Kasashen Faransa Masar Da Jordan Sun Yi Taro Akan Gaza
Published: 7th, April 2025 GMT
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya isa birnin alkahira a jiya Lahadi, inda ya sami kyakkyawar tarba daga Abdulfattah al-Sisi.
Ziyarar ta shugaban kasar Faransa a Masar tana a karkashin tattaunawar da aka bude ne a yau Litinin da kasar Jordan ta kuma ita kanta mai masaukin baki akan halin da Gaza take ciki.
Yin wannan taron dai ya biyo bayan sake dawo da yaki da HKi ta yi ne a Gaza, saboda ta ki amincewa da bude shafi na biyu yarjejeniyar tsagaita wutar yaki.
A yau Litinin shugabannin kasashen na Masar da kuma Faransa sun yi tir da sake dawo da yaki da Isra’ila ta yi a zirin Gaza, haka nan kuma kin amincewa da shigar da kayan agaji a cikin yaki.
Ana sa ran cewa shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron zai ziyarci yankin Arisha mai nisan kilo mita 50 daga zirin Gaza saboda ya gana da ma’aikatan agaji a suke da sansani a wurin.
Bayan kammala taron nasu, kasashen uku sun fitar da bayani na yin kira da a tsagaita wutar yakin Gaza da gaggawa, da kuma bude kafar ci gaba da aikewa da kayan agaji zuwa yankin.
Tun da fari, shugabannin kasashen Masar da Faransa sun yi taron manema labaru da su ka nuna kin amincewarsu da duk wata siyasa ta korar Falasdinawa daga kasarsu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Harkokin Wajen Siriya Yana Rasha Don Bude Sabon Shafi Tsakaninsu
Ministan harkokin waje na kasar siriya ya isa birnin Mosco a yau Alhamis don bude sabon shafi da kasar Rasha bayan kifar da gwamnatin Bashar Al-asad a shekarar da ta gabata.
Shafin yanar gizo na larabai Arabnews na kasar Saudiya ya bayyana cewa Asaad Hassan al-Shaibani tuna ya gana da ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov sannan ya fada masa cewa, kasar Siriya tana son ta kara tabbatar da wasu yarjeniyoyi dake tsakanin Rasha da Siriya a can baya, sannan a samar da sabbin wuraren wadanda sabuwar gwamnatin rikon kasar Siriya take son ta kulla da Rasha, a cikin yanayin mutunta juna.
A nashi bangaren Sergey Lavrov ya bayyana cewa kasar Rasha a shirye take ta taimakawa sabuwar gwamnatin kasar Siriya ta fita daga cikin matsalolin da take fama da su. Kuma tana fatan shugaba Ahmad Ashaar zai halarci taron kasashen Larabawa da Rasha wanda za’a gudanar nan gaba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kananan Yan Wasan Dabben Gargajiya Na Iran Sun Zama Zakara A Gasar Wannan Shekara July 31, 2025 Canada Zata Amince Da Samuwar Kasar Falasdinu A Taron MDD July 31, 2025 Shugaban Kasar Lebanon Aun Ya Ce Mun Aike Wa Amurka Sakwanni Akan Dakatar Da Hare-haren HKI July 31, 2025 Sojojin Mamaya Suna Ci Gaba Da Kisan Kiyashi A Gaza July 31, 2025 Kassim: Duk Wanda Yake Neman Hizbullah Ta Ajiye Makamanta Yana Yi Wa Isra’ila Aiki July 31, 2025 Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Yi Allah Wadai Da Takunkumin Da Amurka Ta Kakaba Mata July 31, 2025 Tawagar Iran Ta Fice A Taron Majalisun Dokokin Kasashen Duniya A Lokacin Jawabin Wakilin Isra’ila July 31, 2025 Kasar Iran Ta Bayyana Gushewar Hasashen Raunin Karfin Sojinta Kuma Ba Zai Dawo Ba July 31, 2025 Sojan Amurka Ya Bada Ruwayar Yadda Sojojin Sahayoniyya Suka Kashe Wani Yaro Balasdine July 31, 2025 Sojojin Yemen Sun Kai Zafafan Hare-Hare Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Guda Uku July 31, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci