Senegal ta yi Allah-wadai da tsare ‘yan kasarta a Mauritania
Published: 14th, March 2025 GMT
Ministar Harkokin Wajen Senegal, Yacine Fall, ta ce hukumomin kasarta sun bayyana rashin jin dadi game da tsare ‘yan Senegal da kuma tilasta musu barin kasar bisa zarginsu da zama cikin Mauritania ba bisa ka’ida ba.
Hukumomin kasar Mauritaniya sun kaddamar da wani gangamin korar bakin haure daga kasashen Afirka daban-daban.
A wani jawabi da ta gabatar yayin taron amsa tambayoyi a majalisar dokokin kasar ta Senegal kamar yadda kamfanin dillancin labaran Faransa Fall ya ruwaito, “kowace kasa tana da nata dokoki, amma rashin samun takardar zama ko takardar izinin aiki a cikin sa ba zai taba hujja ta cin zarafi ba.
Majalisar dokokin kasar Senegal ta yi kira ga gwamnatin da ta gaggauta daukar matakai don ganin an warware matsalar a’yan kasar da suke zaune a Mauritania,” tana mai bayyana abin da Mauritania ke yi a matsayin “cin zarafin bil’adama.”
A nata bangaren, ma’aikatar harkokin wajen kasar Mauritaniya a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce kasar ta tabbatar da bude kofa ga bakin haure tare da karfafa tare da yin komai a cikin tsari, da kuma shiga kasar cikin kasar bisa sharudda da suke a a kan doka, tana mai cewa “Mauritaniya tana maraba da baki da ke zama a cikin kasarta bisa doka kuma cikin yanayi mai kyau, musamman wadanda suka fito daga kasashe makwabta.”
Ta kuma yi nuni da cewa, yin kaura ba bisa ka’ida ba a wasu lokuta ya kan zama barazana ga yanayin zaman lafiya da tsaron kasa, a kan haka ne take kokarin tantance yanayin baki mazauna kasar, amma hakan ba zai yi tasiri a kan alakar da ke tsakaninta dad a kasashen dab akin suka fito ba, kuma za a warware batun ta hanyar fahimtar juna.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Najeriya Na Asarar Dala Biliyan 10 Bayan Girbi Duk Shekara- Gwamnatin Tarayya
Gwamnatin Tarayya ta ce Najeriya na rasa sama da Dala Biliyan 10 duk shekara sakamakon asarar amfanin gona bayan girbi.
Ministan Noma Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana haka a wajen kaddamar da shirin Hanyar Inganta Noma da Kayayyakin Mire Rayuwa a Yankunan Karkara G.R.A.I.N a ƙaramar hukumar Birnin Kudu ta Jihar Jigawa.
Ya ce asarar na faruwa ne saboda rashin ingantattun wuraren ajiya, karancin ababen more rayuwa, sauyin yanayi da kuma ambaliya.
Kyari ya bayyana cewa noma na bada gudunmawar kashi 24 bisa 100 na Jimillar Darajar Kayayyaki da Ayyuka da Kasa ta Samar a Cikin Shekara GDP, inda ƙananan manoma ke samar da sama da kashi 70 bisa 100 na abincin da ake ci a ƙasa.
Ya jaddada cewa gwamnati za ta tallafa musu da kayan noma na zamani da wuraran kasuwanci domin inganta tattalin arziki.
A nasa jawabin, Gwamna Umar Namadi na Jigawa ya yaba da samun Cibiyar Cigaban Karakara ta Pulse ta farko a Jigawa, yana mai cewa za ta kawo sauyi a harkar noma da rayuwar jama’ar karkara.
Haka zalika, shi ma Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya ce haɗin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu zai taimaka wajen ci gaban tattalin arziki.
Shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kudu, Alhaji Builder Muhammad Uba, ya jaddada goyon bayansa ga shirin Renewed Hope Agenda na Shugaba Tinubu tare da yabawa gwamnatin Namadi kan sauya fasalin noma a jihar.
Usman Muhammad Zaria