HausaTv:
2025-04-30@23:08:43 GMT

Karancin Man Fetur A Jamhuriyar Nijar Yana Damun ‘Yan Kasa

Published: 14th, March 2025 GMT

An kusa shiga mako guda daga lokacin da aka fara fuskantar karancin mai a gidajen man fetur da hakan ya jefa masu ababan hawa cikin damuwa.

Rabon man fetur da kamfanin SONIDEP yake yi bai wadatar da masu abubuwan hawa ba, yana kuma kawo cikas a harkokinsu na yau da kullum.

Da akwai dalilai da dama da su ka haddasa karancin man fetur din, sai dai al’ummar kasar suna son ganin mahukunta sun fito fili sun yi musu bayanin abinda yake faruwa.

Wani mazaunin birnin Yemai Assoumane Hamadou suley ya fada wa manema labaru cewa; Ba mu da cikakken bayani akan abinda yake faruwa, domin mahukanta da ya kamata su fito su yi bayani, ba su yin hakan.

Su kuwa matukan motocin Tasi (SYNCTAXITU), cewa su ka yi, ya kamata gwamnati ta kara yawan man fetur da ake hakowa a kowace rana.

Babban sakataren kungiyar matuka Tasi din Agali Ibrahim cewa ya yi, “ Idan aka fada mana cewa da akwai manyan motocin jigilar man fetur 25 da ake bai wa birnin Niamey, to abinda zan fada musu shi ne cewa bai isa ba.”

Haka nan kuma ya yi ishara da fasakwaurin man fetur din da ake yi da yana daga cikin dalilin karancinsa da ake fuskanta.

Da akwai shirin kara yawan tankokin mai daga 25 zuwa 100 da za a rika bai wa babban birnin ka kowace rana.

Ba kasafai ake shiga irin wannan yanayin ba a jamhuriyar Nijar wacce take da arzikin mamn fetur da aka fara hako shi tun a wajajen 2011.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Ma’aikatar Sharia A Nan Iran Zata Bayyana Abinda ya farsu A Tashar Jiragen Ruwa Na Shahid Rajae

Kakakin ma’aikatar sharia a nan JMI ya bada sanarwan cewa,ma’aikatar za ta bayyanawa mutanen sakamakon bincken da suka gudanar kuma suke ci gaba da yi, dangane da fashewa da kuma gobatar da ta tashi a tashar jiragen ruwa ta Shahid Rajaee a cikin yan kwanakin da suka gabata. .

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran, ya bayyana cewa, Asgar Jahangir  kakakin ma’aikatar sharia da kuma Zabihullah Khudayiyan shugaban hukumar bincike ta kasa, sun gudanar da taron hadin guiwa da yan jaridu da kafafen yada labarai na cikin gida da waje a safiyar, dangane da fashewa da kuma gobarar da ta biyo baya a tashar jiragen ruwa na Shahid Rajaee.

Banda haka jami’an sun amsa tambayoyin yan jarida bayan jawabansu dangane da hatsarin wanda ya lakume rayukan mutane, fiye da 70 da kuma jikata wasu kimani dubu guda.

Kafin haka dai jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminaee ya bada umurni ga ma’aikatun biyu su gudanar da cikekken bincike don gani musabbabin wannan hatsarin sannan idan akwai wadanda suka da hannu, ko sakaci a cikinsa, a bi tsarin da ake da shi don hukunta wadanda suke da laifi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran ta sha alwashin ci gaba da aiwatar da manufofinta na raya dangantakarta da Nijar
  • Amurka ta sake laftawa wasu kamfaninin mai na Iran takunkumi
  • Ma’aikatar Sharia A Nan Iran Zata Bayyana Abinda ya farsu A Tashar Jiragen Ruwa Na Shahid Rajae
  • Riza’i: Babu Hannun  Waje A Cikin Hatsarin Da Ya Faru A Tashar Ruwa Ta Shahid Raja’i
  • Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Na Iran Ya Ce: Maganar ‘Yan Sahayoniyya Rudu Ne Maras Amfani
  • Gwamnati Ta Kafa Kwamitin Binciken Yawaitar Haɗurran Tankokin Man Fetur A Nijeriya 
  • Nijeriya Na Ke Yi Wa Biyayya Ba Wani Ko Jam’iyya Ba – El-Rufai
  • Sin Na Maraba Da Karin Abokai Daga Kasa Da Kasa Su Ziyarci Kasar
  • Shugaban Kasar Yana Maraba Da Masu Zuba Hannun Jari A Kasarsa Daga Kasashen Waje
  • Kissoshin Rayuwa: Imam Al-Hassan 114