Leadership News Hausa:
2025-06-15@13:43:53 GMT

Ko Jam’iyyun Adawa Na Iya Kai Bantensu A 2027?

Published: 31st, January 2025 GMT

Ko Jam’iyyun Adawa Na Iya Kai Bantensu A 2027?

A kwanakin baya, jam’iyyar PDP da sauran jam’iyyun adawa sun zargi APC da ruruta wutar rikicin da ke tsakaninsu, inda suka yi zargin cewa jam’iyya mai mulki na neman murkushe ‘yan adawa domin tabbatar da ci gaba da mulkin Shugaba Tinubu a 2027. APC ta musanta wadannan ikirari.

Tun da aka hambarar da jam’iyyar PDP, jam’iyyun adawa sun yi yunkuri da dama amma ba su samu nasara ba.

Na baya-bayan nan shi ne samar da wata sabon jam’iyyar siyasa mai suna ‘The Alternatibe’, domin tabbatar da madafun iko a babban zabe na 2027. Wani tsohon dan takarar shugabancin jam’iyyar PDP na kasa, Segun Sowunmi, wanda ke tallata wannan sabuwar jam’iyyar, ya ce an kafa jam’iyyar ne saboda ‘yan Nijeriya sun gaji da tsarin siyasar da ake da su, suna kuma neman hanyar da ta dace.

Kafin wannan, a shekarar 2018, jam’iyyar PDP ta kulla kawance da wasu jam’iyyun siyasa 38, inda suka sanya mata suna ‘Coalition of United Political Parties’ (CUPP) a wani taro da aka gudanar a cibiyar Musa Yar’adua da ke Abuja. Wannan gamayyar dai ta yi nufin kayar da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyar APC a zaben 2019. Shugabannin jam’iyyun ADC, SDP, NCP, LP, da sauran jam’iyyu da dama da suka yi rajista sun halarci taron.

Sai dai kawancen ta kasa hana Buhari sake lashe zabe, saboda rashin kokarin habaka dimokuradiyya na samun goyon bayan ‘yan Nijeriya.

A ranar 6 ga Disamba, 2023, PDP, NNPP da wasu jam’iyyun siyasa biyar suka kafa sabuwar kawance. Jam’iyyun da abin ya shafa sun hada da ADC, APM, SDP, YPP da ZLP.

Wannan sabon yunkuri mai suna ‘Coalition of Concerned Political Parties’ (CCPP), an kafa shi ne a sakatariyar jam’iyyar SDP ta kasa da ke Abuja. Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya bukaci jam’iyyun adawa da su hada kai a yunkurin kwace mulki daga hannun APC.

A ranar 12 ga Disamba, 2024, jam’iyyar PRP ta tabbatar da cewa ta fara tattaunawa da jam’iyyar ADC gabanin zaben 2027.

Shugaban jam’iyyar PRP na kasa, Falalu Bello ya tabbatar da tattaunawar a wani taron manema labarai na hadin gwiwa da shugaban ADC, Ralph Nwosu a Abuja. Bello ya jaddada cewa, “Mun fara tattaunawa. Ba ma tsoron hadewa kwata-kwata. Jam’iyyar PRP ita ce jam’iyyar siyasa mafi dadewa a yau, kuma muna da tarihin kawance da suka samu nasara.”

Ana ta rade-radin cewa za a raba madafun iko tsakanin Atiku, Kwankwaso da Obi, inda Atiku zai yi mulki na tsawon shekaru hudu, sai kuma Kwankwaso na wasu shekaru hudu, da Obi na tsawon shekaru takwas. Sai dai a kwanakin baya Kwankwaso ya musanta wanzuwar irin wannan yarjejeniya, inda ya bayyana hakan a matsayin kage.

Shi ma ya musanta wata tattaunawa na hadewa ko yarjejeniyar siyasa da PDP, NNPP ko wata jam’iyya.

Wani mai sharhi kan harkokin siyasa, Jackson Lekan Ojo, ya yi imanin cewa jam’iyyun adawa za su iya kayar da Tinubu a 2027 idan suka yi amfani da dabaru irin na APC kafin zaben 2015. Ojo ya kara da cewa akwai batutuwa da dama a karkashin wannan gwamnati da ‘yan adawa za su iya cin gajiyarsu, da suka hada da kalubalen tsaro, tabarbarewar tattalin arziki, da kuma cin hanci da rashawa.

“Idan har jam’iyyun adawa suka hada kai suka mayar da hankali kan gazawar gwamnati mai ci, musamman matsalar tsaro da tabarbarewar tattalin arzikin kasar, za su iya samun nasara. Abu mai muhimmancin shi ne, a zakulo dan takara mai karfi wanda zai iya hada kan ‘yan adawa tare da gabatar da sahihin zabi,” in ji Ojo.

Daraktan makarantar nazarin zamantakewar siyasa ta Abuja, Dakta Sam Amadi ya yi imanin cewa hadewar jam’iyyun adawa za ta iya yin nasara idan har shugabannin ‘yan adawa suka kuduri aniyar cimma wata manufa ta ci gaban kasa tare da ajiye muradun kashin kai.

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: tabbatar da

এছাড়াও পড়ুন:

Yarima Mai Jiran Gadon Saudiyya Ya Jaddada Goyon Bayan Kasarsa Ga Iran

Yarima mai jiran gadon Saudiyya ya tabbatarwa shugaban kasar Iran cewa: Saudiyya tana goyon bayan Iran

Yariman mai jiran gadon Saudiyya Mohammed bin Salman ya tabbatar da hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian a yammacin jiya Asabar, yana mai jaddada cewa: Masarautar Saudiyya da daukacin al’ummar musulmin duniya sun hadu a kan goyon bayan Iran.

Yarima mai jiran gadon sarautar Saudiyya ya ce: Dukkanin al’ummomin kasashen musulmi a yau suna da hadin kai da jaddada goyon bayansu ga Iran, kuma yana iyaka kokarinsa a fagen diflomasiyya da matsin lamba na kasa da kasa don dakatar da wuce gona da irin da ‘yan sahayoniyya suke yi kan Iran.

Bin Salman ya yi Allah wadai da hare-haren rashin adalci da ‘yan sahayoniyya suke kaiwa Iran.

Ya kuma bayyana jimaminsa tare da jajantawa al’ummar kasar Iran dangane da wadannan hare-hare da suka rutsa da su, yana mai jaddada cewa: Saudiyya tana da tabbataccen matsayi kan tsayawa tare da ‘yar uwarta Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kuma duniyar musulmi a yau ta hade kan muryar daya wajen goyon bayan Iran.

Ya ci gaba da cewa: “Mun yi imanin cewa, gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila na neman ta hanyar kara kunna wutar rikici ta janyo Amurka a cikin tsakiyar rikici, amma suna da yakinin cewa martanin Iran a kan ma’aunin daidaito da matakan hankali zai dakile wannan  yunƙurin makirci.”

Bin Salman ya kuma jaddada cewa: Kasarsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen bayar da duk wani tallafi da ya dace ga ‘yan uwanta Iran.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yarima Mai Jiran Gadon Saudiyya Ya Jaddada Goyon Bayan Kasarsa Ga Iran
  • Martanin sojojin Iran ga Isra’ila zai zama mafi muni idan aka ci gaba da kai hari (Pezeshkian)
  • Arakci: Babu Wani Dalili Na Ci Gaba Da Tattaunawa Tsakanin Iran Da Amurka
  • Dimokuradiyya A Shekara 26: Ba Yabo Ba Fallasa
  • Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin Fadar Shugaban Kasa Da Peter Obi Kan Tallafin Mai
  • Sarkakiyar Da Ke Tattare Da Zaben 2027 Da Yadda Za Ta Kaya
  • Sin Ta Bayyana Adawa Da Keta Hurumin ‘Yanci Tsaro Da Ikon Mulkin Yankunan Iran
  • Mayar da Nijeriya tsarin jam’iyya ɗaya ba ya cikin manufofinmu — Tinubu
  • Iran ta caccaki kudurin IAEA wanda ta ce yana cike da siyasa
  • Ba Zan Bar Nijeriya Ta Zama Kasa Mai Jam’iyya Daya Ba – Tinubu