Tiktok Ya Yi Hadin Gwiwa A Kenya Don Bunkasa Tattalin Arziki Mai Nasaba Da Kirkire Kirkiren Jama’a
Published: 31st, January 2025 GMT
Dandalin sada zumunta na TikTok ya sanar da hada gwiwa da kamfanin tallace-tallace ta kafofin zamani na Aleph Holdings da dandalin sayayya kan intanet na kasar kenya wato Wowzi, wanda ake sa ran zai bunkasa tattalin arziki mai nasaba da kirkire-kirkiren jama’a a kasar Kenya.
Carl Jordon, shugaban sashen tallace tallace da harkokin cinikayya a yankin kudu da hamadar Sahara na kamfanin TikTok, ya shaidawa manema labarai a Nairobi cewa, hadin gwiwa da kamfanin Aleph holdings zai saukakawa harkokin kasuwanci a kasar wajen tallata kayayyaki da hidimominsu a kan dandalin wallafa bidiyo na wayar salula.
Ya ce hadin gwiwar ya nuna kudurin TikTok na karfafa muhallin kirkire-kirkire na jama’a a cikin gida ta hanyar tabbatar da masu basira sun samu kyakkyawan sakamako. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Da Rasha Sun Jaddada Yin Aiki Tare A Fagen Kiwon Lafiya
Ministan kiwon lafiya na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Muhammad Ridha Zafarqandi ya tattauna hanyoyin bunkasa aiki tare a fagen kiwon lafiya da mataimakin ministan kiwon lafiya na tarayyar kasar Rasha.
Ministan na Iran dai ya yi wannan trattaunar ne a jiya Lahadi inda su ka tabo fagage da dama da su ka yi tarayya akansu a cikin harkar kiwon lafiya.
Ministan na Iran ya kuma ce, a baya kasashen biyu sun cimma yarjejeniya wacce a wannan lokacin ake son bunkasa ta.
Muhammmad Ridha Ya kuma bayyana yadda kasashen biyu suke da kayan aiki masu yawa a fagagen magance cutuka masu yaduwa da wdanda ba su yaduwa haka nan kuma fagen yin magunguna.
Shi kuwa mataimakin ministan kiwon lafiyar na tarayyar Rasha Olog Silgy ya tabbatar da cewa,kasarsa a shirye take ta bunkasa aiki da jamhuriyar musulunci ta Iran a fagen musayar dalibai da kuma nazarce-nazarce da bincike na ilimin likitanci.
Kasashen biyu sun kafa kwamitin hadin gwiwa na yin fada da cutuka masu yaduwa da zai taka rawa mai girma wajen magance cutuka.