Aminiya:
2025-09-18@02:16:11 GMT

Tinubu ya tafi Faransa daga nan zai wuce Habasha

Published: 5th, February 2025 GMT

Shugaba Bola Tinubu a wannan Larabar ya bar Nijeriya zuwa ƙasar Faransa domin kai wata ziyara ta ƙashin kai.

Daga nan kuma Shugaba Tinubu zai wuce ƙasar Habasha inda zai halarci taron gamayyar ƙungiyar ƙasashen Afirka ta AU.

NAHCON ta tsawaita wa’adin biyan kuɗin Hajjin bana Dalilin da farashin citta ya yi tashin gwauron zabo

Mai bai wa Tinubu shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga a shafinsa na X, ya ce Tinubu zai tafi Paris ɗin ne gabanin tafiyar da zai yi zuwa Addis Ababa, babban birnin Habasha domin taron ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU).

A lokacin taron da za a yi a birnin na Addis Ababa a farkon mako mai zuwa, Shugaba Tinubu zai gana da shugabannin ƙasashen Afirka domin taron ƙungiyar da za a gudanar daga ranar 12 zuwa 16 ga watan Fabrairun 2025.

A yayin ziyararsa a Faransa, Tinubu zai gana da takwaran aikinsa na Faransa Emmanuel Macron.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Faransa

এছাড়াও পড়ুন:

An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB

Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta sanar da samun nasarar cafke Ifeanyi Eze Okorienta, wanda aka fi sani da “Gentle de Yahoo”, ɗaya daga cikin manyan kwamandojin ƙungiyar IPOB, a wani samame da ta kai a yankin kudu maso gabashin ƙasar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito wata majiya daga hedikwatar rundunar sojin tana cewa an cafke Gentle de Yahoo ne yayin farmakin da sojojin suka kai a ranar Lahadi kan sansanonin ’yan ƙungiyar a cikin wani dajin da ke ƙaramar hukumar Okigwe a Jihar Imo.

An tattauna yadda za a inganta walwalar malamai a Gombe Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a Ribas

Majiyar ta ce a yayin cafke jagoran na IPOB, an kuma ƙwato makamai da dama daga hannunsa, ciki har da bindigogi kirar Turai, harsasai, kakin sojoji da na ’yan sanda.

“Cafke wannan kwamanda babban ci gaba ne wajen murƙushe ayyukan ta’addanci da ƙungiyar IPOB ke aikatawa, musamman a yankunan da suke hana zaman lafiya,” in ji majiyar.

Kungiyar IPOB, wacce ke fafutukar ballewa daga Najeriya don kafa ƙasar Biyafara, ta kasance a gaba-gaba wajen aikata hare-hare da ta da tarzoma a jihohin kudu maso gabas, musamman ta hannun sashen rundunar da suka kafa da kansu mai suna Eastern Security Network (ESN).

Ana dai zargin cewa Eze yana ɗaya daga cikin jagororin da ke tsara harin kwantan bauna, da hana zirga-zirga a wasu sassan yankin, wanda hakan ya jefa al’umma cikin fargaba da zaman ɗar-ɗar.

Wannan nasara na zuwa ne bayan makonni kaɗan da wata kotu a ƙasar Finland ta yanke wa Simon Ekpa, wani babban jigo a ƙungiyar IPOB, hukuncin ɗaurin shekaru shida a gidan yari kan laifukan da suka shafi ta’addanci da tayar da zaune tsaye.

Masu sharhi na ganin cewa cafke Gentle de Yahoo wata alama ce da ke nuna cewa ana shirin ragargaza ƙungiyar IPOB gaba ɗaya, duk da cewar har yanzu akwai sauran rina a kaba, musamman ganin cewa wasu sassan yankin na ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Karamar Hukumar Malam Madori Ta Horar Da Mata Kare Kai Daga Cututtukan Mahaifa
  • Yawan Kadarorin Kamfanoni Mallakar Gwamnatin Sin Ya Wuce Yuan Triliyan 90 a Lokacin Shirin Raya Kasa Na 14 Na Shekaru 5 
  • An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB
  • Yanzu-yanzu: Shugaba Tinubu Ya Ɗage Dokar Ta-ɓaci A Jihar Ribas
  • Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Hutun Sati 2 A Ƙasar Faransa
  • Sin Ta Daga Zuwa Mataki Na 10 A Jadawalin GII Na Kasashen Dake Kan Gaba A Fannin Kirkire-Kirkire
  • An Fara Taron Hukumar Makamashin Nukliya Ta Duniya IAEA Karo Na 69 A Birnin Vienna
  • Taron Doha: Daga matakin Allawadai zuwa matakan kalubalantar laifukan Isra’ila
  • Jami’in Kasar Yemen Ya Aike Da Sako Ga Mahalarta Taron Birnin Doha Na Kasar Qatar
  • Barcelona Ta Farfaɗo Zuwa Matsayi Na Biyu Bayan Lallasa Valencia A Johan Cruyff