Ya Kamata Trump Ya Yi Koyi Da Nixon
Published: 25th, February 2025 GMT
Ranar 21 ga watan Fabrairu ne aka cika shekaru 53 da shugaban kasar Amurka na lokacin Richard Nixon ya kawo ziyara kasar Sin a shekara ta 1972, ziyarar ta sauya tarihin duniya, ta kuma samar da tushen ci gaban yankin Asiya da tekun Pasifik cikin lumana. Lokacin da tunanin yakin cacar baka ya yi kamari a Amurka, Nixon ya fahimci muhimmancin jamhuriyar jama’ar kasar Sin a ci gaban Asiya da duniya baki daya.
Duk da cewa, akwai da yawa daga cikin kalaman Trump dake nuna yakininsa na cewa zai iya “sassantawa” da kasar Sin da kuma yabon da yake yi wa shugaban kasar Sin Xi Jinping, za a iya samun wata boyayyar ajanda karkashin manufar Trump fiye da kallon kasar Sin a matsayin “kishiya ko abokiyar takara”. To, idan duk harajin da ya yi barazanar kakabawa suka fara aiki, ba shakka matakin zai yi tasiri ga tattalin arzikin kasar Sin, amma zai fi yin tasiri ga mabukatan Amurka. Wasu na ganin zai iya haifar da koma bayan tattalin arziki a duniya. Kana, zai yi matukar wahala a kai ga cimma matsaya da fahimtar juna wajen tunkarar dabaru ko wasu batutuwa masu muhimmanci a tsakanin kasashen biyu idan har aka fara gasar daukar matakan da za su illata tattalin arziki. Gaskiyar lamarin ita ce, farfado da tattalin arzikin Amurka kamar yadda Trump ya yi ikirari na bukatar karin zuba jari a ababen more rayuwa na Amurka da kuma kokarin hadin gwiwa daga bangaren gwamnatin Amurka don habaka fannin kimiyya da fasaha, sai dai kash, babu dayan wadannan da ke faruwa a halin yanzu. Maslaha mafi sauri da sauki ita ce yin aiki da kasar Sin kamar yadda Nixon ya yi, ba yin adawa da ita ba. Amma fa da Trump zai gane. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Trump ya yi
এছাড়াও পড়ুন:
Tattalin Arzikin Sin Ya Samu Ci Gaba Ba Tare Da Tangarda Ba A Watan Agusta
Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar Sin ya gudanar da taron manema labarai da misalin karfe 10 na safiyar yau Litinin, inda kakakin hukumar kididdiga ta kasar, kuma babban masanin tattalin arziki, kana daraktan sashen kididdigar tattalin arziki na kasar, Fu Linghui ya yi karin haske kan ayyukan tattalin arzikin kasar cikin watan Agustan bana, tare da amsa tambayoyin manema labarai.
A cewar bayanan da aka gabatar a yayin taron, ayyukan tattalin arzikin kasar a watan Agusta sun samu ci gaba ba tare da tangarda ba. Kuma hakan ya bayyana ne ta hanyoyi daban-daban kamar haka: masana’antu sun habaka cikin sauri, masana’antar kera kayayyakin aiki da masana’antar fasaha sun samu ci gaba mai kyau. Kana ayyukan bayar da hidima su ma sun bunkasa cikin sauri. Baya ga haka, an samu ci gaba mai kyau a bangaren bayar da hidimomi na zamani. Harkokin kasuwanci sun samu ci gaba cikin natsuwa, inda harkokin sayar da kayayyaki ga masu sayayya suka kara habaka. Har ila yau, kadarorin jari sun ci gaba da karuwa, jarin masana’antu ya habaka cikin sauri, harkokin fice da shigen kayayyaki sun ci gaba da girma, tsarin kasuwanci ya ci gaba da ingantuwa, kana yanayin samar da guraben aikin yi, ya kasance kan wani mataki mai daidaito. Sai dai kuma saboda yanayin da ake ciki, adadin marasa aikin yi a birane ya karu, ma’aunin Core CPI ya ci gaba da hauhawa, kana faduwar farashin kayayyakin masana’antu ya ragu.
Bayanan sun kara da cewa, akwai bukatar lura da cewa, ana fuskantar yanayin rashin tabbas a waje, kuma tattalin arzikin kasar Sin yana fuskantar kalubale da hadari da yawa. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp