Mutane 7 Sun Mutu, Kadarorin Miliyan 50.3 Sun Salwanta Dalilin Gobara A Kano
Published: 14th, March 2025 GMT
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta bayyana cewa mutane bakwai sun rasa rayukansu a gobara daban-daban da suka afku a jihar cikin watan Fabrairu 2025. Rahoton ya kuma nuna cewa an samu tashin gobara 77, an gudanar da ceto 11, yayin da aka samu ƙarar bogar bogi guda uku a cikin wannan lokaci.
Sanarwar da Kabiru Isah Jaafar ya fitar a madadin jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Saminu Yusif Abdullahi, ta bayyana cewa kadarori da darajarsu ta kai naira miliyan 50.
Hukumar ƙarƙashin jagorancin Alhaji Sani Anas ta shawarci al’umma da su kula da amfani da wuta domin guje wa afkuwar gobara. Haka nan, an yi kira ga direbobi da su bi dokokin hanya, musamman a manyan tituna, don rage afkuwar haɗura da kare rayuka da dukiyoyi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Gobara
এছাড়াও পড়ুন:
Za A Yi Allurar Rigakafi Ga Dabbobi Sama Da Miliyan Daya A Babura
Dabbobi sama da miliyan guda ne ake sa ran za a yi wa rigakafi a fadin karamar hukumar Babura da ke jihar Jigawa.
Shugaban karamar hukumar Babura, Alhaji Hamisu Muhammad Garu, ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da aikin rigakafin dabbobi na bana.
A cewarsa, fiye da tumaki da awaki miliyan daya da shanu dubu ashirin ake sa ran za a yi wa rigakafi a fadin karamar hukumar.
Ya jaddada cewa karamar hukumar na da cikakken shiri da kudurin tallafawa sauyin noma na Gwamna Umar Namadi, domin inganta rayuwa da tattalin arzikin al’ummar jihar.
Shugaban ya jaddada muhimmancin masu kiwon dabbobi su bada hadin kai yayin aikin rigakafin domin tabbatar da lafiyar dabbobinsu.
Alhaji Hamisu Garu ya kuma nuna jin dadinsa game da zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya a yankin, yana mai kira gare su da su ci gaba da gudanar da rayuwa cikin fahimta da hadin kai.
Haka zalika, yayin taron, Shugaban Sashen Noma da Albarkatun Kasa, Malam Lawan Sabo Kaugama, ya bayyana cewa an ware cibiyoyi guda goma sha biyu domin gudanar da aikin rigakafin wanda ake sa ran zai dauki kwanaki hudu.
Ya yaba da kokarin gwamnatin jiha da ta karamar hukuma wajen samar da allurar rrigakafn da kuma duk wasu kayan aiki da ake bukata.
Usman Muhammad Zaria