Manyan jami’an kasar Jordan sun gargadi Amurka cewa: Idan ta janyo hargitsi a Jordan, to zai mamaye dukkan kasashen yankin gaba daya

Shugaban majalisar dattijan kasar Jordan Faisal Al-Fayez ya jaddada a ranar Juma’a cewa: Ana daukar kasarsa a matsayin ginshikin zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya, yana mai cewa; Duk wani hargitsin da zai iya faruwa a kasar, zai shafi kasashen yankin baki daya, yana mai jaddada cewa: Kasashen yamma, musamman Amurka, suna da cikakkiyar masaniya game da wannan lamari.

Al-Fayez ya bayyana cewa, a cikin hirarsa da tashar talabijin ta masarautar Jordan kan manyan kalubale da kasarsa ta fuskanta a baya, amma ta yi galaba a kansu da karfi da kuma tsayin daka, tare da dogaro da muhimman abubuwa, wadanda mafi muhimmancinsu su ne tsaro da zaman lafiyarta, yana mai cewa, diflomasiyyar kasar Jordan tana da babban karfin wajen samar da daidaito, kamar yadda sarkin Jordan  Abdallah na biyu ya yi nasara a fagen gudanar da kyakkyawar alakar kasarsa da kasashen yanki da na kasa da kasa wajen nisanta hatsarori da dama.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Mutuwar majinyata: Asibitin Aminu Kano na roƙon KEDCO ya dawo da wutar lantarki

Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) ya roƙi Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na KEDCO ya gaggauta dawo masa da wuta bayan rasuwar wasu marasa lafiya da ke samun kulawa ta ceton rayuwada na’ura.

Wata sanarwa da kakakin asibitin, Hauwa Inuwa Dutse ta fitar ta nuna takaici bisa rasuwar marasa lafiyan, tana mai cewa mace-macen waɗanda za a iya kauce wa ne idan akwai tsayayyiyar wutar lantarki.

Ta bayyana cewa Asibitin yana AKTH yakan biya kuɗin wuta akai-akai daga kuɗaɗen shigansa, kuma yana kashe kuɗaɗe wajen sanya mai a janareto domin amfani idan aka ɗauke wuta daga KEDCO.

Don haka, “Hukumar gudanarwar Asibitin AKTH na roƙon Kamfanin KEDCO da ya taimaka wa ayyukan asibitin ta hanyar dawo da wutar a yayin da muke ƙoƙarin biyan ragowar kuɗin wutar,” in ji sanarwar.

Ambaliya: An gano gawar ’yar shekara 3 da ruwa ya tafi da ita a Zariya Gwamnati ta gargaɗi jihohi 11 kan yiwuwar afkuwar ambaliya a wannan makon

Ta bayyana cewa a yayin da take ƙoƙarin biyan bashin da kamfanin ke bin sa, yana da muhimmanci a fahimci cewa yanke wutar lantarki daga muhimmiyar cibiyar lafiya babbar barazana ce ga majinyata da danginsu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB
  • Tinubu bai shirya gudanar da sahihin zaɓe ba a 2027 – Buba Galadima
  • Iran da Saudiyya sun bukaci hadin Musulmi game da halin da ake ci a yankin
  • Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo
  • Ministan Tsaron Kasar venezuela Ya Gargadi Amurka Dangane Da Kokarin Juyin Mulki A Kasar
  • Pezeshkian: Ya kamata kasashen musulmi su yanke alaka da gwamnatin sahyoniya tare da kiyaye hadin kai
  • Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Dakatar Da Shuka Kiyayya Da Tashin-Tashina A Tekun Kudancin Sin
  • Ƴan Bindiga Sun Sace Malamin Krista Na Ɗarikar Katolika A Kogi
  • Dole sai mun tantance wa’azi kafin a yi —Gwamnan Neja
  • Mutuwar majinyata: Asibitin Aminu Kano na roƙon KEDCO ya dawo da wutar lantarki