Wasu Kasashen Musulmi Sun Fara Azumin Ramadana A Yau Asabar, Yayin Da Wasu Za Su Fara A Gobe Lahadi
Published: 1st, March 2025 GMT
Daga cikin Kasashen da su ka fara azumi a yau Asabar, da akwai Saudiyya, Katar, Hadaddiyar Daular Larabawa, Omman, Bahrain da Kuwait. Saikuma Masar, Syria, Falasdinu, Yemen, Sudan,Somaliya, Libya, Tunisa da kuma Aljeriya.
Kasar Moroko kuwa ta sanar da cewa, yau Asabar ne cikon watan Sha’aban, gobe Lahadi zai zama farkon Ramadan.
A kasar Iraki, ofishin dake kula da wuraren addini na Ahlussunnah, ya sanar da cewa, yau ne farkon Ramadan, yayin da ofishin babban marji’in shi’a Sayyid Ali Sistani ya sanar da cewa gobe Lahadi ne farkon Ramadan.
A nan Iran ma dai an sanar da rashin ganin wata a fadin sassan kasar a daren jiya Juma’a, don haka yau Asabar zai zama cikon watan Sha’aban, gobe Lahadi zai zama farkon watan Ramadana.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Tawagar Jami’ai Da ‘Yan Kasuwar Ta Tunusiya Ta Gana Da Mataimakin Shugaban kasar Iran
Tawagar jami’ai da ‘yan kasuwan kasar Tunisiya ta gana da mataimakin shugaban kasar Iran
A yayin ganawarsa da ministan kasuwanci da fitar da kayayyaki na kasar Tunisiya Samir Ben Salem Obeid, mataimakin shugaban kasar Iran na farko na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Mohammad Reza Aref ya jaddada cewa: Lokaci ya yi da za a dauki kwararan matakai wajen fadada dangantakar tattalin arziki tsakanin Iran da Tunusiya.
A yayin taron, wanda aka gudanar a ofishinsa tare da halartar jakadan kasar Tunisiya a Iran Imed Rahmouni da tawagar da ke tare da shi, Aref ya bayyana cewa, dangantakar siyasa da ke tsakanin al’ummar Iran da Tunisiya na tafiya cikin wani yanayi mai ma’ana, amma hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya ya kasance kasa da abin da ake bukata, bisa la’akari da dama da karfin da bangarorin biyu ke da shi.
A yayin ganawar, Aref ya tunatar da ziyarar da ya kai birnin Qairawan na kasar Tunusiya shekaru ashirin da suka gabata, lokacin da ya rike mukamin mataimakin shugaban kasar na farko na Jamhuriyar. Ya kara da cewa a lokacin yana jin kamar ya ratsa daya daga cikin garuruwan Khorasan na kasar Iran, yana daukar birnin Qairawan wata alama ce ta hadin kan al’ummar musulmi da alakar al’adu da addini tsakanin Iran da Tunisiya.