Mutum 20 sun rasu a hatsarin jirgin sama a Sudan ta Kudu
Published: 29th, January 2025 GMT
Aƙalla mutane 20 ne ska rasu a wani hatsarin jirgin sama da ya auku a Jihar Unity da ke Sudan ta Kudu.
Rahoton gidan rediyon Miraya, na tawagar Majalisar Ɗinkin Duniya da ke ƙasar, ya bayyana cewa jirgin ya yi hatsari ne jim kaɗan bayan tashinsa daga wata rijiyar mai a Unity, inda ya ɗauki hanyarsa ta zuwa babban birnin ƙasar, Juba.
Jirgin yana ɗauke da fasinjoji 21 da kuma ma’aikatan jirgin lokacin da hatsarin ya auku.
Rahotanni sun tabbatar da cewa matuƙin jirgin ya rasu, yayin da mutum ɗaya kacal ya tsira da ransa, sai dai yana cikin mawuyacin hali.
A baya-bayan nan, hatsarin jiragen sama ya ƙaru a Sudan ta Kudu, musamman sakamakon rashin isassun kayan fasaha da kuma matsalolin tsaro a filayen jiragen sama.
A shekarar 2018, wani jirgin sama mai ɗauke da fasinjoji 19 ya faɗi a yankin Yirol, inda mutum 17 suka rasu.
Gwamnatin Sudan ta Kudu, ta sha alwashin yin bincike kan wannan hatsari da kuma ɗaukar matakan da suka dace don rage irin waɗannan haɗura a nan gaba.
A halin yanzu, hukumomi na ci gaba da bincike domin gano musabbabin aukuwar wannan hatsari.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yan Ta’adda Sun Hallaka Mutum 8 Da Bam A Borno
Wata majiya kuma ta bayyana cewa adadin mutanen da suka mutu na iya fin haka, duba da yawan mata da yara da lamarin ya rutsa da su.
A lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomin soji da ‘yansanda ba su fitar da wata sanarwa ba dangane da lamarin ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp