Direba cikin barasa ya murƙushe sojoji sun mutu a Legas
Published: 31st, January 2025 GMT
Wasu sojoji da har yanzu ba a tantance adadinsu ba sun mutu yayin da wasu suka samu raunuka bayan da wani da ake zargin wani direba da ya bugu cikin barasa ne ya kutsa cikin su a yankin Shomolu da ke Jihar Legas.
Lamarin ya faru ne ’yan mintuna kaɗan bayan da sojojin suke kan hanyarsu daga Barikin Myoung da ke yankin Marocco a Shomolu.
Waɗanda suka samu raunuka suna jinya a asibitin sojojin Nijeriya da ke Yaba, yayin da aka ajiye gawarwakin sojojin da suka rasu a ɗakin ajiye gawa a asibitin.
Hedikwatar Runduna ta 81 ta Sojojin Nijeriya, ta sanar a ranar Alhamis cewa za ta fara gudanar da tattakinta a yankin na farko, na kowace shekara a yau Juma’a.
Tattakin mai tsawon kilomita 15, wanda aka dakatar sakamakon wannan mummunan al’amari, ya kamata ya ratsa sassan babban yankin da tsibirin Legas.
Sanarwar ta kuma gargaɗi mazauna yankin da su kwantar da hankulan su domin tattakin da aka saba yi na atisayen soji ne.
Wata majiyar soji ta ce motar ta kutsa cikin taron sojojin, inda ta kashe wasu daga cikin su nan take.
Majiyar ta kuma bayyana cewa, tun daga lokacin aka kama direban.
Sai dai majiyar ba ta bayyana inda ake tsare da mutumin domin amsa tambayoyi ba.
Wani ganau ya ce, “Tattakin hanyar ya tsaya kwatsam sakamakon lamarin. Ba zan iya bayar da cikakken bayani kan adadin waɗanda suka mutu ba, amma sojoji da dama sun samu munanan raunuka yayin da wasu ’yan ƙalilan suka mutu.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yaba
এছাড়াও পড়ুন:
Ƴan Bindiga Sun Sace Malamin Krista Na Ɗarikar Katolika A Kogi
Haka kuma, wannan na faruwa ne makonni biyu bayan yin garkuwa da Pastor Friday Adehi na Christian Evangelical Fellowship of Nigeria (CEFN) tare da wani abokin cocinsa bayan kammala wa’azi. Wannan ya kara nuna yadda matsalar garkuwa ke ta’azzara a yankin Kogi East.
A gefe guda, kungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA), reshen Idah, ta bukaci gwamnati a matakai daban-daban da ta dauki matakan gaggawa don kawo karshen satar mutane a jihar. Shugaban kungiyar, Barr. James Michael, ya ce yawaitar garkuwa a kan titunan yankin ya jefa rayukan jama’a cikin hatsari, don haka gwamnati ya kamata ta dauki tsauraran matakai domin kare lafiyar al’umma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp