Masana Fasahar Gina Jiragen Sama A Iran Sun Samar Da Wata Fasahar Nano Mai Rage Nauyin Jiragen Sama
Published: 3rd, March 2025 GMT
Masu fasahar gina jiragen sama a kasar Iran sun samar da wani sinadari wanda ake kira ‘Smart Magnesium’ wanda ake iya rage nauyin jiragin sama da shi.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto masu binciken na cewa sun samar da wani sinadari wanda baya sanya ‘magnesium Alloy’ a jikin jiragen sama tsatsa, kuma idan an rufe jikin jirgi da shi zai rage nauyinsa.
Rahoton ya kara da cewa wannan kirkirar ya na da muhimmanci a kamfanonin kera jiragen sama, da kuma samar da injuna, saboda zai kara dadewar jikin jiragen sama, kafin yayi tsatsa. Har’ila yau ya kuma taimaka wajen rage nauyin jikin jirgin.
Banda haka sabon fasahar da aka gano dai, zata tsawon lokacin amfani da jikin fiye da yadda yake a yanzun. Labarin ya kammala da cewa Wannan fasahar zai taimakawa jiragen sama da kuma kumbo masu zuwa sararin samaniya.
Roqaieh Samadian-Fard, kwararre a wannan fannin ya bayyana cewa kafin haka ana samun matsalar tsatsar jikin jiragen sama da sauri, idan an kwatanda da wannan sabon sinadarin.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: jiragen sama
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Sin Za Ta Samar Da Dokar Da Ta Shafi Raya Kasa
Haka kuma za a aiwatar da dukkan abubuwan da aka dade ana yinsu cikin shirin raya kasa a hukumance.
Ana sa ran dokar za ta kara inganta tsare-tsaren da za su tabbatar da aiwatar da shirye-shiryen raya kasa da karfafa dacewar manufofin da suka shafi dukkan bangarorin tattalin arziki da juna. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp