Cin Zali Ba Zai Iya Hana Kasashen Afirka Ci Gaba Ba
Published: 7th, April 2025 GMT
A nata bangare, ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ita ma ta sanar da cewa, kowace kasa na da hakkin neman ci gaba, saboda haka bai kamata a ba wasu kasashe damar yin babakere ba. Ganin yadda kasar Amurka ke neman dora moriyarta a kan hakkin kasashen duniya, ya sa kasar Sin kin amincewa da matakinta.
Yanzu haka ra’ayin kasar Sin na samun amincewa daga mutanen kasashe daban daban. Bisa sakamakon binciken ra’ayin jama’a da kafar watsa labarai ta kasar Sin CGTN ta gudanar, cikin mutanen kasashe daban daban da aka yi musu tambayoyi, kaso 86.9% sun ce matakan ramuwar gayya da kasashe daban daban suka dauka bisa matakin karbar karin haraji na kasar Amurka, sun halatta, kana kaso 87.7% na mutanen sun ce ya kamata kasashe daban daban su yi hadin gwiwa, a kokarin dakile matakin Amurka na cin zarafin sauran kasashe.
A nahiyar Afirka ma, matakin Amurka ya janyo sabon tunani kan dabarar raya kasa. Inda masanin ilimin shari’a na kasar Najeriya Livingstone Wechie ya ce, ko da yake kasar Amurka ta taba alkawarin raya masana’antu a kasashen Afirka karkashin dokar AGOA, sakamako na karshe ya nuna cewa ta yi karya ke nan. Saboda haka mista Wechie ya ce dogara kan tallafin da ake samu daga kasashen waje ba zai raya tattalin arzikin kasashen Afirka yadda suke bukata ba.
Kana a ganin masaniyar ilimin tattalin arziki ‘yar kasar Afirka ta Kudu, Annabel Bishop, cin zalin da kasar Amurka ke yi, zai sa kasashen Afirka gaggauta karkata ga abokan hulda dake kan hanyar tasowa wajen gudanar da ciniki.
Ban da haka, Leseko Makhetha, masanin ilimin tattalin arziki na kasar Lesotho, ya ce matsin lambar da kasar Amurka ta yi wa kasashen Afirka, za ta sa su kara kokarin gina yankin ciniki mai ‘yanci na nahiyar Afirka.
Yayin da a nata bangare, minista mai kula da masana’antu, ciniki da zuba jari ta kasar Najeriya, Jumoke Oduwole, ta ce matakin matsin lamba na Amurka ya sa Najeriya tabbatar da niyyar raya bangaren fitar da kayayyakin da ba su shafi danyen mai ba. A cewarta, Najeriya za ta yi kokarin inganta kayayyakinta, don neman sayar da su a karin kasuwannin kasashe daban daban.
Amurka na son toshe hanyar neman ci gaban tattalin arziki ta kasashen Afirka, da ta sauran kasashe masu tasowa na nahiyoyi daban daban. Sai dai ba za ta samu biyan bukata ba. Saboda matakin cin zalin ba zai haifar da komai ba, illa farkarwa, da dogaro da kai, da karfin zuci, da hadin kai, ga kasashe daban daban. Tabbas rinjayen kasashe, wadanda suke da adalci, za su ci nasara a karshe, a wannan gasar da ake gudanar da ita a duniya. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
An Kaddamar Da Bikin Gabatar Da Jerin Shirye-shiryen Telebijin Da Fina-finai Na CMG A Birnin Astana
Gabanin tafiyar shugaban kasar Sin Xi Jinping birnin Astana na kasar Kazakhstan, inda zai halarci taron koli na Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya karo na biyu, an kaddamar da bikin gabatar da jerin shirye-shiryen shirye-shiryen telebijin da fina-finai, na babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG na shekarar 2025 a birnin Astana.
Za a gabatar da shirye-shiryen CMG guda 12, ciki har da alakar dake tsakanin shugaba Xi Jinping da al’adun kasar Sin, da hanyar zamanintar da kasa mai salon kasar Sin na musamman da sauransu, a manyan kafofin watsa labaru na kasashen Kazakhstan, da Kyrgyzstan, da Tajikistan, da Turkmenistan, da Uzbekistan da dai sauransu.
Shugaban gidan CMG Shen Haixiong ya bayyana cewa, a ta bakin shugaba Xi Jinping, kasar Sin kyakkyawar abokiya ce ta kasashen tsakiyar Asiya, don haka ya kamata a kara yin kokari wajen raya makomar bai daya ta Sin da kasashen tsakiyar Asiya. Kuma kafar CMG ta yi hadin gwiwa tare da kafofin watsa labaru na kasashen tsakiyar Asiya, wajen gabatar da shirye-shirye, don sa kaimi ga aiwatar da ayyukan da aka cimma, a taron koli na Sin da tsakiyar Asiya na shekarar 2023, da kara gudanar da mu’amalar al’adu, da sada zumunta a tsakaninsu bisa manufofin da shugaba Xi ya gabatar. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp