’Yan bindiga sun kashe mutum 3 sun sace 24 a Zamfara
Published: 31st, January 2025 GMT
’Yan bindiga sun kashe mutane uku tare da yin garkuwa da wasu 24 a wasu jerin hare-hare a wasu kauyuka hudu a Ƙaramar Hukumar Shinkafi da ke Jihar Zamfara.
’Yan ta’adan sun kai hare-haren ne ranar Alhamis, a ƙauyukan Shinkafi da Jangeru da Shanawa da Birnin Yero.
A garin Shinkafi, ’yan bindigar sun kashe mutum uku tare da yin garkuwa da wasu tara, ciki har da mata hudu.
Mazauna garin sun bayyana cewa maharan sun bude wuta kan mai uwa da wabi, lamarin da ya haifar da fargaba.
Direba cikin barasa ya murƙushe sojoji sun mutu a Legas Ya tona kabarin mijin mahaifiyarsa ya yanke kansaA kauyen Birnin Yero, ’yan bindiga sun kai hari a wani masallaci a lokacin sallar magariba, suka yi awon gaba da mutane takwas tare da raunata wasu da dama wadanda suka tsere zuwa cikin daji.
Sun kuma kai hari kauyen Shanawa, inda suka sace mutane hudu. Wannan harin ya faru ne kwana guda bayan an sako wasu mazauna kauyen guda 12 bayan an biya kudin fansa naira miliyan 12.
A Jangeru, an yi garkuwa da wata mata amma daga baya aka yi watsi da ita a cikin daji bayan da ’yan bindigar sun tabbatar ba za ta iya ci gaba da tafiya ba.
Wani mazaunin garin ya bayyana cewa sun sumar da ita ne, sai daga bisani ta dawo hayyacinta ta koma kauyensu.
’Yan ta’addan sun kuma gargadi mazuna kauyukan Kwari da Kurya, inda suka bai wa mazauna kauyukan wa’adin kwanaki uku su fice daga gidajensu ko kuma su fuskanci farmaki.
Sai dai mazauna kauyen Kurya sun sha alwashin yin fito-na-fito da wannan barazana, inda suka bayyana cewa sun gaji da biyan haraji da kudin fansa.
Sun kuma yi kira ga gwamnati da ta kara yawan jami’an tsaro domin taimaka musu wajen kare kansu daga hare-hare a nan gaba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Garkuwa Zamfara
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji sun daƙile hari, sun kashe mayaƙan Boko Haram 9 a Borno
Dakarun Operation Haɗin Kai da ke Arewa maso Gabas, sun ɗakile wani sabon hari da mayaƙan Boko Haram suka kai a Jihar Borno.
Sun kai harin ne yankunan Konduga, Bama da Gwoza.
Shugaban hukumar zabe ta jihar Bauchi ya rasu Adadin Falasdinawan da Isra’ila take kashewa a Gaza yanzu ya haura 60,000’Yan ta’addan sun yi yunƙurin tarwatsa gadar da ke kan hanyar Marte zuwa Dikwa ta hanyar dasa bama-bamai.
Amma sojoji sun gano abubuwan fashewa guda 17 da suka dasa a ƙarƙashin gadar kuma suka cire su.
A yayin daƙile harin, sojoji sun kashe ’yan ta’addan Boko Haram guda tara, sannan sun ƙwato bindigogi ciki har da AK-47 da bindigar PKT.
Kakakin rundunar sojin a Maiduguri, Kyaftin Reuben Kovangiya, ya ce dakarun na ci gaba da kai farmaki da sanya ido kan ayyukan ‘yan ta’addan a yankin.
Ya ce wannan nasarar na nuna cewa sojoji sun ƙudiri aniyar hana ’yan Boko Haram da ISWAP aikata ta’addanci.
Rundunar sojin ta roƙi jama’a da su ci gaba da bayar da haɗin kai ta hanyar bayar da rahoton motsin duk wani mutum da suke zargi yana da alaƙa da ’yan ta’adda ga jami’an tsaro.