Aminiya:
2025-04-30@19:00:27 GMT

Ƙarin ’yan Najeriya za su fuskanci talauci nan da 2027 — Bankin Duniya

Published: 25th, April 2025 GMT

Bankin Duniya ya yi hasashen cewa talauci a Najeriya zai ƙaru da kashi 3.6 cikin ɗari a cikin shekaru biyar masu zuwa, ciki har da shekarar zaɓe ta 2027.

Wannan hasashe yana ƙunshe ne a cikin rahoton Bankin wanda aka fitar a lokacin taron bazara na Bankin Duniya da Asusun Lamuni na Duniya (IMF) da ake yi a birnin Washington, D.

C., a ƙasar Amurka.

Rahoton ya jaddada cewa duk da wasu nasarorin da aka samu a harkokin tattalin arziki a kwanakin baya, musamman a ɓangaren da ba na man fetur ba a cikin rubu’i na ƙarshe na shekarar 2024, matsalolin da suka shafi dogaro da albarkatun ƙasa da kuma raunin ƙasa na iya kawo cikas ga ci gaba.

A cewar Bankin Duniya, Najeriya, tare da wasu ƙasashe masu arzikin albarkatu da masu rauni a yankin kudu da Sahara, za su fuskanci ƙaruwar talauci —saɓanin ƙasashen marasa arzikin albarkatu, waɗanda ake tsammanin za su samu raguwar talauci cikin sauri.

’Yan bindiga sun kashe ango, sun sace amarya a Nasarawa NAJERIYA A YAU: Dalilin da zazzaɓin cizon sauro ba ya jin magani

Rahoton ya bayyana cewa, “Ana hasashen talauci zai ƙaru da kashi 3.6 cikin ɗari tsakanin 2022 zuwa 2027a ƙasashe masu arzikin albarkatu da masu rauni—ciki har da manyan masu tattalin arziƙo kamar Najeriya da Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango.”

A halin da ake ciki, Sanatan da ke wakiltar Ondo ta Kudu, Jimoh Ibrahim, ya yi kira ga ƙasashen a Afirka, Bankin Duniya, da Asusun Lamuni na Duniya (IMF) da su ba da fifiko ga amfani da bayanai don ci gaban Afirka.

Da yake magana a yayin taron bazara na IMF/Bankin Duniya a Washington, D.C., Amurka, Sanata Jimoh Ibrahim ya jaddada muhimmancin bayanai a ci gaban tattalin arziki da siyasa.

Ya ce, “Idan babu bayanai ba, babu wanda zai iya rage aikata laifuka yadda ya kamata ko kuma gudanar da gwamnatin da ke da nufin cimma nasarar rage talauci.”

Ya ƙara da cewa, “Bayanai kan yawan jama’a da cikakkun bayanai na mutane sun nuna cewa ya kamata ’yan ƙasa su mallaki fasfo na tantancewa domin tattara muhimman bayanai game da su wane ne su da kuma abin da suke yi.”

Sanatan ya yi gargadi ga IMF game da yin hasashe ba tare da ingantattun bayanai ba, yana mai cewa irin waɗannan hanyoyin ba su da inganci.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Albarkatu Bankin Duniya Najeriya Tattalin Arziki Bankin Duniya

এছাড়াও পড়ুন:

Xi Jinping Ya Ziyarci Sabon Bankin Raya Kasashen BRICS

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yanayin Rudani Na Tsawon Kwanaki 100 Kashedi Ne Ga Amurka
  • Rawar da Arewa za ta taka a Zaɓen 2027
  • Wang Yi: Neman Sulhu Da Ja Da Baya Riba Ne Ga Masu Son Cin Zali
  • Sabbin Bayanai Kan Fashe-Fashe Wasu Abubuwa A Tashar Jiragen Ruwan Kasar Iran
  • Xi Jinping Ya Ziyarci Sabon Bankin Raya Kasashen BRICS
  • NAJERIYA A YAU: Dalilin karyewar farashin shinkafa a kasuwannin Najeriya
  • Mutanen da talauci ya yi wa katutu zai ƙaru a Nijeriya — Bankin Duniya
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jadadda Cewa: Duk Wani Harin Wuce Gona Da Iri Kan Iran Zai Fuskanci Mayar Da Martani
  • Akwai Ƙarin Gishiri A Yawan  Masu Sauyin Jam’iyya Zuwa APC – El-Rufai
  • NAJERIYA A YAU: “Dalilin da muke sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki”