Wata Kungiya Mai Zaman Kanta Ta Ba Masu Bukata Ta Musamman Su 450 Tallafi a Kano
Published: 6th, March 2025 GMT
A wani yunkuri na bunkasa sana’o’in hannu da kuma karfafa wa masu bukata ta musamman, wata kungiya mai zaman kanta mai suna Women Farmers Advancement Network (WOFAN) ta kaddamar da wata cibiyar kasuwanci ta mata masu sarrafa kayayyaki tare da baiwa masu bukatar su 450 a yankin Karfi.
Wannan yunƙurin na da nufin ƙarfafa su 450 da kayan aikin farawa, wanda zai ba su damar yin aiki mai daraja da riba.
Da take jawabi a wajen taron, Daraktar Hukumar WOFAN-ICON2, Dakta Salamatu Garba, wadda ta samu wakilcin jami’in kula da ofishin na Kano, Alhaji Dayyabu Abubakar, ta jaddada cewa cibiyar kasuwanci za ta baiwa mata damar kula da harkokin kasuwancinsu da kuma amfani da dabarun tattaunawa da suka samu ta hanyar WOFAN.
Ta bayyana cewa, wannan shiri zai karfafawa mata ta hanyar ba su ikon sarrafa albarkatunsu, da kara samun riba, da kuma fadin albarkacin bakinsu kan batutuwan da suka shafe su.
Ta kara da cewa shirin ya yi daidai da manufofin shirin WOFAN-ICON2 a karkashin gidauniyar Mastercard, wanda ke kokarin samar da ayyukan yi mai dorewa ga matasa, mata, da masu bukata ta musanna a jihohi goma na Najeriya. Wanda shi ne shirin shekara biyar.
“Cibiyar kasuwancin Karfi ita ce irinta ta biyu a karamar hukumar Kura, bayan da aka kafa irin wannan wurin a kasuwar Kura. Kasuwar Kura, daya ce daga cikin manyan kasuwannin da dake Kano, tana sayar da hatsi sama da tireloli 500 a kullum zuwa wurare daban-daban a ciki da wajen Najeriya.”
Hakimin Karfi, Alhaji Magaji Shehu wanda Jamilu Magaji ya wakilta ya taya wadanda suka ci gajiyar shirin murna, inda ya bayyana cewa shirin ba wai kawai zai amfanar da jama’a ba, zai kuma yi tasiri ga al’umma baki daya.
Wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin, Safiya Isah, Safiya Isah Kura, Rakiya Rabi’u, Haruna Sule Karfi da Sule Shehu sun nuna jin dadinsu da tallafin tare da ba da tabbacin za su yi amfani da kudaden cikin adalci.
Gidan Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, cibiyar kasuwancin ta kunshi shaguna guda uku: daya yana aiki a matsayin ofishi da mambobin kungiyar za su tattauna matsalolinsu da dabarun kasuwanci a cikin kasuwar Karfi, yayin da sauran biyun kuma aka kebe su domin gudanar da harkokin kasuwanci.
KHADIJAH ALIYU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Karfi
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaba Tinubu Ya Taya Sabon Firaiministan Kanada Mark Carney Murna
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Mista Mark Joseph Carney murna bisa zaɓensa a matsayin Firaiminista na 24 na ƙasar Kanada, bayan nasarar jam’iyyar Liberal a zaɓen majalisar dokokin da aka kammala kwanan nan.
A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya bayyana zaman Carney a wannan matsayi a matsayin wani muhimmin ci gaba, musamman a wannan lokaci da Kanada ke bukatar gogaggen shugaba domin fuskantar ƙalubale da dama.
Carney, wanda fitaccen masani ne a fannin tattalin arziki, ya taba rike mukamin Gwamnan Babban Bankin Kanada daga shekarar 2008 zuwa 2013, sannan ya ci gaba da zama Gwamnan Babban Bankin Ingila daga 2013 zuwa 2020.
Shugaba Tinubu ya bayyana kwarin gwiwar cewa ƙwarewar sabon shugaban Kanada a fannin kuɗi da shugabanci za ta taka muhimmiyar rawa wajen gina makomar ƙasar. Haka kuma, ya sake jaddada kudirin Najeriya na ƙarfafa dangantakar diflomasiyya da Kanada, musamman a fannonin ilimi, sauyin yanayi da hijira.
Shugaban Najeriya ya ƙara da cewa yana fatan kafa kyakkyawan hadin gwiwa da gwamnatin Carney, yayin da ya nuna godiyarsa ga kyakkyawar alakar da aka kula a tsakaninsu a zamanin tsohon Firayim Minista, Justin Trudeau.
Bello Wakili