Najeriya ce ƙasa ta biyar mafi yawan Musulmai a duniya
Published: 7th, September 2025 GMT
Wasu cibiyoyin bincike na Pew Research da CIA World Factbook sun tabbatar da cewa Najeriya ce ƙasa ta biyar mafi yawan Musulmai a duniya, inda ƙasar ke da Musulmai kimanin mutane miliyan 124.
Ƙididdigar ta waɗannan cibiyoyi ta nuna Musulunci na ci gaba da zama addini na biyu mafi girma a duniya, wanda yawan mabiyansa suka kai kusan mutane biliyan 2.
Ƙasar Indonesia ce ke kan gaba da Musulmai miliyan 242, sai kuma Pakistan mai miliyan 235. Sai kuma ƙasar India da miliyan 213 sa’annan kuma Bangladesh da miliyan 150. Daga nan kuma sai Najeriya wacce ta biyo su da mutane miliyan 124.
Tarihi ya nuna cewa Musulunci ya fara shigowa Najeriya tun daga ƙarni na 11 ta hanyoyin kasuwanci na ‘trans-Sahara’ daga Arewaci da kuma Yammacin Afirka.
Sai kuma a ƙarni na 19, an kafa Daular Musulunci ta Sakkwato wacce ta ƙara jaddada addinin Musulunci musamman a yankin Arewacin ƙasar.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Kundin Bajinta na Guinness ya taya Hilda Baci murna
Fitacciyar mai girkin nan, Hilda Effiong Bassey, wadda aka fi sani da Hilda Baci, ta sake kafa tarihi a duniya ta hanyar girka tukunyar dafa-dukar shinkafa mafi girma bayan shafe awa takwas tana girkin.
Hakan dai na ƙunshe ne cikin wani saƙon taya murna da Kundin Bajinta na Guinness ya wallafa a shafukan sada zumunta.
Peter Obi ya kai wa Obasanjo ziyara ’Yan sanda sun sasanta rikicin asibitin AKTH da KEDCOHilda Baci dai ta dafa shinkafa dafa-duka mafi yawa a tarihi tare da sauran kayan haɗi da sunadaran ɗanɗano wadda nauyinta ya kai kilo 8,780 a yankin Victoria Island da ke Legas.
A shekarar 2023 Hilda mai shekaru 28 ta shiga Kundin Bajinta na Guiness World Record bayan shafe awa 93 da mintuna 11 tana girke-girken abinci iri-iri.
A wannan karon, Hilda ta girka ƙananan buhuna 200 na shinkafa wanda nauyinsu ya kai kilo 4,000 da katan 500 na tumatir da kilo 600 na albasa da sauran kayan haɗi.
An gudanar da zaman girkin a fili a cikin birnin kasuwanci na Legas, lamarin da ya ja hankalin ɗaruruwan masu kallo.
Dafa-dukar shinkafa wadda a wasu harsunan ake kira Jollof rice abinci ne da ake sha’awa sosai a yankin Yammacin Afirka, inda ƙasashe kamar Nijeriya, Ghana, Senegal, Kamaru, da Gambiya ke da’awar cewa su ne ke da mafi ƙwarewa a wurin girka ta.
A shekarar 2023, Hukumar Ilimi, Kimiyya, da Al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO) ta amince da Senegal a matsayin wurin da wannan abinci na dafa-dukar shinkafa ta samo asali.