Aminiya:
2025-05-01@00:52:20 GMT

Ɗan sanda ya harbe kansa har lahira a Nasarawa

Published: 5th, February 2025 GMT

Wani Jami’in Ɗan Sanda da ke aiki a ofishin ’yan sanda na yankin Mada a Jihar Nasarawa, ya harbe kansa da bindiga har lahira.

An gano ɗan sandan, mai suna Dogara Akolo-Moses, yana aiki ne a Ƙaramar Hukumar Nasarawa Eggon lokacin da ya kawo ƙarshen rayuwarsa.

’Yan sanda sun kama baƙin haure 165 a Kebbi Sarkin Jiwa a Abuja ya yi rashin mahaifiya 

Shaidu sun bayyana cewar ya shiga wani ɗaki sannan ya harbe kansa da bindiga.

Sautin harbin bindigar ne ya jawo hankalin abokan aikinsa, waɗanda suka garzaya zuwa ɗakin, inda suka same shi kwance cikin jini da bindiga a gefensa.

Har yanzu ba a san dalilin da ya sa ya hallaka kansa ba.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Nasarawa, Ramhan Nansel, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce rundunar tana gudanar da bincike don gano abin da ya sa jami’in ya ɗauki wannan mummunan mataki.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Jihar Kebbi Ta Kammala Shirye-shiryen Aikin Hajjin 2025

Hukumar Jin Daɗin Alhazai a Jihar Kebbi ta bayyana cewa ta kammala dukkan shirye-shiryen gudanar da aikin Hajjin bana a Ƙasa Mai Tsarki.

Amirul Hajji na jihar na shekarar 2025 kuma Sarkin Argungu, Alhaji Samaila Muhammad Mera, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a lokacin taron farko da aka gudanar a hedkwatar hukumar da ke Birnin Kebbi.

Ya kuma yi alkawarin tabbatar da jin daɗin mahajjatan jihar yayin da suke a ƙasa mai tsarki.

Amirul Hajjin ya bayyana cewa jimillar mahajjata 3,800 daga jihar ne suka biya kuɗin kujerunsu gaba ɗaya domin aikin hajjin bana, kuma jigilar mahajjatan za ta fara ne ranar 9 ga watan Mayu, inda ya ce da yardar Allah za a ci gaba da jigilar ba tare wani tsaiko ba har sai an kammala.

Ya kuma bayyana cewa, a wannan shekarar, za a yi wa mahajjata canjin kuɗin guzirinsu na BTA zuwa kudin Saudiyya wato riyal  kai tsaye, da nufin dakile ayyukan damfara da kuma kare mahajjata daga asarar kuɗi yayin musayar kuɗaɗe a nan gida da kuma Saudiyya.

Alhaji Muhammadu Mera ya shawarci mambobin tawagar gwamnati da jami’an hukumar jin daɗin mahajjata da su gudanar da ayyukansu bisa tsoron Allah, tare da kare haƙƙoƙin mahajjata, daidai da manufar Gwamna Nasir Idris na gudanar da sahihin aikin Hajji mafi kyau.

Shugaban Hukumar, Alhaji Faruk Musa Yaro, ya yi alkawarin bayar da cikakken haɗin kakaga tawagar gwamnati domin tabbatar da nasarar aikin Hajji da ba a taɓa irin sa ba a tarihin jihar.

Ya ce an riga an samu masauki da sauran abubuwan buƙata ciki har da sufuri da abinci a ƙasa mai tsarki, sannan kuma kamfanin jirgin samsada ya yi jigilar Alhazan jihar a shekarar da ta gabata,  wato Flynas, a bana ma shi ne zau yi jigilar mahajjatan zuwa kasa mai tsarki.

Haka kuma, an an fara yi wa Amirul Hajj da sauran mambobin tawagar gwamnati allurar rigakafi  yayin kaddamar da shirin rigakafin mahajjatan.

 

Daga Abdullahi Tukur

 

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kasar Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Najeriya Wajen Yin Watsi Da Kariyar Cinikayya Da Yin Adawa Da Danniya Da Cin Zarafi
  • Gwamnan Sokoto Ya Amince Da Sauya Wa Manyan Sakatarori 25 Ma’aikatu A Jihar 
  • Sojoji Sun Daƙile Harin ‘Yan Bindiga , Sun Ceto Fasinjoji 6 A Taraba
  • Sojoji Sun Harbe Mutane Biyu Har Lahira Da Ake Zargi Ɓarayin Mota Ne A Filato 
  • Ta yi wa saurayinta ƙaryar shekarunta 27 maimakon 47
  • Makiyayi Ya Kashe Abokai 2 A Nasarawa Kan Rikicin Kiwo
  • Jihar Kebbi Ta Kammala Shirye-shiryen Aikin Hajjin 2025
  • Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci Ta Yaba Wa Gwamna Lawal Kan Matakan Yaƙi Da ‘Yan Bindiga A Zamfara
  • Ma’aikata 240 na karɓar albashi biyu, wasu 217 na amfani da lambar BVN ɗaya a Kano
  • Iran Da Rasha Sun Jaddada Yin Aiki Tare A Fagen Kiwon Lafiya