Uwa ta jefo jaririnta daga saman bene mai hawa biyu
Published: 24th, February 2025 GMT
Wani jariri sabuwar haihuwa ya riga mu gidan safiyar Litinin bayan mahaifiyarsa ta jefo shi ta tagar wani otel a birnin Paris. Jami’an tsaro da ke shigar da ƙara sun ce an tsinci gawar jaririn wanda ko cibiyarsa ba a yanke ba. An yi zanga-zangar kisan ɗalibi a Jami’ar FUDMA da ke Katsina NNPP ta dakatar da Kawu Sumaila da Ali Madakin Gini Wata majiya ta ce uwar jaririn mai shekaru 18 ta jefo shi ne ta tagar ɗakin wani otel daga hawa na biyu a Kudancin Faransa.
Tuni dai mahukunta a Faransa suka ƙaddamar da bincike kan lamarin yayin da suka tabbatar da cafke matashiyar da ake zargi.
An ruwaito cewa BaAmurkiyar na daga cikin tawagar wasu matasan ɗalibai da ke yawon ƙaro ilimi a nahiyar Turai.
A halin yanzu dai an kai matashiyar asibiti domin samun kulawar da ta dace a sanadiyar haihuwar da ta yi a yayin da bincike zai ci gaba da gudana.
AFP
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Makiyayi Ya Kashe Abokai 2 A Nasarawa Kan Rikicin Kiwo
Michael, wanda ke zaune a Phase 4, ya yi ƙoƙarin ceton abokinsa, amma shi ma makiyayin ya sare shi da adda.
An garzaya da Michael zuwa Asibitin Mararaba domin ceto rayuwarsa, amma likita ya tabbatar da mutuwarsa bayan isar su.
‘Yansanda sun bayyana cewa an adana gawar Michael a asibitin domin gudanar da bincike.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, ya umurci a tura jami’an tsaro domin kare rayuka da dukiya a yankin, tare da umartar Mataimakin Kwamishinan Sashen Binciken Laifuka da ya fara bincike da kuma kamo wanda ake zargi domin gurfanar da shi a kotu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp