Leadership News Hausa:
2025-05-01@00:12:20 GMT

Hasashe Kan Tarukan CPPCC Da NPC Na 2025

Published: 4th, March 2025 GMT

Hasashe Kan Tarukan CPPCC Da NPC Na 2025

Taron kwamitin ba da shawara kan harkokin siyasa na kasar Sin (CPPCC) da za a fara ranar 4 ga watan Maris, da na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin (NPC) da za a fara ranar 5 ga watan Maris, su kasance manyan taruka biyu na kasar Sin inda ake gangamin siyasa domin nazartar baya da kuma hangen gaba. Wadannan hukumomi biyu suna karkashin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, wadda ke karkashin jagorancin babban sakataren Xi Jinping.

Kwamitin CPPCC na kasa, mai mambobi 2,169, yana aiki ne a matsayin babbar hukumar da ke tafiyar da tsarin dunkulewar sassan kasar ta fuskar siyasa, wanda ke hada kungiyoyin zamantakewa daban daban mashawarta jam’iyyar. Ita kuma, majalisar NPC mai wakilai 2,977, tana aiki ne a matsayin majalisa guda, kuma babbar majalisar dokokin kasar.

Hasashen manazarta kan taruka na bana na da alaka da wani taron karawa juna sani wato “taro kan kamfanoni masu zaman kansu” wanda shugaba Xi ya karbi bakunci a ranar 17 ga watan Fabrairu, wanda ya samu halartar manyan ’yan kasuwa na kasar. A shekarar 2018 ne aka fara gudanar da irin wannan taro da ya kasance na musamman wanda ke kara wa tattalin arzikin kasar karfin gwiwa, musamman bayan dawowar shugaba Trump na Amurka a karo na biyu, wanda ya ayyana kansa a matsayin “sarkin kakaba haraji”, wanda tuni ya sanya karin harajin kashi 10 cikin 100 kan kayayyakin Sin da ke shiga kasarsa. Yanzu, hankalin mahukunta ya karkata kan yadda Sin za ta kara kuzari, da tallafawa kasuwanci da kamfanoni, da kuma mayar da martani ga manufofin cinikayya na Trump.

Ana sa ran tarukan biyu za su bayyana ajandar da za ta kara habaka ci gaba idan aka kwatanta da bara, tare da hasashen kusan kashi 5% na ci gaban GDP, da kashi 4% na GDP na gibin kasafin kudi, da kashi 2% na hauhawar farashin kayayyaki. Bugu da kari, ana sa ran za a samu karin lamuni na kusan yuan tiriliyan 3 daga asusun baitulmali na musamman da kuma yuan tiriliyan 4.5—-5 daga lamuni na musamman na kananan hukumomi. Ta hakan za a gabatar da matakan da za su bunkasa sayayya da karfafa kamfanoni cikin gida masu zaman kansu a fannin kirkire-kirkire. Kazalika, ana sa ran za a tabo batutuwan da suka shafi ci gaban kamfanonin waje masu zaman kansu, da manufofin kasashen wajen musamman wadanda suka shafi batun Taiwan da yadda za a mayar da martani ga hauragiyar Trump. (Mohammed Yahaya)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Iran Da Iraki Sun Ce An Kammala Shimfida Layin Dogo Daga Shalamcheh Zuwa Basra

A wani taro wanda ya hada ministan riko na tattalin arziki da kudade na JMI da kuma mai bawa firai ministan kasar Iraki shawara, bangarorin biyu sun tabbatar da cewa an kammala aikin shimfida layin dogo tsakanin garin Shalamcheh na kasar Iran da kuma birnin Basra a kasar Iraki.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jami’an gwamnatocin kasashen biyu na fadar haka, sun kuma jaddada muhimmancin layin dogon da kuma samar da kasuwar babu kudaden fito a kan iyakokin kasashen biyu.

Labarin ya kara da cewa harkokin kasuwanci tsakanin kasashen biyu ya zuwa yanzu ya kai dalar Amurka biliyon $11a ko wace shekara kuma anan saran nan gaba zai iyakaruwa zuwa dalar Amurka biliyon $25.

Rahmatollah Akrami, ministan riko na tattalin arziki da kudade na JMI, da kuma Hazem Majid Naji Al-Khalidi mai bawa firai ministan kasar Iraki shawara sun jaddada muhimmancin kammala layin dogo tsakanin kasashen biyu, da kuma kasuwar ba kudaden fito tsakanin kasashen biyu. Da kuma fatan zasu yi kokarin amfanar juna gwagwadon abinda zasu iya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hajj 2025: Kaduna Ta Gaddamar Da Ayarin Likitoci Da Za Su Kula Da Alhazan Jihar
  • Iran Da Iraki Sun Ce An Kammala Shimfida Layin Dogo Daga Shalamcheh Zuwa Basra
  • Cinikayyar Hidima Ta Kasar Sin Ta Matukar Bunkasa A Rubu’in Farko Na Nana
  • Abubuwan Da Na Gani A Yankin ‘Hero Bay’ Da Ke Cikin Kasar China
  • An dawo da wutar lantarki a Sifaniya da Portugal
  • Hajjin 2025: Gwamna Namadi Ya Nada Sarkin Kazaure Amirul Hajj
  • Makafi 37 Sun Zana Jarabawar JAMB A Bauchi
  • Shekara 10 ina sayar da sassan jikin ɗan Adam — Wanda ake zargi
  • Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Tattauana Da Shugaban Hukumar IAEA
  • Ma’aikata 240 na karɓar albashi biyu, wasu 217 na amfani da lambar BVN ɗaya a Kano