Aminiya:
2025-11-03@03:08:12 GMT

2027: Mene ne mafita ga ’yan adawa?

Published: 3rd, May 2025 GMT

A yayin da jam’iyyun hamayya ke ci gaba da shirye-shirye tunkarar babban zaɓen shekara ta 2027, a bayabayan nan an ga yadda suke haɗuwa da juna, inda tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya tabbatar wa duniya cewa, suna tattaunawa domin ganin sun yi haɗakar da za ta kayar da Jam’iyyar APC mai mulki a zaɓen mai zuwa.

Ko da yake yaƙi ɗan zamba ne, abi da har yanzu bai fito fili ba zuwa yanzu shi ne dabarar da ’yan adawar ke son yin amfani da ita wajen tunkarar APC a 2027, ganin yadda Jam’iyyar ke ta ƙara karɓar masu sauya sheƙa daga wasu jam’iyyu.

Guguwar APC ta girgiza ’yan adawa

Wasu na ganin sauyin sheƙar na iya kawo babban koma-baya ga jam’iyyun adawar, ganin yadda a makon jiya shugabancin Jam’iyyar PDP ɗungurungum a Jihar Delta suka koma Jam’iyyar APC — ciki har da Gwamnan Sheriff Oboreɓwori da tsohon gwamnan jihar kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a jam’iyyar, Ifeanyi Okowa da sauran ƙusoshin jam’iyyar.

Hakazalika, a Jihar Kano an ga yadda Sanata Kawu Sumaila da wasu ƙusoshin Jam’iyyar NNPP mai mulkin jihar — a Majalisar Dokoki ta ƙasa, suka sauya sheƙa zuwa APC.

Masana na ganin waɗannan sauyin sheka za su yi mummunan tasiri ga su ’yan adawa a yayin da ake tunkarar babban zaɓen na 2027.

Zaɓin da ya rage wa ’yan adawa — Masana

Sai dai masu lura da al’amuran yau da kullum na ganin cewa, duk da wannan sauya sheƙa, jam’iyyun adawa na da zaɓi biyu: Ko dai su haɗe wuri ɗaya tare su fito da sabuwar jam’iyya, wato ‘maja’ ko kuma su goya wa ɗaya ɗaya daga cikinsu baya.

Tsohon Mataikamakin Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa a Shiyyar Arewa maso Yamma, kuma jigo a tattaunawar yin haɗakar jam’iyyun adawa, Alhaji Salihu Muhammad Lukman, ya ce: “Ana ƙoƙarin a ga an samu jam’iyyar da za a gyara ta, a gina ta sannan a ga yadda za a yi amfani da ita domin yin takarar shekarar 2027”.

Rikici ya dabaibaye jam’iyyu

Amma ya ce babban abin da ke ba su tsoro shi ne yadda aka, shiga aka dagula jam’iyyun adawan da ake da su.

A halin da ake ciki, rikicin cikin gida ya dabaibayen yawancin manyan jam’iyyun adawa, lamarin da ke barazana ga haɗin kansu.

Tun bayan babban zaɓen 2023 ne babbar Jam’iyyar adawa ta PDP ta faɗa rikicin shugabanci da ya kai ga cire shugabanta, Iyorchia Ayu, tare da ɗora Ambasada Iliya Damagun a matsayin muƙaddashi.

Tun daga wancan lokacin ne wasu ke ƙorafi game da yankin da shugaban jam’iyyar ya fito.

Haka nan a baya-bayan nan jam’iyyar ta yi fama da rikici na waye sahihin sakatarenta na ƙasa, lamarin da ya kai har Kotun ƙoli, inda ta ta tabbatar wa da Sanata Samuel Anyanwu da matsayin.

Jam’iyyar LP ita ma na fama da rikicin shugabanci tsakanin Mista Julius Abure da ɓangaren Sanata Nenadi Usman.

Haka ma Jam’iyyar NNPP, inda ɓangarori biyu ke jayayya kan mallakar jam’iyyar tsakanin NNPP mai alamar kayan marmari da kuma mai alamar littafi da alƙalami.

‘Maja’ ko mara baya?

Sai dai Alhaji Salihu Muhammad Lukman ya ce, “Idan son samu ne, kuma zai yiwu a yi amfani da ɗaya daga cikin jam’iyyun, idan kuma ba zai yiwu ba, mun yi nisa wajen tattaunawa da

jam’iyyun nan kuma idan an cim ma yarjejeniya, za mu fito mu bayyana wa jama’a.”

Sai dai ɗaya daga cikin manyan jagoran ’yan adawa kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya ce, zai yi wahala jam’iyyun su iya dunƙulewa domin samar da adawa mai ƙarfi a 2027.

“Idan ka kalli sunayen waɗanda suke taruwa, sam ba su a cikin tattaunawar, babu jam’iyya a ciki, saboda haka akwai kuskure,” in ji Shekarau.

Ya ƙara da cewa “A 2012 zuwa 2013 lokacin da muka fahimci cewa akwai buƙatar a kawo canji, ba ɗaiɗaikun mutane ne suka haɗu suka yi APC ba, jam’iyyu ne suka taru, suka samar da ita.”

A watan Fabarairun 2013 ne wasu daga cikin jam’iyyun siyasa — CPC da ACN da ANPP, da haɗin kan wasu ’yan siyasa da suka ɓalle daga Jam’iyyun PDP da APGA suka haɗe wuri ɗaya, inda suka samar da Jam’iyyar APC, wadda kuma ita ce ta yi nasarar ƙwace mulki a hannun Jam’iyyar PDP mai mulki a shekarar 2015, inda Muhammadu Buhari ya zama Shugaban ƙasa.

Hamayya ta mutu a siyasarmu — Bafarawa

Tuni tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Attahiru ɗalhatu Bafarawa ya ce, a yanzu babu wata hamayya da ta rage a fagen siyasar ƙasar nan.

Bafarawa ya ce, ’yan siyasar ƙasar ne ke hamayya da kansu da cutar juna game da neman muƙamai ba tare da sun amfanar wa talakawa ba.

Ya ƙara da cewa, yadda wasu ƙusoshin jam’iyyun hamayya ke tururuwar komawa APC a wannan ɗan tsakanin da ya rage wajen shekara biyu a yi babban zaɓe, wata babbar alamar tambaya ce.

Tsohon gwamnan ya yi zargin cewa duk wannan sauya sheƙa da ’yan adawa ke yi zuwa jam’iyya mai mulki ba don komai suke yi ba, face don amfanin kansu, saboda haka ya ce siyasar hamayya ta mutu a yanzu, domin babu aƙida.

“Cikin duhu ake, da mai nema da wanda ake nema. Shi mai nema idonsa sun rufe ba imani ba tausayi, shi dai ya samu muƙami, shi kuma talaka idonsa sun rufe ga yunwa ga talauci ga jahilci saboda haka duk a yamutse ake,’’ in ji shi.

Jam’iyyar NNPP mai mulki a Jihar Kano da kuma tsagin Kwankwasiyya a ’yan kwanakin nan sun sha fama da guguwar ficewar wasu jigajiganta zuwa APC.

Hakan dai ya sa masana harkokin siyasa da masu sharhi kan harkokinta ke ta nazari kan makomar siyasar jagoran NNPP na ƙasa da kuma Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda shi ne ya yi wa jam’iyyar takarar shugaban ƙasa a 2023.

Ana cikin haka, Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya shelanta cewa, nan ba da jimawa ba za su karɓe Kwankwason a jam’iyyar tasu, yana mai cewa na gaba kaɗan za su sanar da ranar bikin karɓar ’yan siyasar zuwa APC.

Akwai dai wasu bayanai da ba a tabbatar ba, da ke cewa akwai yiwuwar Kwankwaso na hanƙoron komawa APC ne domin ya samu kujerar mataimakin shugaban ƙasa. Akwai kuma tunanin cewa babban sharaɗin Kwankwaso na karɓar kowanne irin tayi a gwamnatin Shugaba Tinubu shi ne ba zai zauna ƙarƙashin Shugabancin Ganduje ba.

Sai dai ƙoƙarinmu na jin ta bakin ɓangaren Kwankwaso a kan wannan dambarwar ya ci tura. Wani ƙusa a tafiyar da ya nemi a sakaya sunansa ya ce lokacin da za su yi magana a kan batun bai yi ba tukunna, har yanzu suna nazari a kan lamarin. Sai dai da muka tuntuɓi Shugaban Jam’iyyar NNPP na Jihar Kano, Hashimu Sulaiman Dungurawa ya ce, a iya saninsu, Sanata Kawu ne kawai ya bar jam’iyyarsu a hukumance, “Shi ma har yanzu bai rubuto mana ba, kuma ai tun a watan Maris ma shi da wasu ’yan Majalisar Wakilai uku (Aliyu Sani Madaki da Kabiru Alhasan Rurum da Abdullahi Sani Rogo) muka kore su saboda ba su da wani amfani a jam’iyyarmu.”

Amma ya ƙi yarda ya yi magana a kan batun sauya sheƙar Kwankwason, inda ya ce Kwankwason ne kaɗai zai iya magana a kai da kansa.

Buba Galadima: Kwankwaso ba zai koma APC ba

ɗaya daga cikin makunsantan Kwankwason, Injiniya Buba Galadima, a kwanakin baya ya musanta batun yiwuwar komawar Kwankwason APC, inda ya ce babu gaskiya a labarin, kuma idan ma da gaske ne, to daga wajensu ya kamata a ji labarin, ba Ganduje ba.

Ya kuma ƙaryata batun yiwuwar shigarsu haɗakar ’yan adawa ta SDP, wacce tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i ke jagoranta, inda ya ce, “Aƙidunmu da nasu sun sha bamban, su ’yan jari-hujja ne, mu kuma talakawa ne a gabanmu”.

‘Kwankwaso na cikin sarƙaƙiya’

A hirarsa da Aminiya, masani kan harkokin siyasa kuma malami a Jami’ar Skyline da ke Kano Dakta Kabiru Sa’id Sufi ya ce, ko Kwankwason ya zaɓi ya zauna a NNPP ko kuma ya koma wata jam’iyyar, zai fuskanci wasu ƙalubale.

A cewar Dakta Sufi, “Idan Kwankwaso ya zaɓi ya zauna a jam’iyyarsa, to sai ya nemo wasu jiga-jigan ’yan siyasar da za su maye gurbin waɗanda suka fice kwatankwacin ƙarfinsu a siyasance, wanda hakan kuma ba abu ne mai sauƙi ba, saboda sun bayar da gudunmawa ga nasarar jam’iyyar, komai ƙanƙantarta.

“Sannan idan ya shiga wata jam’iyyar da ba APC ba, zai yaƙi ’yan adawa masu yawa ke nan. Idan kuma APCn ya koma, zai sake haɗuwa da mutanen da yanzu suka raba gari ke nan, kuma yadda za su sake shiryawa babban ƙalubale ne. Sannan dole ya yi wa magoya bayansa gamsasshen bayani kan dalilin yin haka domin su amince da shi,” in ji Sufi.

A yayin da zaɓukan 2027 ke daɗa ƙaratowa, duk alƙiblar da Kwankwaso ya zaɓa za ta zama zakaran gwajin dafin makoma ba wai iya siyasarsa kaɗai ba, har ma da ta NNPP da kuma Kwankwasiyya baki ɗaya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: adawa SDP Jam iyya shugaban jam iyyar Shugaban Jam iyyar ɗaya daga cikin Jam iyyar NNPP tsohon Gwamnan Jam iyyar APC sauya sheƙa a jam iyyar a Jam iyyar

এছাড়াও পড়ুন:

Dan Majalisar Jema’a/Sanga, Daniel Amos, Ya Koma Jam’iyyar APC

Harkokin siyasa na Kudancin Kaduna ya dauki wani salo yayin da dan majalisar da ke wakiltar mazabar Jema’a/Sanga a majalisar tarayya, Hon. Dan Amos, ya sanar da komawarsa jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar PDP,  yana mai cewa ya dauki wannan mataki ne domin ya hada kai da gwamnatocin jiha da na tarayya don cigaban yankin.

Yayin da yake jawabi ga manema labarai a Kafanchan kafin karbar sa a hukumance tare da Sanata Marshall Katung, Amos ya bayyana cewa wannan mataki ya biyo bayan dogon shawarwari da aka yi da shugabannin al’umma, kungiyoyin addini, kwararru da kuma sarakunan gargajiya a fadin mazabarsa.

Ya ce jam’iyyar PDP, wacce a da take da karfi sosai a Kaduna, ta ragu saboda rikice-rikicen cikin gida da suka dade suna faruwa, wanda hakan ya janyo ficewar mambobi da kuma rasa goyon bayan talakawa a fadin kasa.

“Mun dauki lokaci muna tattaunawa da mutane a matakai daban-daban – daga tsarin jam’iyya zuwa kungiyoyin addini da na kwararru – kuma abin da muka cimma shine, don amfanin jama’armu, ya dace mu nemi wata madogara ta daban,”

“Ya zama sauki mu shiga APC saboda muna ganin irin kokarin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Uba Sani ke yi wajen hada yankin Kudancin Kaduna cikin shirin cigaba da ci gaba da kasa.” in ji Amos.

Dan majalisar ya yaba wa Shugaba Tinubu bisa nadin ɗan asalin yankin, Janar Christopher Musa, a matsayin Babban Hafsan Tsaro (CDS) da kuma amincewa da a kafa Jami’ar Kimiyyar Aiki ta Tarayya da Asibitin Tarayya (Federal Medical Centre) a yankin.

Ya kuma gode wa Gwamna Uba Sani saboda gudanar da mulki cikin hadin kai, gina ababen more rayuwa, da bude kofa ga kowa, wanda ya ce ya karfafa zumunci da bai wa kowane bangare na jihar damar shiga.

“Shugaban kasa da gwamna suna nuna shugabanci na hada kan jama’a. Wannan ya sa muka ga dacewar mu hade da su domin mu samu karin cigaba a yankinmu,” in ji Amos.

Amos ya karyata jita-jitar cewa ya koma APC don son kai ko muradin siyasa, yana mai cewa wannan mataki ne na Allah da kuma na amfanin jama’ar Kudancin Kaduna.

“Ba don bukatar kaina ba ne, amma don mu tabbatar da yankinmu ya ci gajiyar dimokuradiyya. Ina da yakinin cewa tarihi zai tuna da mu bisa wannan mataki na jarumta da muka dauka,” ya kara da cewa.

Dan majalisar, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Ayyukan Majalisa, ya tabbatar wa mazaunar mazabarsa cewa komawarsa APC ba za ta canza manufarsa ta kyakkyawan wakilci ba, yana mai cewa ya shiga jam’iyyar mai mulki ne don kara daraja, ba don kawo rarrabuwar kawuna ba.

Ya bayyana fatan cewa da hadin kai tsakanin jama’a da gwamnati, Kudancin Kaduna zai ci gaba da samun cigaba a bangaren ababen more rayuwa, ilimi, da tsaro.

An shirya taron karbar Amos, Sanata Katung, da sauran wadanda suka koma daga PDP zuwa APC a ranar 1 ga Nuwamba a Kafanchan, kuma manyan baki da ake sa ran halarta sun hada da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, da kuma shugabannin jam’iyyar APC daga fadin kasar nan.

Radio Nigeria ta ruwaito cewa wannan sauyin jam’iyya ya nuna babban sauyi a siyasar jihar Kaduna, wanda ya kawo karshen rinjayen PDP da ta yi sama da shekaru 25 a Kudancin jihar.

Daniel Karlmax

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • 2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su
  • Shin Mene Ne Matsalar Liverpool A Wannan Kakar?
  • Rikicin PDP: Tsagin Wike ya dakatar da Damagum
  • PDP ta dakatar da Anyanwu da wasu ’yan tsagin Wike
  • PDP ta dakatar da Anyanwu da wasu da ke da alaƙa da Wike
  • ‘An Kashe Masu Zanga-zanga Akalla 500 a Tanzania’
  • Dan Majalisar Jema’a/Sanga, Daniel Amos, Ya Koma Jam’iyyar APC
  • Zaben 2027 Zai Kasance Ne Tsakanin Mulkin Tinubu Da Zabin Ƴan Nijeriya —Atiku Abubakar
  • Kotu ta tsige dan majalisar da ya sauya sheka zuwa APC
  • Madagascar Ta Sanar da Kafa Sabuwar Gwamnati Tare da Manyan ‘Yan Adawa