Ana Bikin Zagayowar Ranar Aiko Da Manzon Tsira (SAW)
Published: 28th, January 2025 GMT
Yau Talata ana bikin tunawa da aiko ma’aiki tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa wato Yaumil Mab’as.
Ranar Mab’as 27 Ga Rajab rana ce ta murna da farin ciki saboda saukar Mala’ika Jibril (a.s) a kogon Hira dauke da sakon ayoyin farko na Kur’ani zuwa ga (Annabi) Muhammad ibn Abdullah (s.
a.w) a lokacin yana dan shekara 40.
Babbar manufar gudanar da wannan biki ita ce tunawa da ranar aiko manzon Allah Nuhammad (SAW), wanda ya zo wa dan adam da sako tsira daga halaka da kuma fita daga duhun kafirci da jahilci.
Manzon Allah (SAW) ya kasance mutum na musamman a cikin larabawa, wanda dukkanin al’ummar da ke tare da shi ta yi masa shedar gaskiya da rikon amana da karamci da kuma girmama jama’a, wadanda suka girme shi da ma wadanda ya girma.
Allah madaukain sarki ya aiko da sako zuwa ga bil adama, wanda ya zama sanadin shiririyar jama’a da dama a lokacinsa, mafi yawan wadanda suka muslunta tare da manzon Allah a Makka sun musulunta ne sakamakon kyawawan dabi’unsa, kamar yadda da dama daga cikin wadanda suka muslunta a Madiana bayan hijira sun karbi muslunci ne sakamakon kyawawan dabi’u da suka gani tare da manzon Allah, wadanda addinin ke koyar da dan Adam.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Bom Da Ya Tashi A Arewa Maso Gabashin Najeriya Ya Kashe Mutane 6
Wani bon kirar hannu da aka dasa akan hanyar dake hada Rann da Gamboru a jihar Borno ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 6.
Daga cikin wadanda su ka rasa rayukansu sanadiyyar tashin bom din sun hada mata da kananan yara kamar yadda majiyar ‘yan sanda ta sanar.
Kungiyar nan mai suna; gwamnatin musulunci a yammacin Afirka ce ta sanar da daukar alhakin kai hari na ranar Litinin din da ta gabata.
Bugu da kari sauran wadanda su ka rasa rayukan nasu manoma ne da suke cikin motar a-kori-kura da ta taka nakiya.
Baya ga wadanda su ka rasa rayukansu, wasu mutanen su 3 sun jikkata,kuma tuni an dauke su zuwa asibiti domin yi musu magani.
Wani dan sintiri da yake aiki da rundunar fararen hula masu taimakawa jami’an tsaro, Abba Madu, ya shaida wa manema labaru cewa; Da alamu an dasa bom din domin ya tashi da jami’an tsaro da suke yin sintiri akan wannan hanyar.
Kungiyoyin ‘yan ta’adda sun saba dasa irin wadannan nakiyoyin da bama-baman akan hanyar da jami’an tsaro suke bi.
Kungiyar nan da take kiran kanta; Gwamnatin Musulunci a yammacin Afirka wacce a takaice ake kira; “ISWAP” ce ta dauki nauyin kai harin.
Tun a 2009 ne yankin Arewa maso gabashin kasar ta Najeriya yake fama da matsalar kungiyoyi masu dauke da makamai da su ka hada Bokoharam, sannan kuma daga baya waje 2016, kungiyar gwamnatin musulunci a yammacin Afirka.