An dakatar da Max Air na tsawon wata 3 bayan hatsari a Kano
Published: 29th, January 2025 GMT
Gwamnatin Tarayya, ta dakatar da zirga-zirgar jiragen Max Air na tsawon wata uku, bayan ɗaya daga cikin jiragen kamfanin, tayarsa ta yi bindiga yayin sauka a filin jirgin saman Malam Aminu Kano a daren ranar Talata.
Jirgin Max Air ƙirar Boeing 734 mai lamba 5N-MBD ne ya samu matsalar kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Dukkanin fasinjoji 53 da ke cikin jirgin sun kuɓuta cikin ƙoshin lafiya.
Wannan shi ne karo na uku da jirgin Max Air ke fuskantar matsala cikin watanni uku da suka gabata.
Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Ƙasa (NCAA), ta sanar da dakatarwar domin bai wa kamfanin damar sake duba yanayin aikinsa, yayin da Hukumar Binciken Haɗuran Jiragen Sama (NSIB), ta fara bincike kan lamarin.
Daraktan Harkokin Jama’a da Kare Haƙƙin Fasinjoji na NCAA, Michael Achimugu, ya yi ƙarin haske kan lamarin.
Ya ce, “Za mu iya gano musababbin wannan hatsari ne kawai bayan binciken NSIB, amma dole ne mu ɗauki matakan kariya don tabbatar da tsaro.”
Ya ƙara da cewa, “A lokacin dakatarwar watanni uku, NCAA za ta gudanar da cikakken bincike kan tsaro da kuma ƙarfin tattalin arziƙin Max Air.
“Kamfanin jirgin zai iya ci gaba da zirga-zirga ne kawai idan ya cika dukkanin sharuɗan da ake buƙata.”
NCAA ta nemi afuwar fasinjojin da wannan mataki zai shafa, amma ta jaddada cewa lafiyar fasinjoji ita ce abin da yafi muhimmanci a wajenta.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ababen fashewa dakatarwa fashewa Hatsari Jiragen sama Taya
এছাড়াও পড়ুন:
Sojojin HKI Sun Ci Gaba Da Kashe Kawunansu
A cikin kwanakin bayan nan ana samun karuwar sojojin HKI da suke kashe kawunansu saboda tabuwar kwakwalensu sanadiyyar yakin Gaza.
Kafafen watsa labarun HKI sun kunshi rahotanni da suke bayani akan yadda sojojin mamayar da su ka yi yaki a Gaza, suke samun tabuwar hankali, da hakan yake sa su kashe kawukansu bayan sun baro Gaza.
Wasu rahotannin sun ambaci cewa, sojojin na HKI suna rayuwa ne a cikin tsaro da ranaza saboda munanan ayyukan da su ka aikata marasa kyau.