Ranar Hausa Ta Duniya: Ba Ka Iyawa Duk Dagewarka Kuma Ba A Yaba Maka
Published: 26th, August 2025 GMT
Na yi imani babu rayuwa ba tare da harshe ba, domin duk wata al’umma tana da buƙatar harshe domin gudanar da rubuce-rubuce, kimiyya da fasaha.
Amma an yi sakaci da nazarin harshen Hausa, duk da cewa yana cikin manyan harsunan duniya masu ƙarfi da adabi.
Don haka zan fara bayyana matsalolin, sannan in kawo shawarwari.
Idan gwamnati da manyan al’umma ba su ɗauki Hausa da muhimmanci ba, ba zai samu ci gaba ba. An taɓa samun shugaban ƙasa da ya ce nazarin wasu darusa ɓata lokaci ne, amma shi kansa a lokacin yaƙin neman zaɓe da Hausa yake magana.
Gwamnati ta nuna rashin kulawa da harshen Hausa, tana ganin ba shi da amfani. Alal misali:
1. Mayar da Hausa “zaɓi” a sakandire.
2. Tsaurara sharuɗa wajen shiga jami’a domin nazartarsa.
3. Rashin bayar da tallafin karatu kamar yadda ake yi wa wasu harsuna.
Matsala ta biyu: Ka Ƙi Naka, Duniya Ta So ShiDa yawa daga cikin Hausawa ba sa alfahari da harshensu. Maimakon su zurfafa a kansa, sai ƙasashen waje suka ɗauki Hausa suna koyarwa a jami’o’in duniya. Haka kuma, yawancin Hausawa idan suna amfani da shafukan sada zumunta, rubuce-rubucensu da Hausa suke yi, ko littattafan addini sai an fassara musu da Hausa.
Abin kunya ne a ce ƙasar Nijar ta ayyana Hausa a matsayin harshen ƙasa, amma Nijeriya ba ta yi haka ba, duk kuwa da cewa Hausa na daga cikin manyan harsunan ƙasar.
Haka kuma wasu malamai suna sa wa ɗalibai wahala wajen nazarin Hausa, suna ƙauron da su daga koyonsa.
Matsala ta uku: Idan An Bi Ta Ɓarawo…Ya kamata malamai da ɗalibai su ci gaba da aikin fassara kalmomi daga fannoni daban-daban na ilimi zuwa Hausa, don a samu damar shiga kowanne fanni kamar yadda ake yi da Turanci, Larabci, Sinanci da sauransu.
Gudunmuwar Harshen Hausa:1. An fassara kusan duk littattafan addini zuwa Hausa.
2. An fassara littattafan kimiyya, tarihi, lissafi da sauransu.
3. Hausa ta mamaye kafafen sada zumunta kamar Facebook, WhatsApp, X, Instagram da TikTok.
4. Ana amfani da Hausa a kafafen yaɗa labarai a ƙasashe irin su Amurka, Sin da Faransa.
5. Malamai sun rubuta littattafai da muƙaloli da dama domin ci gaban harshen.
Shawarwari:1. A tafiya da zamani wajen koyar da Hausa.
2. A sauƙaƙa hanyoyin koyo da koyarwa.
3. A mayar da Hausa darasi na dole a firamare da sakandire.
4. A wajabta wa ɗaliban ƙasashen waje koyon Hausa idan suka zo karatu a Nijeriya.
5. A shigar da Hausa cikim fannin kimiyya da fasaha.
6. A sa Hausa cikin darussan GES/GSE a jami’o’i da kwalejojin ilimi.
7. A ayyana Hausa a matsayin harshen hukuma a Arewa ko Nijeriya baki ɗaya.
8. A ƙarfafa gwiwar iyaye, abokai da malamai ga ɗaliban da ke nazartar Hausa.
9. A riƙa bai wa masanan Hausa aikin da ya dace da su, musamman fassara da rubuce-rubuce.
Idan aka aiwatar da waɗannan, za a dawo da martabar harshen Hausa.
KammalawaTakardar ta nuna matsalolin da harshen Hausa ke fuskanta, gudunmuwar da yake bayarwa ga al’umma da addini, sannan ta kawo hanyoyin da za a bi don dawo da martabarsa a ƙasar nan.
Mubarak Idris Jikamshi ne ya rubuta albarkacin Ranar Hausa ta Duniya
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Harshe Nazari Gundumawa Ranar Hausa ta Duniya Shawarwari takarda harshen Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
DSS Ta Maka Sowore, Facebook Da X A Kotu Kan Wallafa Rubutu Game Da Tinubu
Ta kuma ba shi umarnin ya goge rubutun da ta ce ya ci zarafin shugaban ƙasa.
Sai dai Sowore ya ƙi sauke rubutun da ya wallafa.
Ya rubuta a shafinsa na X cewa: “DSS ta shigar da ƙara mai tuhuma biyar a Babbar Kotun Tarayya a Abuja a kaina, X da kuma Facebook.
“Sun ce wai na aikata wasu sabbin laifuka saboda na kira Tinubu ‘ɓarawo’. Duk da haka, zan halarci kotu duk lokacin da aka fara shari’ar.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp