin suka ƙwato.