Ƴan Bindiga Sun Sace Mutum 4 Ƴan Gida Ɗaya A Abuja
Published: 28th, January 2025 GMT
Rundunar ƴansandan Abuja, ta bayyana cewa rashin samun labarin lamarin da wuri ne ya kawo jinkirin ɗaukar mataki.
Mun Fara Bincike – ƳansandaKakakin rundunar ƴansandan Abuja, Josephine Adeh, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce tuni suka fara bincike domin ceto waɗanda aka yi garkuwa da su.
Ta ce: “Ƙarfe 1 na dare muka samu kiran gaggawa cewa ƴan bindiga sun kai hari Chikakore.
Ta kuma ce wata maƙwabciyarsu da ta yi ƙoƙarin taimaka musu ta ji rauni, kuma tana karɓar magani a asibiti.
Rundunar ta buƙaci mazauna yankin su kwantar da hankalinsu tare da bayar da haɗin kai wajen bincike.
Fargaba Kan Matsalar Tsaro a AbujaWannan harin ya jefa tsoro a zukatan mazauna yankin, musamman waɗanda suka sha fama da matsalolin tsaro a baya.
A farkon watan nan, wasu ƴan bindiga da ake sun tayar da abun fashewa a wata makarantar Islamiyya a ƙauyen Kuchibuyi, Bwari, inda mutane biyu suka rasa rayukansu.
Yankin Bwari, wanda ke maƙwabtaka da jihohin Kaduna da Neja, ya sha fama da hare-haren ƴan bindiga, ciki har da sace mutane domin neman kuɗin fansa.
Wannan ya sa mazauna yankin ke fargabar dawowar zaman ɗar-ɗar a rayuwarsu.
কীওয়ার্ড: Hari Yan bindiga
এছাড়াও পড়ুন:
An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano
Mai shari’a Dahiru ya amince da buƙatar, ya kuma ɗage shari’ar zuwa ranar 12 ga watan Disamba, 2025, domin ci gaba da sauraron shari’ar.
Ƙuli-ƙuli dai nau’in abin ci ne mai taushi da ake yi da gyaɗa, ana soyawa har sai ya zama ƙura-ƙura ta yadda za a ci cikin nishaɗi.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA