’Yan sanda sun kama baƙin haure 165 a Kebbi
Published: 5th, February 2025 GMT
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi, ta kama wasu mutum 165 da suka shigo Najeriya ba tare da izini ba.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Nafi’u Abubakar, ya ce an kama mutanen ne a Birnin Kebbi.
Gobara ta yi ajalin almajirai 17 a Zamfara Tinubu ya ƙara kasafin kuɗin 2025 zuwa N54.2trnYa ce 35 daga cikinsu ’yan asalin ƙasar Burkina Faso ne, yayin da 11 ’yan asalin Jamhuriyar Benin ne.
Akwai kuma mutum biyar daga Nijar, huɗu daga Mali, sai mutum 110 ’yan ƙasar Ivory Coast.
Ya ce mutanen ba su da takardun izinin shigowa Najeriya kuma an same su da aikata damfara.
Rundunar ta bayyana cewa an miƙa su ga Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa da ke Jihar Kebbi, domin gudanar da bincike da kuma ɗaukar matakin da ya dace.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Najeriya Rashin Izini
এছাড়াও পড়ুন:
Ƴansanda Sun Kama Wani Mai Wasa Da Bindiga AK-47 A Cikin Wani Bidiyo A Adamawa
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar October 31, 2025
Manyan Labarai NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa October 31, 2025 Labarai Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda October 31, 2025