Tsohon Shugaban Google: Deepseek Ya Kawo Muhimmin Sauyi A Bangaren AI
Published: 30th, January 2025 GMT
Tsohon shugaban kamfanin Google Eric Schmidt, ya bayyana bullar kamfanin DeepSeek na Sin a matsayin wadda ta kawo muhimmin sauyi ga takara a fagen kirkirarriyar basira ta AI a duniya.
Wannan na kunshe ne cikin wani sharhi da jaridar Washington ta wallafa ranar Talata, inda Eric Schmidt ya jaddada cewa, karfin Sin na yin takara da manyan kamfanonin fasaha ba tare da amfani da albarkatu mai yawa ba, ya nuna bukatar da Amurka ke da ita ta karfafa karfinta a bangaren.
DeepSeek kamfanin Sin ne dake mayar da hankali kan kirkirarriyar basira ta AI, wanda aka kafa a shekarar 2023. A cikin wannan watan na Junairun, kamfanin ya fitar da sabon samfurin AI mai suna DeepSeek-R1, wanda ya ja hankali sosai saboda kaifin basirarta. Aikin wannan sabon samfurin AI ya kai matsayin takara da tsare-tsaren AI kamar su ChatGPT na OpenAI, kuma an samar da shi ne kan farashi mai rahusa da bai kai na abokan takararsa ba.
Kaddamar da DeepSeek-R1 ya girgiza masa’antar fasahar zamani, lamarin da ya haifar da saukar farashin hannayen jari manyan kamfanonin fasaha kamar Microsoft da Meta da Nvidia. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Gano Wani Dutse Mai Sassaka Na Daular Qin A Kan Tsaunin Qinghai-Tibet
Hukumar kula da al’adun gargajiya ta kasar Sin ta sanar a yau cewa, an gano wani dutsen da aka yi sassaka kan sa a kan tsaunin Qinghai-Tibet, wanda ya kasance irinsa daya tilo na daular Qin da har yanzu ke mazauninsa na asalin, kuma a wuri mafi tsawo.
Dutsen wanda ke arewacin bakin tabkin Gyaring na gundumar Maduo, dake arewa maso yammacin lardin Qinghai, na wuri mai tsawon mita 4,300.
Gano dutsen na tattare da wata muhimmiyar daraja ga tarihi da fasaha da kimiyya. Sarki Qinshihuang na daular Qin ne ya fara hada kan kasar Sin. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp